✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda APC ta hana Tinubu taron yakin neman zabe a Neja

Ana zargin rashin jituwar da ke tsakanin Sanata Abadullahi da Gwamna Bello ya hana gudanar da taron.

Jam’iyyar APC reshen Jihar Neja, ta hana gudanar da taron yakin neman zabe da aka shirya wa dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar da kuma dan takarar gwamna a jihar.

Wakilin ya ruwaito cewa tun da fari dai Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya aika sakon gayyata ta hannun hadiminsa, Mohammed Garba Danladi zuwa ga shugaban APC na jihar, Honorabul Haliru Zakari Jikantoro da Kwamitin Gudanarwa da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar.

Hakan ce ta sanya aka shirya gangamin domin dan takarar Shugaban Kasa, Bola Tinubu da kuma  Honorabul Mohammed Bago da Kwamred Yakubu Garba – masu takarar gwamna da mataimaki a jihar a Zaben 2023.

“Domin karfafa damar samun nasara ga jam’iyyarmu a zabe mai zuwa, muna neman hadin kai da goyon baya don samun nasara a gangamin,” kamar yadda gayyatar ta nuna.

Sai dai kuma shugabannin jam’iyyar a jihar sun nesanta kansu da taron, tare da hana mambobin jam’iyyar halartar gangamin da aka shirya.

Cikin sanarwar da shugabannin jam’iyyar suka fitar ta hannun sakataren jam’iyya, Musa Dan Sarkindaji, ya ce gangamin ya saba wa tsarin da jama’iyyar ta tanada na gudanar da tarurrukanta.

Maimakon haka, jam’iyyar ta bukaci shugabaninnta da masu ruwa da tsaki da sauran mambobinta da su halarci taron da ta za ta gudanar ranar Laraba a garin Bida.

Bayanai sun ce an girke jami’an tsaro masu yawan gaske filin da aka shirya gudanar da taron a New Bussa inda suka hana kowa shiga harabar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce an girke jami’an tsaro a filin taron ne domin hana yi wa doka karan tsaye bayan da suka hararo cewa komai na iya faruwa idan aka bari taron ya gudana.

Hana taron ya sanya dangartaka ta yi tsami tsakanin Gwamnan jihar, Sani Bello wanda shi ke rike da akalar jam’iyyar da kuma Sanata Sabi Abdullahi, wanda nauyin shirya taron ya rataya a wuyansa.

Abdullahi shi ne Sanatan Neja ta Arewa, ya shiga takarar fidda gwanin da jam’iyyar ta yi a baya duk da matsin da ya fuskanta kan ya janye wa Gwamna Bello, amma bai yi nasara ba.

Tun bayan lashe zaben fidda gwanin da Gwamnan ya yi, hakan ya sa ba sa ga maciji da juna da Sanata Abdullahi wanda ya so maimaimata kujerarsa.

Bayanai sun nuna duk da taron da aka so gudanarwa din na APC ne, amma ba a ga hotunan Gwamna Bello na takarar kujerar Sanata a harabar ba.