Daily Trust Aminiya - Yadda Barazanar harin Boko Haram ta firgita Zamfarawa
Subscribe

Yadda Barazanar harin Boko Haram ta firgita Zamfarawa

Tsoro da fargaba sun kama mazauna garuruwan  Jihar Zamfara bayan da Gwamnatin Jihar ta bayar da sanarwar cewa kungiyar Boko Haram tana shirin kai hare-hare a wasu kananan hukumomi bakwai na jihar.

Kananan humomin dai gwamnatin ta ce za a kai wa harin sun hada da Talata Mafara da Maradun da Gusau da Tsafe da Anka da Zurmi da Maradun da sauran wurare. Gwamnatin kuma ta kara da cewa ’yan ta’addan Boko Haram za su kai wasu jerin hare-haren a wuraren taruwar jama’a, kamar masallatai da kasuwanni.

Wani mazaunin garin Gusau mai suna Hamisu Aliyu ya shaida wa Aminiya cewa tun bayan da gwamnati ta ba da sanarwar suka shiga cikin halin dar-dar a jihar, duk da cewa  jihar ta shafe shekaru ana kai munanan hare-hare a kan al’ummomi, musamman a yankunan karkara.

“A lokutan baya ana kai hare-hare a kauyuka da dazuka amma mazauna manyan guruwa ba a kai musu irin wadannan hare-hare, in ban da garkuwa da mutane to, sai ga shi an ce wadannan ’yan ta’adda za su kai hari har da masallatai da kasuwanni. Lamarin yana da ban tsoro sosai,” inji shi.

Shi ma wani mazaunin garin Talata Mafara ya shaida wa Aminiya ta tarho cewa, yana cikin rudu game da lamarin jihar, duk da cewa an samu kwanciyar hankali a jihar bayan da aka bullo da shirin sulhu da ’yan bindiga. Ya  ce a yanzu maganar kai hari irin na kungiyar Boko Haram zai kara dagula lamura ne kawai.

“Yanzu da gwamnati ta ce kungiyar Boko Haram na shirin kai hari, wannan ya kara saka fargaba a zukatan jama’a. Kamata ya yi su ja bakinsu su yi shiru, kawai sai dai a ga suna kara inganta matakan tsaro a jihar; ba kawai su tada hankalin mutane ba,” inji shi.

Wani mai yin Sallar Juma’a a Babban Masallacin Gusau da ke Kanwuri, ya shaida wa Aminiya cewa ba zai daina zuwa masallacin domin Sallar Juma’a ba, duk da cewa ya tsorata da ya ji wannan sanarwa. Ya ce shekararsa fiye 50 yana Sallah a masallacin, don haka ba ya jin cewa zai bari.

“Na ji tsoro lokacin da aka ce ’yan kungiyar Boko Haram na shirin kai hari, har da masallacin da nake Sallar Juma’a, to amma  ba zan daina zuwa masallacin ba kuma ko wannan Juma’ar a can zan yi Sallah,” inji shi.

To sai dai wani mazaunin garin Anka, kira ya yi ga gwamnati da jami’an tsaro su tashi haikan wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya ce ’yan ta’adda ba su fadin lokacin da za su tafka ta’asarsu, don haka ya zama wajibi a dauki mataki a kansu.

Sai dai duk da fargabar da wadansu ke nunawa, wadansu jama’ar jihar sun yi watsi da barazanar kai harin, suna cewa ’yan siyasa ne a jihar suke son cimma muradunsu; don haka barazanar ba ta da wani tasiri a wajensu.

Aminiya ta tuntubi Mai ba Gwamna Shawara kan Lamuran Tsaro, Alhaji Abubakar Dauran., inda ya ce sabanin yadda mutane ke yada jita-jita cewa yarjejeniyar da gwamnatin jihar ta kulla da ’yan bindiga ce ke neman wargajewa ya sa gwamnatin ta fitar da wannan sanarwa. Ya ce yarjejeniyar tana nan daram.

“Mun zauna da shugabannin Fulani, wadanda da su ne muka kulla yarjejeniyar kuma sun tabbatar mana cewa babu abin da ya shafi yarjejeniyar tasu. Hasali ma cewa suka yi sun yi mamakin yadda suka ji ana maganar harin Boko Haram.

“Kafin mu fidda sanarwar, mun kira su mun fada musu bayanan sirrin da muka samu, sun nuna mamakinsu game da lamarin suka ce su a daji suke kuma idan akwai wata barazana, su ya kamata su fara sani, kuma duk abin da suka gano za su sanar wa hukumomi ba ma sai an nemi suyi haka ba. Saboda, haka babu wani abu da ya shafi yarjejeniyarmu da su. Kuma sun zama kamar idanunmu a cikin dazukan. Kuma kada ka manta mun yi nasarar karbo bindigogi kirar AK47 guda 49. Kuma su tubabbun ’yan bindigar sun taimaka mana wajen karbar makaman,” inji shi.

Da yake magana a kan fitaccen dan bindigar nan da ake kira Dogo Gide, Dauran ya ce Dogo Gide, wanda yanzu haka  yankin Rijau a Jihar Neja ya ba su goyon baya lokacin da suke zaman sulhu da ’yan bindigar.

“Dogo Gide ya turo wakilansa kuma ya fada mana cewa yana goyon bayan sulhu kuma shi ya daina fashi da garkuwa da jama’a, shi ne ma dalilin da ya sa ya bar yankin Zamfara zuwa Jihar Neja, don ya ci gaba da kiwon shanunsa,” inji shi.

Sai ya yi kira ga mutanen jihar su kwantar da hankalinsu, inda ya cewa gwamnati tana daukar dukkan matakan kare rayuka da dukiyoyinsu. Kuma ya bukaci jama’ su kai rohoton duk wani ko wata kungiya da suke da suke shakku a kanta ga jami’an tsaro don daukar mataki.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara ma ta hannun Kakakinta SP Muhammad Shehu ta fidda sanarwar cewa kowa ya kwantar da hankalinsa, ya ci gaba da gudanar da al’amuransa, domin rundunar tana daukar matakai don magance duk wata barazana.

More Stories