✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake dafa Tuwon Shinkafa da miyar Ganyen Ugwu

A yau muna dauke ne da yadda za ki girka Tuwon shinkafa da miyar Ganyen  Ugwu

Uwargida barka da rana.

A yau muna dauke ne da yadda za ki girka Tuwon shinkafa da miyar Ganyen  Ugwu.

Kayan hadin da ake bukata

Tuwon shinkafa

Shinkafar tuwo

Ruwa

Yadda za a dafa tuwon

A jika shinkafar tuwo a ruwa ta jiku sosai, sai  a dora ruwa a wuta, bayan ya tafasa sai a wanke jikakkiyar shinkafar a zuba sannan a rage wuta a rufe da murfin tukunya.

Sai a bar shi ya yi ta tafasa sai ya yi laushi sosai, sai a sauke a tuka

A kwashe a zuba a kwanuka.

Miyar ganyen Ugwu

Kayan hadi:

Ganyen Ugwun

Naman shanu ko na kaza

Ganda

Kifi

Albasa

Tumatir

Attarugu

Daddawa

Sinadarin dandano

Manja

Tafarnuwa

Yadda za a dafa miyar

  • A wanke ganda da naman  sannan a sanya a tukunyar.
  • A yanka albasa a sa magi da gishiri sai a rufe a dora a kan wuta.
  • Idan suka yi laushi sai a sauke a ajiye a gefe.
  • A wanke ganyen  ugwu da gishiri da ruwa sannan a yayyanka a ajiye a gefe.
  • A wanke kifi  sannan a yanka shi a ajiye a gefe.
  • A dora tukunyar a wuta sannan a zuba manja.
  • Idan manjan ya yi zafi, sai a zuba jajjagen kayan miya a yi ta soyawa har sai sun soyu.
  • Sai a zuba magi da dadawa da dafaffen naman da ganda.
  • Bayan ya dan tafasa sai a zuba ganyen ugwun a jira na tsawon minti sannan a sauke.