✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda APC da PDP ke jifan juna da zargin aikata laifuka

Magoya bayan 'yan takarar na jifan juna da zargin aikata laifuka daban-daban.

Yayin da ake ke shirin gudanar da zaben Shugaban Kasa a watan gobe, magoya bayan dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da magoya bayan takwaransa na PDP, Atiku Abubakar na ci gaba da zargin juna kan aikata manyan laifuffuka daban-daban.

APC ta zargi Atiku da jagorantar almundahana lokacin da yake rike da mukamin Mataimakin Shugaban Kasa a karkashin gwamnatin Olusegun Obasanjo, wadda ta ce ya ba shi damar satar kudaden talakawa tsakanin 1999 zuwa 2007.

Wannan ya sa Tinubu ya bukaci Atiku da ya janye daga takarar zaben da kuma gabatar da kansa ga hukumomin yaki da rashawa na EFCC da ICPC don bincikarsa.

Magoya bayan PDP sun bayyana Bola Tinubu a matsayin wanda kwaya ta yi wa illa da kuma wanda aka taba samu da laifin safarar kwayoyi a Amurka, sai dai wannan zargi APC ta musanta shi.

Sannan PDP ta zargi Tinubu da kafa rundunar ‘yan bindiga wadanda za su yi wa shirin zabe mai zuwa zagon kasa, inda suka bukaci kama shi domin amsa tambayoyi daga hukumomi.

PDP ta kuma bayyana cewar Tinubu ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai iya jagorantar miliyoyin al’ummar kasar nan.

Wannan zargi ya sa magoya bayan Tinubu gabatar da wani hoton bidiyo mai dauke da dan takarar yana tikar rawa da kuma hawa keken motsa jiki.

Yanzu dai mai magana da yawun Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, Festus Keyamo ya maka EFCC da ICPC da kuma hukumar kula da da’ar ma’aikata a gaban kotu, inda ya bukace su da su tuhumi Atiku kan zargin da ake masa na karkatar da wasu kudade lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.

Daukar wannan mataki ya biyo bayan wa’adin sa’oi 72 da Keyamo ya bayar na gayyatar Atiku wanda ya cika ba tare da daya daga cikin hukumomin ta yi wani yunkuri ba.

Ministan ya bukaci haka ne bayan da a ka ruwaito wani tsohon hadimin Atiku da ake kira Michael Achimugu, ya saki wasu bidiyo da ke dauke da zarge-zarge da dama a kan tsohon mai gidan nasa.

Bisa dukkan alamu, magoya bayan wadannan ‘yan takara za su ci gaba da amfani da sauran lokacin da ya rage na gudanar da zaben domin batanci a tsakaninsu, ganin yadda kowane bangare ke zargin juna.

Sai dai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gargadi ‘yan siyasa da amfani da kalmomin da ka iya tunzura wani bangare da zai iya haifar da rikici ko tashin-tashina.