✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake ‘sayen’ shaidar riga-kafin Coronavirus ta bayan fage

Bai dace a ce an wajabta wa kowa sai ya yi allurar ba.

Takardar shaidar allurar riga-kafin cutar Coronavirus (COVID-19) da sauran gwaje-gwaje a Najeriya ta jefa ’yan kasar da dama musamman masu fita zuwa wasu kasashe a tsaka-mai-wuya, ta yadda suke fuskantar sake lale da barazanar sake wata allurar ko sababbin gwaje-gwaje, sakamakon gwajin bogi da aka gano ’yan Najeriya da dama suna yi.

Bincike ya nuna cewa mutane da dama da ba sa bukatar allurar riga-kafin cutar sukan biya wadansu ma’aikatan lafiya ko cibiyoyin yin allurar ’yan kudi kadan da suka kama daga Naira 2000 don karbar takardar shaidar bogi ta yin allurar inda a watannin baya aka gano yadda ake sayen satifiket din bogin a kan Naira dubu 20 zuwa dubu 50, kuma duk da irin lambobin da katin yake dauke da su hakan bai hana yin na bogi ba.

Wasu daga cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu ma ba a bar su a baya ba wajen bayar da takardar shaidar gwaje-gwajen ta karya, inda aka yi zargin suna karbar abin da ya kama daga Naira 5000 zuwa dubu 100, ya dangnta da irin mutanen da suka zo ko matsuwar mutumin.

Tun lokacin bullar cutar COVID-19 da irin matakan da Gwamnatin Tarayya ta bullo da su a tashoshin jiragen sama na kasa, ake ta samun zargin hada baki da jami’ai wajen bayar da irin wadannan takardun na bogi.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa hakan yana da alaka ne da gabatar da tsarin gwaje-gwaje da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta fito da shi wanda hakan ne ya fara haifar da ka-ce-na-ce a harkar diflomasiyya a tsakanin Najeriya da Daular.

Idan za a iya tunawa Gwamnatin Tarayya ta sanya dokar yin gwajin cutar Coronavirus a matsayin sharadi ga matafiyi kafin daga baya Hadaddiyar Daular Larabawa ta kara da gwaje-gwaje a dakunan gwaje-gwajenta, abin da Gwamnatin Najeriya ta ce wannan gwajin ba a tantance shi ba, kuma a sanadiyyar haka ne Najeriya ta dakatar da jiragen Daular Larabawa na Emirate Airlines sauka a Najeriya saboda yin karan-tsaye ga ka’idojin cutar COVID-19.

Aminiya ta gano cewa Daular Larabawar ta bullo da karin gwaje-gwajen ne saboda rashin yarda da ingancin gwajin Najeriya bayan samun rahotannin da ke cin karo da juna kan kwayoyin cutar ta COVID-19.

Darakatan Cibiyar Bincike a Kamfanin Zenith Trabel, Mista Olumide Ohunayo ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kara daura damara a kan lamarin wuraren gwaje-gwajenta kan yadda ake zargin suna bayar da takardun gwaji na karya don ganowa da kuma hukunta masu aikata haka.

Aminiya, ta samu bayanan da suke cewa Hadaddiyar Kungiyar Hukumomin Zirga-Zirgar Jiragen Sama ta Kasa (NANTA), ta fitar da gargadi ga mambobinta da kada wani ya kuskura a hada baki da shi wajen bincike don fitar da takardar shaidar gwaje-gwajen COVID-19 ta karya.

Shugabar NANTA, Misis Susan Akporiaye, ta ce tuni suka yi fatali da harkar takardun karyar tare da shan alwashin ba za su sa hannu a cikin abin da zai cutar da ’yan kasa ba.

Ta kara da cewa, matsalar takardun bogi na gwajin cutar COVID-19 ba ta takaita ga Najeriya ba, sai dai ta yaba wa Gwamnatin Tarayya kan tashi tsaye da ta yi don daukar matakan da suka dace.

Hakan ne ya sa ta yi watsi da maganar cewa an haramta wa ’yan Najeriya zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa ce kan batun sakamakon gwajin cutar Coronavirus.

Aminiya ta gano cewa duk da matakan da gwamnati ke dauka don hana bayar da takardun bogin, wadansu ’yan Najeriya suna ci gaba da bayyana fargabansu game da dokokin wasu kasashen.

Farfesa Wole Soyinka, ya koka a kwanan nan kan yadda ya kusa rasa jirgin tafiya kasar Faransa sakamakon harkalla kan dokokin COVID-19.

Ya ce a matsayinsa na wanda ya saba tafiye-tafiye ta jirgin sama, ana fitar da lambobin takardar ne bayan kammala biyan kudin gwajin wadda ita ce shaidar da ake nunawa a kan iyakokin kasa da kasa, kuma matafiya da dama na kokawa a kan irin tashin hankalin da suke tsintar kansu a ciki kafin su samu.

Farfesa Soyinka, ya bayyana halin da ya samu kansa a hannun jami’an Ma’aikatar Lafiya da na Harkokin Kasashen Waje a hanyarsa ta dawowa daga Faransa a watan Oktoba, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin kan gado.

Ya ce ba kawai a jinkirin tafiyarsa abin ya tsaya ba, a cewarsa baya ga jinkirta masa tashi game da bukatarsa da ya samu izinin tafiya kan dalilan da suka shafi COVID-19, sai ga shi kuma sun buge da sake umurtarsa kan ya bi sauran matakai wanda ya hada da ziyartar shafin tafiyetafiye na Najeriya don neman izinin yin tafiyar kanta.

Ya ce ya rasa gane dangantakar Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje da cutar COVID-19. Soyinka ya ce a karshe an ba shi iznin fita bayan ya gama shan wahala ga kuma irin jinkirin da ya samu sakamakon duba lafiyarsa da aka yi a can.

‘Dalilin da ya sa ake bin bayan fage’

An ce wadansu ’yan Najeriya suna bin bayan fage ne don samun takardar allurar bogin saboda yadda wasu kasashe suke takurawa kan ganin katin shaidar.

Haka batun yake ga masu ganin akwai wata makarkashiya tattare da allurar riga-kafin ta Coronavirus, inda suka gwammace su bi ta bayan fage don sayan katin shaidar da duk abin da ake bukata don shiga ofisoshinsu ko don yin tafiye-tafiye maimakon a yi musu allurar.

Haka kuma, binciken da Aminiya ta yi, ya gano cewa mutane da dama har yanzu ba su gamsu da allurar ba, wanda hakan ya sa suke kin yarda a yi musu duk kuwa da bayanan da Gwamntin Tarayya take yi a kan ingancinta.

Domin bin umarnin sai ma’ikata sun nuna shaidar yin allurar riga-kafin kafin shiga ofis, wani mai suna Ocheni Idris ya tafi wata cibiyar kiwon lafiya da ke Karshi a yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja, inda kai-tsaye ya nufi wajen jami’in da ke kula da yin allurar COVID-19 ya shaida masa yana bukatar katin ne kawai domin bai gamsu da yin allurar ba, inda nan take ya biya kudin katin Naira dubu biyu.

Za mu hukunta masu harkallar —NPHCDA

A watan Satumba ne Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA), Dokta Faisal Shu’aib, ya ce hukumar tare da hadin gwiwa da jami’ai za su fara bincike tare da hukunta duk wanda aka kama da laifin amsar kati ba tare da yin allurar ba.

Ya ce lura da yadda cutar COVID-19 take dada karuwa a duniya ya zama tilas hukumarsu da ma’aikatar lafiya su yunkura don dakile wadanda suke karbar katin ba tare da yin allurar ba domin a cewarsa mallakar katin ba tare da yin allurar ba babban laifi ne da doka za ta yi aikinta a kai ga duk wanda ya saba.

“Ga masu sayarwa da masu son saya dukkansu babu wanda doka za ta kyale.

“Mun dauki wannan mataki ne saboda yadda aikin irin wadannan mutanen ke zubar da kimar Najeriya a idon duniya da rashin yarda da gaskiyar matakai da allurar da ake yi a Najeriya.

“Muna sa ido sosai don ganin hakan bai ci gaba da faruwa ba.

“Za mu bayyana sunayen dukkan wadanda suka shiga hannu, mu kuma kunyata su,” inji shi.

Sai dai duk da daukar watanni da wannan barazana, wakilinmu ya yi kokarin ganoko mutane nawa aka kama tare da hukuntawa, amma hukumar ta ki cewa komai a kai domin Kakakin Hukumar, Mohammad Ohitoto, ya ki mai da sakon waya ko amsa kiran wayar da aka yi masa.

Bai amsa tambayar ko me hukumar ke shirin yi don shawo kan matsalar ba.

Da yake yi wa Aminiya karin haske, wani kwararren masanin kiwon lafiya, Dokta Casmir Ifeanyi, ya ce harkar cogen yin allurar Coronavirus tare da mallakar katin shaida na bogi ba ga Najeriya ya takaita ba, hatta a kasar Ingila ma an samu irin wannan matsalar nan da can.

Ya ce wuraren yin allurar da dama ana zarginsu da bayar da katin ba tare da yin allurar ba.

Dokta Casmir, ya ce wasu dalilan da suka dada taimaka wa hakan su ne daukar ma’aikatan da ba kwararru ba.

“Bai dace a ce an wajabta wa kowa sai ya yi allurar ba.

“Amma idan har ka zabi rashin yi to ka san akwai dokar da za ta tafiyar da kai, don kana da hadari a cikin al’umma kuma kada hadarinka ya shafi sauran jama’a,” inji shi.

Abin da ya sa mutane ke tsoron allurar —Sarkin Musulmi

Da yake jawabi kan dalilan da mutane suke kin allurar, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya ce yadda aka rasa aminci da yarda da juna ne babban kalubalen da ke kawo cikas ga lamarin riga-kafin Coronavirus.

Ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta kara kaimi wajen wayar da kan al’umma, sannan ya ce a shirye sarakunan Arewa suke domin taya ta wannan aiki.

Ya ce za a samu karin nasara idan ana tafiya tare da mutane.

A karshe ya shawarci ’yan Najeriya su yi watsi da rade-radin da ake yadawa kan allurar, inda ya ce su yi allurar domin su ceci kansu da ’yan uwansu.

Kaso 70 na ’yan Najeriya za su yi riga-kafin a 2022 —Gwamnatin Tarayya

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Yaki da Cutar Coronavirus, Mista Boss Mustapha ya ce Gwamnatin Tarayya ta shirya tsaf domin cim ma burinta na tabbatar da kaso 70 na ’yan Najeriya sun yi riga-kafin a badi.

“Yanzu lokaci ne na riga-kafi da kuma kariyar kai-da-kai.

“Muna shawartar mutane da su je su yi riga-kafin nan, sannan su ci gaba da lura da hanyoyin kariya.

“Najeriya ta shirya domin ganin kaso 70 na mutanenta sun yi rigakafin kafin karshen shekarar 2022.

“Riga-kafin nan ba ya illa ko kadan, kuma zai fi kyau idan mutum ya yi,” inji shi.