✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka fatattaki Barcelona daga Gasar Zakarun Turai

Barcelona za ta sake fafatawa a gasar Europa a kaka ta biyu a jere.

An fatattako kungiyar kwallon kafa ta Barcelona daga gasar Zakarun Turai ta Champions League bayan ta gaza kai bantenta tun a zagayen cikin rukuni.

A daren ranar Laraba ne Barcelona ta barar da damar samun gurbi a zagaye na gaba na babbar gasar ta Turai bayan shan kashi da kwallaye 3 da nema a hannun Bayern Munich yayin karon battar da suka yi a Camp Nou.

Ficewar Barcelona daga gasar na da nasaba da yadda Inter Milan ta yi nasara a wasanta da kwallaye 4 da nema kan Viktoria Plzen inda ta kammala wasanninta na rukunin a matsayin ta 2 biye da Bayern lamarin da ya bata damar tsallakawa zuwa zagayen kungiyoyi 16.

Romelu Lukaku da ya shiga filin wasa daga baya ya ci kwallao a saura kiri a tashi wasa, inda tun da farko Edin Dzeko ya ci kwallaye 2, bayan da Henrikh Mkhitaryan ya ci kwallon farko ta wasan.

Hakan na nufin cewa Barcelona ta kammala a matsayi na uku a cikin rukunin da ta ke, batun da ke nuna cewa kungiyar ta Catalonia za ta sake fafatawa a gasar Europa a kaka ta biyu a jere.

Barcelona ta gaza hana kwallaye daga Sadio Mane da Eric Maxim Choupo-Moting da Serge Gnabry shiga ragarsu, duk kuwa da cewa a gida suke wannan wasa a gaban dimbim magoya bayansu.

Tun gabanin kammala wasan na jiya kaso mai yawa na magoya bayan Barca sun fice daga fili, yayin da wasu masu hakuri daga cikinsu suka yi saura don ganin abin da zai ture wa buzu nadi.