✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake yin awarar kwai

Kwai na daga cikin abincin da mutane kan ci musamman domin marmari ko kayatarwa mai hanyoyin sarrafawa iri-iri, ciki akwai awarar kwai. Mutane da dama…

Kwai na daga cikin abincin da mutane kan ci musamman domin marmari ko kayatarwa mai hanyoyin sarrafawa iri-iri, ciki akwai awarar kwai.

Mutane da dama na son cin awarar kwai ko su yi da kansu, amma ba su san yadda za su bullo wa abun ba.

Ku kwantar da hankalinku, yau mun kawo muku bayanin dayya ake yin awarar kwai.

  • Abubuwan da ake ukata:
  1. Kwai
  2. Nama
  3. Mai
  4. Maggi
  5. Attaruhu
  6. Albasa

 

  • Yadda Ake Yi

A gyara nama mara kitse a markada shi sannan a jajjaga attarugu da albasa a juye a ciki.

A fasa danyen kwai sannan a kada shi sai a sa masa magi da gishiri da sauran kayan hadi daidai bukata a juya shi sosai.

Daga nan dan a hada kwan da naman a motsa, sannan a juye hadin a cikin farar leda sai a saka a tukunya a dafa kamar alala.

Idan ya nuna sai a sauke a yayyanka kamar awara.

Daga nan sai a sake kada danyen kwai a rika tsoma hadin da aka riga aka dafa a ciki ana soyawa.

Wannan shi ne yadda ake hadda awaran kwai.

A ci dadi lafiya.