✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake yin burodin ayaba

Barkanmu da warhaka uwargida. Tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwadawa…

Barkanmu da warhaka uwargida. Tare da fatar ana cikin koshin lafiya.

A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwadawa domin yi wa Manyan Gobe a matsayin abin karyawa a duk safiya ko kuma yin sa domin sha’awar cinsa ko kai wa aminan arziki.

Kamar yadda muka yi muku alkawari za mu ci gaba da kawo muku nau’o’in girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:

  • Fulawa
  • Kwai
  • Sukari
  • ‘Baking powder’
  • Ayaba
  • Madara
  • Bata

Yadda ake yin hadin:

A samu ayaba biyu a kwaba su da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da sukari da madara, sannan a kwaba.

Bayan haka a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sai a fasa kwai biyu da kwababbiyar ayabar a cikin fulawar da aka yi mata hadin sukari da sauransu.

Sai a gauraya su sosai su kwabu. Sannan a dauko tukunyar gasa burodi a zuba sannan a sa a gidan gasa burodi. Bayan minti 45 sai a cire.

Za a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandani sabon salon burodi.