✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Yadda Canjin Kudi Ya Rage Harkoki A Manyan Kasuwannin Kaduna

Rashin tabbas kan sauyin fasalin kudi ya kawo raguwar harkoki a wasu manyan kasuwannin da ke ci mako mako a Jihar Kaduna.

Rashin tabbas kan sauyin fasalin kudi ya kawo raguwar harkoki a wasu manyan kasuwannin da ke ci mako mako a Jihar Kaduna.

A Babbar Kasuwar Anchau da ke ci ranar Talata a Karamar Hukumar Kubau, da Kasuwar Makarfi ta ranar Laraba a Karamar Hukumar Makarfi, ’yan kasuwa na cikin rashin tabbas kan farashin amfanin gona saboda rashin sababbin takardun kudi a hannun jama’a.

Hakan ya haddasa rabuwar farashin hatsi zuwa kusan uku a kasuwannin, inda farashin sayen hatsai da sabon kudi daban da na saya tsoffi.

Aminiya ta gano farshin masu karbar taransifa zuwa banki ya fi yin sama, farashin mai saya kudi hannu kuma ya fadi kasa warwas saboda da rashin tsabar kudi a hannun ’yan kasuwa, da kuma rashin tabbas game da makomar amfani da tsoffin kudi ga wadanda suka zo cin kasuwar.

Sai kuma farashin kayan bukatar yau da kullum ya karu da kashi kusan 6 zuwa 8 a makon da ya gabata.

A wurin masu sana’ar POS kuwa, kamar yadda shugaban masu kasuwancin hatsi, Alhaji Yusuf Musa Mai Jakar Hatsi ya tabbatar cewa, “Na ga yadda kasuwar ta kasance a zahiri, an samu canji sosai ba kamar satin da ya wuce ba, duk da cewa al’umma suna cikin rudani saboda rashin tabbas, kuma ga rashin sadarwa ya yi nauyi.”

Sai dai kuma kayan sun kusan yin kunnen doki wajen farashi, domin bambanci bai wuce kashi uku zuwa hudu ba.

Wakilinmu ya gano buhun shinkafa samfarera na kaiwa har N20,000, buhun masara mara aure kuma N14,000, mai aure kuma N15,000.

Buhun dawa N15,000, farin wake N30,000, jan wake N33,000, buhun dauro kuma N26,000, sai waken soya silba N30,000, shi kuma waken soya idon fara N28,000.

Buhun busasshen timatir watau N20,000, busashen barkono N18,000, busasshen kubewa kuma N41,000.

A kayan gwari, danyen timatir yakan kai N1,500 kwando mai nauyin kilo 30, albasa N35,000, tarugu N8,000, shambo N7,500 farin gari kwaki N17,000.

Buhun garin kukar miya N36,000, gyada tsaba N90,000, babbar jarkar manja N33000, mangyada kuma N33,000, sai litar zuma N6,000.

Sai dai manoman sun koka kan tsabar takin zamani a yayin da amfanin gona suka yi kasa domin kuwa ana sayar da buhun Urea akan tsabar kudi har zuwa Naira dubu 23 buhu, NPK 15-15-15 shi kuma N24,500.