✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake wahala kan rashin sabbin kudi a Jigawa

Kwamishinan ya bukaci CBN da ya tausayawa mutane halin da suke ciki.

Gwamnatin Jihar Jigawa ta nuna damuwarta kan yadda rashin sabbin takardun kudi Naira ke ci gaba da ta’azzara a jihar.

Kwamishinan Kudi da Ci Gaban Tattalin Arzikin jihar, Alhaji Babangida Gantsa ne, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Dutse.

Ya ce, bankunan kasuwanci sun gaza samar da sabbin kudaden duk da umarnin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar.

Gantsa wanda ke ido kan yadda ake hada-hadar kasuwancin wasu bankuna ke gudana, ya bayyana cewa galibin injinan ATM ba sa bayar da kudaden ga kwastomomi a fadin jihar.

“Wasu daga cikin manajojin bankin sun yi magana kan kalubalen da suke fuskanta, daya daga cikinsu ya yi ikirarin cewa Naira miliyan biyu kacal CBN ya ba su”.

Kwamishinan ya ce lamarin ya jefa jama’a da dama a jihar cikin mawuyacin hali.

“Wasu kwastomomi suna shafe sama da sa’o’i tara a bankuna ba tare da sun samu sabbin kudin ba.

“Batun raba sabbin kudi a Jigawa suna ya tara, mutane na cikin wahala,” in ji shi.

Don haka ya bukaci CBN da ya tabbatar da samun sabbin takardun kudi ga bankuna ko kuma a sake sanya sabon wa’adi.