✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Buhari ya kashe wa yankin Neja Delta N220bn

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta aiwatar da ayyukan cigaban al’umma 553 a yankin Neja Delta a cikin Shekara bakwai.

Gwamnatin Tarayya ta ce ta kashe zunzurutun kudi Naira biliyan 220 a cikin shekara bakwai don raya yankin Neja Delta.

Ta ce a shekara bakwai da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a kan mulki, an aiwatar da ayyukan cigaban al’umma 553 a yankin.

“Daga 2015 zuwa 2022, ma’aikatar  ta yi kammala ayyuka 553, sauran ayyukan kuma sun kusa kammaluwa a jihohi tara da ke yankin,” in ji Ministan Raya Yankin Neja Delta, Umana O. Umana.

Ya bayyana hakan ranar Laraba a wajen taron auna ayyukan gwamnatin Shugaba Buhari da ke gudana a Abuja.

Ta fuskar kare muhalli kuwa, Umana ya ce gwamnati na aiki tukuru wajen kare yankin daga fuskantar matsalolin ambaliyar ruwa da zaizayar kasa da sauransu.

Ya ce kudaden da aka ware wa yankin da aka sace wadanda EFCC ta kwato, za a sarrafa su wajen yi wa johohin yankin abubuwan more rayuwa.