✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Boko Haram Ta Yi Wa Masunta Kisan Gilla A Tafkin Chadi

Mayakan Boko Haram sun sun yi awon gaba da wasu masunta tare da kashe wasu a yankin Tafkin Chadi na jamhuriyar Nijar

Mayakan kungiyar Boko Haram sun tare masuntan Najeriya, suka yi awon gaba da wasu tare da kashe wasu a yankin Tafkin Chadi na jamhuriyar Nijar, a cewar wata majiyar tsaro da ke yankin tafkin Chadi gab da wurin da masunta suke. 

Arewa maso Gabashin Najeriya dai na fuskantar rikicin ta’addanci na tsawon shekaru 13, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba wasu kusan miliyan biyu da muhallansu tun daga shekarar 2009.

Kisan masunta a wannan makon na nuna yadda tashe-tashen hankula suka kunno kai a kasashen Nijar da Chadi da Kamaru, musamman a tsibirin Tabkin Chadi, inda mayakan suka kafa sansanoni na boye.

Mayakan sun kama masunta da dama daga tsibirin Kwatar Kaoulaha da ke yankin Diffa a ranar Lahadi zuwa Litinin da su ka gabata, inda suka kashe wasu tare da yin garkuwa da wasu saboda rashin bin umarnin barin yankin, kamar yadda masunta suka shaida wa kafar yada labarai ta AFP.

“Masunta da dama ne mayakan Boko Haram masu biyayya ga Baakura Buduma suka kashe tare da yin garkuwa da wasu saboda rashin barin yankin kamar yadda aka umarce su,” inji Kallah Sani, yayin da yake magana kan wani shugaban kungiyar Boko Haram na yankin.

Kallah bai iya bayar da takamaimai adadin masunta da aka kashe da kuma wadanda aka yi awon gaba da su ba, amma ya ce wadanda suka tsere sun shaida masa cewa masunta da dama suna tsibirin a lokacin da aka kai harin.

Sani yana cikin masunta kusan 300 da suka bi umarnin barin aiki na awa daya, inda suka bar sauran dukiyoyinsu ga mayakan.

“Sun gaya mana cewa za su kwashe duk abin da muka mallaka a matsayin ganima tun lokacin da gwamnatinmu ta kama kudadensu,” kamar yadda ya shaida wa AFP.

A ranar Juma’a ne kungiyar Boko Haram ta umarci masuntan wadanda galibinsu ’yan Arewa maso yammacin Najeriya ne da su fice daga yankin tare da barin dukiyoyinsu a matsayin ganima ga mayakan, inji wani masunci na biyu, Anas Ibrahim.

“Su (Boko Haram) sun zo ne da kwalekwale masu gudu biyu, suka umarce mu da mu bar tsibirin, kada mu dauki komai sai kayan da muke da su,” Ibrahim ya shaida wa AFP.

“Masu tayar da kayar bayan sun dawo ne a ranar Lahadi inda suka kashe wadanda suka samu, tare da lalata kwalekwalen su na kamun kifi don hana su tserewa,” in ji shi.

Wata majiyar tsaron Najeriyar ta tabbatar da faruwar lamarin da kuma kashe-kashen, inda ta ce ’yan ta’addan sun ji haushin yadda gwamnatin Nijar ta kama masu sayar musu da abinci da kuma wani mai safarar kudi.

Sai dai wani jami’in Jumhuriyar Nijar daga yankin ya shaida wa AFP cewa mayakan sun umarci mazauna yankin da su fice daga tsibirin, sanna suka kashe wadanda ba su yi hakan ba.

“Na ga gawarwaki 11 da suka hada da na masunta kuma a cikinsu akwai ’yan Najeriya uku, sauran ’yan Nijar ne,” inji majiyar.

Tafkin Chadi mai fadin fadama ya ratsa kan iyakokin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi kuma masu ikirarin jihadi suna amfani da kananan tsibiran da suke da su a matsayin mafaka.

A shekarar 2014 ne kungiyar Boko Haram ta kwace tsibiran da ke Tafkin Chadi bayan munanan hare-hare, lamarin da ya tilasta wa masu kamun kifi barin gidajensu.

Har yanzu kungiyar Boko Haram tana iko da tsibiran da ke gefen tafkin na Nijar.

A shekarar 2020 Kungiyar  ISWAP, wacce ta balle daga Boko Haram, ta kwace mafi yawan yankunan da Boko Haram ke iko da su, tare da barin masunta su koma bayan sun biya kudaden sarauta a lokacin da suka kama.