✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake zamanantar da kasuwanci a Kano

Yadda aka sauya daga kasuwancin ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda zuwa amfani da kudi, tattalin arzikin zamani Amfani da kafar sadarwa· Kasuwar Kurmi da ke birnin Kano tsohuwar kasuwa…

Yadda aka sauya daga kasuwancin ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda zuwa amfani da kudi, tattalin arzikin zamani Amfani da kafar sadarwa·

Kasuwar Kurmi da ke birnin Kano tsohuwar kasuwa ce da take da dadadden tarihi, ba a birnin Kanon ko Najeriya ba, har ma a daukacin Nahiyar Afirka.

Fatake sukan yi takakkiya daga sassan Arewa da Yammacin Afirka zuwa wannan kasuwa. Wannan tarihi kuwa yana komawa tun shekaru fiye da 500 da suka wuce.

A wancan lokaci bakin ’yan kasuwar sukan debo hajojin kasuwanci iri-iri su biyo burtali su taho da su birnin Kano domin sayarwa, yayin da idan suka tashi komawa gida sai su sayi ireiren kayayyakin da suke bukata su tafi da su garuruwansu.

An ce Kasuwar Kurmi ita ce sanadiyar yaduwar Addinin Musulunci a Kano da kewaye.

Wannan ya kawo bunkasar kasuwanci kwarai da gaske a wannan kasuwa ta Kurmi.

Sai dai a tsawon wadannan shekaru an samu canje-canje da dama, kama daga yanayin zama, zuwa tsarin gini da huldodin kudade da makamantansu.

Jaridar Aminiya ta tuntubi wadansu daga cikin wadanda suke gudanar da harkokinsu a wannan kasuwa, don jin irin yadda ake kasuwanci a da, da kuma canje-canjen da zamani ya zo musu da su.

‘Mafarauta ne suka kafa Kasuwar Kurmi’

Da farko Sarkin Kasuwar Kurmi, Alhaji Abdullahi Maikano ya shaida wa Aminiya cewa kasuwanci a wancan lokaci ya sha bamban da kasuwanci a yanzu nesa ba kusa ba. “Da farko ita Kasuwar Kurmi mafarauta ne suka kafa ta, idan wannan ya kamo zomo sai ya kawo a ba shi guza, shi kuma mai maciji sai ya bayar a ba shi gafiya, ko mai gada da mai barewa su yi musanya sai dayan ya yi ciko da wani abin daga cikin kananan dabbobi,” inji shi.

Yadda ta samo sunan Kurmi

Sunan Kurmi ya samo asali ne daga fadama, kasancewar kasuwar a da tana cikin fadama ce mai tarin bishiyoyi da ruwa kafin daga baya a fara gine-gine.

Alhaji Maikano ya kara da cewa, “Daga nan sai masu cinikin bayi suka fara zuwa suna kasuwancinsu a wajen. Sannan sauran masu harkoki suka ci gaba da zuwa.

“A wancan lokaci ita kanta kasuwar tana cikin fadama ce, shi ya sa ake kiranta da Kasuwar Kurmi.

“Ka san Kurmi yana nufin waje mai yawan ruwa da bishiyoyi, amma yanzu ka ga gine-gine iri-iri, ga wutar lantarki ga benaye.”

Da ya juya a kan batun hadahadar kudi a da da kuma yanzu sai ya ce, “A wancan lokaci bayan cinikin ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda, saI aka fara hulda da kudi irin su Wuri da Nayi da Taro da Ahu da dari har aka taho kan Sulalla da Kwabbai, amma yanzu an yi kudaden takarda, ka ga an samu canji.”

Shi ma da yake bayanin yadda aka samu bambanci tsakanin da da yanzu, Shugaban kungiyar Masu Sayar da Huluna ta Kasuwar Kurmi, Alhaji Sani Abdulmumin, cewa ya yi, “Ka ga a da can babu itacen dame hula sai dai kawai a wanke ta idan ta bushe a yi mata kari uku, shi ke nan sai sakawa, kuma kowace hula da hannu ake dinka ta.

Amma yanzu sai a dauki samfurin zanen hula a kai China a kero dubbanta, irin su zanna-bukar ne har yanzu ake yi da hannu.”

A wannan zamani da akalar kasuwanci ta juya zuwa na’urorin sadarwa, wadansu za su dauka cewa an bar ’yan Kasuwar Kurmi a baya ganin cewa kasuwa ce ta gargajiya, sai dai mazauna kasuwar sun ce sam ba haka abin yake ba, domin kuwa sun karbi canjin da zamani ya kawo, kuma suna ganin fa’idar hakan sosai da sosai.

“Yanzu ko kayan Naira miliyan nawa ka saya a wajena sai in ba ka lambar asusun bankina, kai kuma ka tura min, da sun shiga sai in ba ka kaya.

“Haka idan zan saya sai dai in tura musu kudin su turo min kayana. Ai ka ga an samu sauki,” inji shi.

Amma da Aminiya ta tambaye shi ko suna ajiye POS a shagunansu don abokan huldarsu kawai, sai ya ce, “A’a ba mu fara wannan ba, sai dai mutum ya je wajen masu POS na kasuwanci ya ciro ya kawo mana.”

A nasa bangaren wani mai sayar da littafi Alhaji Hamisu Abdulmumin Gora, ya bayyana yadda suka zamanantar da kasuwancinsu da kuma alfanun hakan.

“Ka tuna a baya yadda idan bako ya zo zai sayi kaya ya ba ka tarin kudade ka yi ta kirgawa don ka tabbatar sun cika kafin ka ba shi kaya.

“Ka ga yanzu wannan ya kau, wani lokacin ma kafin bako ya zo ya turo maka kudin, yana zuwa an riga an hada kayansa sai ya dauka ya tafi.

“Idan a baya kana sallamar baki goma a awa daya, to yanzu a minti ashirin za ka sallame su.

“Ke nan an habaka tattalin arziki ta hanyar rage bata lokaci. Amma duk yadda abu ya kai da amfani to ba ya rasa matsaloli.

“Misali a da wadansu masu cinikayya da yawa suna ajiye yaro don kirga kudi, a yanzu babu bukatarsa, haka nan yaran da muke aike su kai kudi banki ko su karbo, su ma yanzu sun rasa aikin yi.”

Alhaji Bala Muhammad Maiwuri wanda ya kwashe shekara 45 yana sayar da tsakiya da munduwa da makamantansu, ya shaida wa Aminiya cewa an samu ci gaba sosai a Kasuwar Kurmi saboda zuwan Intanet.

“Misali, a can baya sai bako ya zo sannan zai ga abin da yake so, idan bai yi masa ba, sai ya koma da kudinsa, amma yanzu da waya muke daukar hotuna mu tura ta Whatsapp, mai saya ya duba ya zabi wanda ya yi masa, ya sanar da mu a tura masa har garinsu, ba sai ya zo ba,” inji shi.

Ya kara da cewa ita ma waya da Intanet sun taho da nasu matsalolin, “Sai dai duk da taimakon ’yan kasuwa da wadannan hanyoyin zamani ke yi, a gefe guda kuma ’yan kasuwa na yin korafi a kansu.

Domin akwai abin da yake faruwa inda ’yan kasuwa ke korafin cewa ana bin bakinsu a baya a karbi lambar wayarsu, sai a ce ba ni lambarka zan yi maka ragi, wato shi ke nan an kwace wa mutum bakonsa.

Kai akwai wadanda ko da bako bai zo da kansa ba, to idan ka hada masa kaya za ka bayar a kai tashar mota, sai a kwafi lambar da ka rubuta a jikin buhun, daga baya a kira shi a yi masa tallar irin kayan da ka sayar masa,” inji shi.