✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda attajiri ya ci ribar Naira tiriliyan biyar a rana daya

Jeff Bezos ya ci ribar Dala biyan 13 a ranar Litinin 20 ga watan Yulin 2020

Shugaban kamfanin Amazon da ke Kasar Amurka Jeff Bezos, ya ci gagarumar riba da ta kai Dala biyan 13, kwatankwacin naira Tiriliyan 5 a cikin kwana daya kacal.

Ya ci rabar ne ranar Litinin 20 ga watan Yulin 2020.

Mujallar Bloomberg Billionaires da ta ke tattara bayanan attajirai ta bayyana cewa wannan shi ne karon farko tun da aka KirKiri mujallar a 2012 da aka samu wani attajiri ya ci gagarumar riba cikin kwana daya kacal.

Mujjalar ta rawaito cewa, gagarumar ribar da attajirin duniyar ya ci, ta samu ne sakamakon dagawar hannayen jari da kaso 7.9, wanda ita ce babbar riba da aka samu tun Disambar 2018.

Samun karuwar ribar ta biyo bayan yawaitar hadahadar cinikayya da aka samu ne ta kafar intanet, a cewar rahoton.

Bloomberg ta kara da cewa Bezos, ya ci ribar da ta kai dala biliyan 74.4 a shekarar 2020, wanda kididdigar yawan dukiyarsa ta kai Dala biliyan 189, duk da masassarar tattalin arziKi da aka shiga wanda cutar coronavirus ta haddasa.

Rahotan ya bayyana cewa a yanzu Mista Bezos, yana da dukiyar da ta haura ta manyan kamfanoni irin su; kamfanin mai na Eddon da Mobil Corp da kamfanin sarrafa kayan wasanni na Nike Inc da kuma McDonald’s Corp.