✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake yin ‘smoothie’ na ayaba

Matakan da ake bi domin hada 'smoothie' din ayaba

Assalamu alaikum warahmatullah, da fatan kuna cikin koshin lafiya.

A yau na zo muku ne da yadda ake yin ‘banana smoothie’ cikin sauki.

  • Abubuwan hadawa:
  1. Ayaba
  2. Madara ta ruwa
  3. Flavor

 

  • Yadda ake hadawa
  1. To da farko za a bare ayaba a tsaga ta a cire bakin abin da ke tsakiyarta.
  2. Daga nan sai a yayyanka ayabar a sa a blender a nika.
  3. Sai a zuba madara da ‘Flavor’ daidai bukata a cikin nikakken ayabar sannan.
  4. Bayan nan sai a juye a mzubi a sa a firji ya yi sanyi.

A sha dadi lafiya.