✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake yin salak din tumatir da kokumba

Yin sa na da sauki kuma yawan cin sa na kara lafiya.

A yau mun kawo maku yadda ake yin salak din kokumba da tumatir, wanda yin sa na da sauki kuma yawan cin sa na kara lafiya.

Kayan hadi:

  • Kokumba
  • Tumatir
  • Albasa
  • Tatasai
  • Gyanyen parsley
  • Man zaitun
  • Ruwan kal (Vinegar)
  • Gishiri
  • Sugar
  • Bakin barkono

Yadda ake hadi

  1. A yi amfani da gishiri a  wanke tumatir, kokumba, albasa, tatasai da gyanyen parsley, sai a daureye sosai a sa kowanne a gwagwa ya tsane.
  2. A yayyanka kowanne daga cikinsu a ajiye a gefe guda.
  3. Sai a samu kwano mai zurfi a zuba su a ciki.
  4. A barbada bakin barkono, gishiri da sukari sai a juya.
  5. Sai a sa vinegar da man zaitun a sake guyawa sosai.

Shi kenan salad ya yi sai ci.

A ci dadi lafiya.