✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake yin wasa-wasar dawa da wake

Babu shakka wannan cimaka tana kada kunnuwan wanda ya dandana.

A wannan zamani ba kasafai ake yin wasa-wasar wake da dawa ba musamman a cikin birane, sai dai babu shakka wannan cimaka tana kada kunnuwan wanda ya dandana.

Kayan hadi:

• Dawa

• Wake

• Man gyada

• Yaji

• Sinadarin dandano

• Gishiri

• Kayan kanshi

Yadda ake hadawa:

Da farko uwargida za ki samu farar dawarki da farin wakenki sai ki gyara kowanne daga ciki.

Sai ki wanke waken ki zuba ruwa ki sa dan gishiri sai ki dora a wuta idan sun jima a kan wuta sai ki dauko dawarki ki wanke ki zuba ta a kan wake nan sai ki bar su su yi ta dahuwa kin san suna da karfi.

Daga nan sai ki zuba sinadarin dandano da kayan kanshi a ciki. Idan suka dahu sai ki rage wuta.

Idan ya tsotse sai ki sauke. Sai ki samu ganyen latas da tumatiri da albasa sai ki hada su waje daya ki yi kwadonsu.

Da wannan kwadon latas din za a ci bayan kin samu soyayyen man gyada da hadadden yajinki kin zuba a ciki.