Yadda bikin karrama ’yan fim na African Magic na bana ya wakana | Aminiya

Yadda bikin karrama ’yan fim na African Magic na bana ya wakana

    Isiyaku Muhammed

A ranar Lahadin da ta gabata ce aka gudanar da bikin karrama ’yan fim na African Magic Viewers Choice Awards (AMVCA).

An gudanar da taron wanda shi ne karo na 8 ne a otel din Eko Hotel and Suites da ke Victoria Island a Jihar Legas bayan hutun shekara biyu.

Sai dai ba kamar wancan karon ba da ’yan Kannywood suka dawo da kambuna, bana sun sha kaye ne a matakai da dama.

A kyauyar Gwarzuwar Jaruma a dirama, jaruma Asabe Madaki da rawar da ta taka a fim din Voiceless ta fafata da jarumai irinsu Osas Ighodaro da Meg Otanwa da Bisola Aiyeola Asabe Madaki – Voiceless da Nancy Isime da sauransu, amma a karse Osas ce ta lashe kambun.

A matakin Zakaran Fim din Hausa, shirin Voiceless na Rogers Ofime ne ya doke shirin Sarki Goma Zamani Goma na Abubakar Maishadda da Bana Bakwai wanda shi ma na Abubakar Bashir Maishaddan ne.