✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda auren ‘talaka’ ya nesanta ’yar sarki da sarautar Japan

Hakan dai na nufin gimbiyar ta rasa damarta ta jinin sarautar kasar.

Bayan shafe shekaru ana ta cece-kuce, babbar ’yar Sarkin Japan ta yi watsi da al’adar masarautar ta auri saurayinta da suka hadu a makaranta.

Gimbiya Mako, babbar ’yar sarkin Japan Naruhito ta auri saurayin ta, Kei Komuro a ranar Talata, wanda talaka ne kuma ba jinin sarauta ban.

Lamarin ya jawo cece-kuce a fadar masarautar sakamakon yadda ita gimbiyar ta rasa damarta ta zama daya daga cikin wadanda za su iya sarauta a fadar matukar ta auri wanda ya ke ba jinin sarautar ba, kamar yadda dokar ta ke a kundin dokokin masarutar.

Sai dai gimbiyar ta kekashe kasa tare da bin ra’ayinta sama da abin da ya ke a cikin kundin dokar masarautar.

Wace ce Gimbiya Mako?

Mako ’yar wa ce ga Sarki Naruhito, wanda ya hau karagar mulki a shekarar 2019, bayan mahaifinsa ya sauka daga karagar, ya fara wani sabon zamanin daular mai suna ‘Reiwa’.

Iyalan gidan sarautar dai na da wani tarihi na sama da shekara 2,600, wanda suka gada daga wurin gunkinsu, Amaterasu.

Me ya sa Mako ta zabi fita daga tsarin masarautar?

Kundin dokar masarautar da aka fara amfani da shi tun a shekarar 1947 bai yarda da mace ta hau karagar Chrysanthemum ta masarautar ba, haka kuma duk wacce da ta auri wani wanda ba jinin sarutar ba za ta rasa matsayin da ake ba mata a masarautar.

Wannan ne ya ke nuna cewa Mako ta zabi barin gidan sarautar tun da ta auri saurayin nata wanda aka yi musu baiko sama da shekara hudu da suka wuce.

Yanzu  dai Hisahito, kani ga Mako mai shekara 15 ne kawai zai iya gadon karagar ban da babansa, Akishino, wanda shi ne yarima mai jiran gado.

Sai dai masu riko da al’adar kasar da dama ba su goyi bayan hakan ba, duba da cewa tun bayan mulkin sarauniya Gosakuramachi, sama da shekaru 250 rabon da a samu wata mace ta hau kan karagar.

Wacce dambarwa aka samu?

Gidan sarautar Japan ya fuskanci matsin lamba daga bangarori da dama dangane da tsofaffin dokokin masarautar inda ake ganin ya kamata a yi musu kwaskwarima don  su dace da zamani.

Mutane da dama sun yi ta cece-kuce tun bayan da aka samu labarin cewa mahaifiyar Komuro ta gaza biyan bashin Yen miliyan hudu, kwatankwacin Dalar Amurka 3,5000 da ta karba  daga wata tsohuwar budurwarsa.

Tun bayan sanar da ranar auren,  amaryar ta fara rashin lafiya bayan fadi tashin da ta ke yi da manema labarai kamar kamfanin dillancin labarai na Imperial Household ya rawaito.

A yayin bikin gimbiya Mako da Komuro, ba a gudanar da abubuwan al’adar da aka saba na aure a masarautar ba, sannan kuma ba su biya kudin da ake biya idan matan da za su auri wani wanda ba dan sarautar ba wanda aka ce ya kai Yen miliyan 153.

Shin an taba samun irin hakan a baya?

Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin masarutar Japan da aka taba yin bikin sarauta ba tare da yin al’adun gargajiya ba.

Amma akan samu duk lokacin da ake auren wata a masarautar ta kwanta jinya sakamakon fadi tashin da ake fama da shi yayin bikin.