✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bulala ta sa na tsere daga makarantar allo —Obasanjo

Obasanjo ya ce duk da cewa tsoron bulala ta sa yi har yanzu bai manta abubuwan da ya koya a makarantar allo ba.

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa tsoron bulala ne ya sa ya tsere bayan an sanya shi a makarantar allo.

Obasanjo, ya bayyana cewa tun yana karami aka sanya shi a makarantar allo, wadda ake kira Ile-Kewu a kasar Yarabawa, amma gudun bulala ya hana shi zama a ya mayar da hankali a makarantar.

“Kamar yadda na sha fada, tsoron dorina ce ta hana ni zama in koyi karatun Kewu (Larabci) yadda ya kamata. Har yanzu kuma, ban manta da wasu wake-waken da ake yi mana a lokacin da muke makarantar allo ba,” inji tsohon shugaban kasar.

Bulala da dorina na daga cikin hanyoyin ladabtar da almajiria da ake yawan amfani da su a makarantun allo.

Obasanjo, wanda a yanzu yake da digirin digirgira fannin Tauhidin Kiristanci, ya yi bayanin ne a taron nadin Sheikh Salis Alao Adenekan a matsayin Khalifan Darikar Tijaniyyah na Kasar Yarabawa da jihohin Edo da Delta.

A jawabinsa ga taron, Obasanjo, ya bukaci mahalarta da su dage wajen aikata ayyuka na gari domin samun dacewa da shiga Al-Jannah Firdausi.

Ya ce, “Babban manufar rayuwa ita ce samun shiga Al-Jannah, kuma duk wanda ya san darajar Al-janna, ba zai taba sakaci da addini ba a tsawon rayuwarsa.”

Taron dai ya samu halarcin wakilan ’ya’yan Shugaban Darikar Tijjaniya, Sheikh Ibrahim Niass, wadanda Sheikh Abdullah Baye Ibrahim Niass ya jarogranta daga birnin Kaulaha na kasar Senegal; Akwai kuma baki daga jihohin Kudu Maso Yammacin Najeriya da kuma jihohin Edo da Delta.

Da yake gabatar da jawabinsa, shahararren malamin Islama a Legas, Sheikh Sulaimon Faruq Onikijipa, ya shawarci shugabanni da su guji amfani da ikon da suke da shi yadda suka ga dama saboda son zuciya, domin akwai ranar hisabi.

Malamin wanda shi ne Babban Mufti na Ilori ya bukaci mabiya Darikar Tijaniyyah su zama tsintsiya madaurinki daya domin amfanin al’ummar Musulmi da kuma neman hakkinsu daga gwamnati.