✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Buhari ya dana wa magajinsa tarko da tallafin mai

Siyasa ce ta sa Buhari ci gaba da biyan tallafin mai, amma wanda zai gaje shi zai shiga tsaka-mai-wuya

Masa sun bayyana cewa siyasa ce ta sa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dakatar da batun janye bayar da tallafin man fetur.

Malamin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano kuma masanin harkar man fetur da iskar gas, Farfesa Kamilu Sani Fage ya ce ci gaba da biyan tallafin wata dabara ce ta jam’iyyar APC na neman cin zaben 2023.

Ya ce, “Siyasa ce ta sa gwamnati ta jingine batun janye tallafi, amma idan sabuwar gwamnati ta hau, ko ta APC ce ko PDP, matukar akwai wadannan basuka (na Asusun Lamuni na Duniya wato IMF) a kanmu, to sai maganar janye tallafin mai ta sake tasowa.”

A ranar Talata Gwamnatin Buhari ta yi ma’ara-koma-baya cewa za ta ci gaba da biyan tallafin man fetur na tsawon wata 18, bayan kungiyar kwadago ta yi barazanar shiga yajin aiki kan shirin janye tallafin da gwamnati ke yi.

Sabon matsayin da gwamnatin ta dauka ya sa ake ganin gadar zare ta yi wa gwamnatin da za ta gaje ta kan  dambarwar tallafin da aka jima ana yi, ganin cewa yanzu wata 16 ne ya rage wa Gwamnatin Buhari.

Masana na zargi Gwamnatin Buhari da yin sakaci kamar magabatanta, wajen rashin samar da wani nagartaccen tsari da zai magance ainihin matsalar da ta haddasa takaddama kan biyan tallafin man da ya dade yana lakume biliyoyin Naira, yake kuma ci wa Najeriya tuwo a kwarya.

Sun bayyana cewa a yayin da wa’adin mulkin gwamnatin ya ke dab da karewa, da wuya ta iya yin wani abin a zo a gani kan tallafin man a cikin wata 16 da ya rage mata.

Siyasar ci gaba da biyan tallafi

Farfesa Kamilu Sani Fage ya ce abu ne mai wuya a yarda cewa ba tsoron shan kaye a zaben 2023 ba ne ya sa gwamnatin APC sauya matsayinta kan tallafin man.

“Lura da cewa zabe na kara matsowa ne ya sa gwamantin ta sauya shawararta domin ta san cewa idan ta yi gaban kanta ta janye tallafin, hakan zai yi mata illa.

“Na biyu, dole ta yi la’akari da matsalolin da kasar nan take ciki, kama daga Boko Haram da ’yan bindiga da kungiyar IPOB a yankinn kudi. Saboda haka babu hikima gwamnatin ta janye tallafin, ta kara wa kanta kanta matsala alhali kungiyar kwadago na barazanar shiga yajin aiki.

“Babu mamaki wannan ne ya sa gwamantin ta janye batun domin kada ta karo wa kanta yawan rikice-rikicen da take fama da su,” inji Farfesa Kamilu Fage.

Shi kuma Shugaban Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Ilorin, Farfesa Muhammed Alada, cewa ya yi, gwamnatin APC ta yi amfani da fikirarta ce wajen kawar da yiwuwar tashin wani sabon rikici musamman ganin yadda zabe ke kara matsowa.

“Zaben 2023 kara matsowa yake yi, saboda haka siyasa na da tasiri a duk abubuwan da za ta yi, abin da gwamnatin ta yi yanzu ba wani abu ba ne face jinkirta lokacin janye tallafin saboda ba yanzu ya kamata ta yi hakan ba.

“Ba a irin wannan lokaci ya kamata ta dauko wani abin da zai kawo mata rikici ba, wanda kuma tabbas janye tallafin zai haifar”, inji shi.

Tsugune ba ta kare ba

Farfesa Kamilu Sani Fage ya ce muddin Najeriya za ta rika cin bashi daga Asusun Lamuni na Duniya (IMF), maganar janye tallafi a Najeriya ba za ta kare ba, saboda neman janyewar na daga cikin sharuddan da IMF din take gindaya wa masu karbar bashi.

“Wannan ne ya sa gwamnati take kokarin cika sharadin da IMF ta sanya mata, shi ya sa suke kakaba wa mutane haraji ta yadda za su iya samun biyan bashin.

“Shi ya sa kashi 70 cikin 100 na kudaden da kasar nan take samu ana kashewa ne a wajen biyan bashi.

“Ba na tunanin maganar janye tallafin mai ta kare. Siyasa ce kawai ta sa gwamnati dakatar da maganar, amma idan sabuwar gwamnati ta hau, APC ce ko PDP, matukar akwai wadannan basuka a kanmu, to babu mmakawa sai batun janye tallafin ya sake tasowa.”

Yunkurin magudin zabe ne —PDP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP dai na zargin cewa ci gaba da biyan tallafin wani salo ne na jam’iyyar APC na tara kudaden yakin neman zaben 2023.

Kakakin PDP na Kasa, Debo Ologunagba, ya ce akwai lauje cikin nadi, lura da lokacin da gwamnatin ta dauki matakin da kuma yadda a shekarun baya-bayan nan yawan kudaden da ake kashewa wurin biyan tallafin ke ta tashin gwauron zabo, “saboda almundahana da kuma siyasa.”

“A 2017 kadai APC ta biya tallafin biliyan N144.3, amma a 2018 ya karu zuwa biliyan N878. A a 2019 ya sauka zuwa biliyan N551.2.

“A 2020 ya kara sauka zuwa biliyan N102, amma a 2021 ya karu zuwa tiriliyan N1.4, alhali yawancin mutane na zaune a gida saboda kullen COVID-19. To wa ya shan man da aka biya wa tallafi?

“Wannan almundahanar neman cin zabe ne da aka lullube da rigar tallafin man fetur, wanda kuma tsantsar tufka da warwara ce a tsarin tafiyar gwamantin,”inji shi.

APC ba ta da hujjar janye tallafi

Shi ma tsohon Shugaban Jami’iyyar PDP Reshen Jihar Legas, Kyaftin Tunji Sele (mai ritaya), ya zargi jam’iyiyar APC da rashin cika ko daya daga cikin alkawuran da ta dauka wa al’ummar Najeriya.

A cewarsa, duk da cewa ya kamata a soke biyan tallafin, ba gwamnatin APC ya kamata ta yi ba saboda mukarraban gwamnatin na yanzu su ne a baya suka yaki gwamntin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan lokacin da ta nemi soke tallafin.

Ya bayyana cewa abin takaici ne ganin yadda aka yi gyaran fuska ga sabuwar Dokar Man Fetur (PIA) wadda gwamnatin APC take bugun kirji da ita a matsayin babbar nasarar da ta samu, tun kafin a fara aiwatar da dokar.

A watan Fabrairu mai kamawa ne aka tsara PIA din za ta fara aiki, kafin Buhari ya bukaci tsawaita wa’adin aiki da dokar da wata 18.

Hutun jaki da kaya

Da yake nasa bayani kan dakatar da soke tallafin, masani daga Sashen Tsimi da Tanadi a Jami’ar Legas, Farfesa Ndubisi Nwokoma, ya ce siyasa ce ta hana gwamnati soke tallafin a yanzu, matakin da ya kira hutun jaki da kaya.

Ya ce, “Abin da suka yi yanzu wani kokari ne na kwatar kansu, saboda idan suka janye tallafin yanzu, tattalin arzikin kasar zai shiga tangal-tangal, wanda kuma zai kawo musu cikas idan zabe ya zo.

“Abu na biyu da ya sa suke ta kwan-gaba-kwan-baya a kan wannan abu shi ne ba su da wani zabi saboda sun riga sun kassara tallatin arzikin kasar nan.

“Na uku kuma shi ne rashin gaskiya. Ban tunanin mutanen da ke kan madafun iko a yanzu sun nuna cewa su masu gaskiya ne, domin su ne a baya suka kalubalanci Gwamnati Jonathan kan janye tallafin.”

Kawo yanzu dai APC ba ta ce uffan a kan wannan dambarwa ba.

Daga: Sagir Kano Saleh, Sunday M. Ogwu, Muideen Olaniyi, Idowu da Isamotu (Abuja), Abdullateef Aliyu (Legas), Clement A. Oloyede (Kano) da Mumini AbdulKareem (Ilorin).