✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ciyar da ’yan firamare ke tafiyar hawainiya

Wasu daliban sun ce tunda suka dawo makaranta ba su taba ganin an kawo abincin ba.

Ga dukkan alamu shirin ciyar da daliban makarantun firamare da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shi don karfafa sanya yara a makarantun ya fara tafiyar hawainiya, inda a wasu jihohi shirin yake neman kwanciya da sirdi.

Shirin wanda duk da cewa na Gwamnatin Tarayya ne gwamnatocin jihohi ne suke gudanar da shi.

Wakilanmu sun bi diddigin yadda shirin yake gudana a wasu jihohi inda suka rubuta mana rahoto kamar haka:

Tun lokacin da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shirinta na ciyar da daliban makarantun firamare, Jihar Bauchi ta kasance daya daga cikin jihohin da suke cin gajiyar shirin duk da cewa ana samun jinkiri wani lokaci kafin a samu a fara ba da abincin.

Binciken da wakilinmu ya yi a makarantun firamare da dama da ke cikin garin Bauchi ya gano cewa shirin yana tafiyar hawainiya, saboda tunda aka dawo hutun wannan zangon karatu na farko an ciyar da daliban abinci na mako biyu ne kacal, a daidai lokacin da aka shiga mako na takwas da komawa makaranta.

Wadansu daliban ma sun ce tunda suka dawo makaranta ba su taba ganin an kawo abincin a makarantarsu ba.

Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Jinkai da Walwala, Hajiya Amina Katagum ya ci tura saboda ta tafi Abuja.

Wani jami’i da ke cikin masu kula da shirin wanda bai amince a bayyana sunansa ba, saboda bai samu izinin yin magana daga shugabanninsa ba ya ce daya daga cikin dalilan da aka fara yin wannan shiri shi ne domin a jawo ra’ayin yara, su rika zuwa makaranta musamman yaranmu na Arewa kuma a gaskiya hakan ya taimaka sosai wajen samun karuwar yaran da suke zuwa makaranta.

Ya ce yawancin yaran da ake ciyarwa a makarantun gwamnati yara ne wadanda ba su da galihu.

Sai dai ya ce wata babbar matsalar da ake fama da ita ita ce a kowane lokaci akan samu jinkiri wajen biyan wadanda suke raba wa yaran abinci kudadensu, ko wani lokaci akan samu jinkiri daga Abuja wanda wannan jinkirin ke jawo tsaiko na tsawon makonni ko wata kafin a samu a biya su su fara kai abincin.

Jami’in ya ce misali, a wannan zango dukkan jihohin da suke cin moriyar shirin an ba su kudadensu suna ciyarwa, amma na Jihar Bauchi har yanzu ba su samu ba saboda ba a kawo kudin da ya kamata a bai wa jihar daga Abuja ba.

Ya ce da zarar Ma’aiakatar Jinkai ta Tarayya ta biya kudaden za a koma ciyar da daliban, in ba a biya ba, ba su da ikon sa wadanda suke kawo abincin su rika kaiwa.

Jami’in ya ce a Bauchi an yi shiri mai kyau da yake tabbatar da cewa abincin da ake bayarwa, na isa hannun daliban, kuma a kowane lokaci ana nada jami’an da za su zagaya don tabbatar da hakan a kananan hukumomi 20 da ke jihar.

Ya ce a baya an samu ’yan matsaloli kama daga wadansu daga cikin masu ciyar da daliban da wadansu daga cikin malaman makaranta amma tunda suka dauki matakan sa-ido aka samu saukin lamari yanzu kowane dalibi yana samun abincinsa.

Sai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kara fadada shirin ya isa ga dukkan daliban makarantun firamare don inganta harkokin ilimi a kasar nan.

Mako uku ke nan da daina bai wa ’yan firamare abinci a Jihar Sakkwato

Ciyar da daliban firamare abinci da Gwamnatin Tarayya ta fito da shi a jihohin Najeriya, Jihar Sakkwato kamar sauran takwarorinta an soma shirin, sai dai hukumomin da abin ya shafa sun tabbatar da tsayuwar shirin mako uku da suka gabata, saboda suna jiran kudi daga Gwamnatin Tarayya kafin a ci gaba da rabon abincin a makarantun firamaren jihar.

Aminiya ta gano akan bai wa yara kunu da kosai ko shayi da burodi da kwai ko shinkafa daga ranar Litinin zuwa Juma’a.

Wani shugaban makaranta da ya nemi a sakaya sunansa ya ce yadda ake gudanar da shirin wani abu ne kawai na son rai da rashin makama domin su da suke shugabancin yaran ba su san yadda lamarin yake tafiya ba.

Ya ce ya kamata a gyara tsarin ciyarwa a inganta shi musamman abincin da ake bai wa yaran.

Shugaban ya ce ko a shirin ciyarwa da aka yi kafin cutar Coronavirus, masu dafuwar ne kawai da ’yan kwamitin rabo suke yin harkokinsu, ba a sa shugabannin makarantun wajen kula da ciyarwar, don haka wannan na musamman ne a nemi wadanda aka dora wa nauyi don sun san in da aka kwana.

Alhaji Musa Abubakar Girkau shi ne Manajan Kula da Ciyarwar da Dalibai a Jihar Sakkwato a zantawarsa da wakilinmu ya ce, “Tsaikon ciyarwa an same shi ne daga Abuja domin a can ne ake biyan kudin masu kaya.

“Mu a wurinmu in ka ba mu kaya akan sanar da mu lokacin da za su kare a duk kasa haka suke yi, kuma ba cewa ake yi tabbas in abinci ya kare nan take za a kawo wani ba, matan da suke dafa abinci ba kwangila ake ba su ba, ba su ciyarwa sai an ba su kudi, mun rubuta don a ba da kudin, in ba a bayar ba ta yaya za a raba abincin?”

Ya ce tunda aka fara shirin ba a cewa koyaushe sai an yi in dai kana biye da shi, abin da yake faruwa ke nan, mun rubuta mun kai masu har yanzu su ne ba su ba mu kudin ba, muna jiran a biya ne.

“Wannan tsaikon ba sabo ba ne a tsarin shirin, biyan da aka yi a kwanan baya, Sakkwato tana cikin wadanda suka samu a cikin lokacin, amma wadansu za ka samu sai gaba, misali ana iya bai wa Kebbi nata sai ta fara ciyarwa, Zamfara nata zai samu a wani mako, ka ga bayar da kudin bai cika zuwa a lokaci daya ba, haka suke abubuwansu,” inji Girkau.

Kan tsarin gaba daya, ya ce kowace mai dafa abinci ana sanya mata kudinta ne a asusunta na banki, ta je ta sayo abinci, ba a ce ta bai wa kowa ba, duk wadda ta bai wa wani kudi ba da yawun Gwamnatin Tarayya da ta jiha ba ne, in kuma suka yi aka yi ba daidai ba hukuma za ta hukunta su.

Ya ce matan da suke dafa abincin su ne ke raba wa yara babu hannun hedimasta a ciki, iyayen yara ke saya wa ’ya’yansu kwanon zuba abincin.

Ya ce a Jihar Sakkwato yaran da suke amfana da shirin sun kai dubu 360 da 978 daga aji daya na firamare zuwa aji uku, masu dafa abincin kuwa sun kai mata 3,458.

“Shirin nan ya samar da nasarori don ya sa yara zuwa makaranta sabanin baya kafin shirin, matan da suke cikin shirin sun samu abin dogaro da kai ta ciyar da iyalinsu da kansu,” in ji shi.

An fara shirin ciyar da ’yan firamaren a Jihar Yobe

Shirin Ciyar da Daliban Makarantun Firamare daga aji 1-3 sau daya a kullum ya kankama a Jihar Yobe.

Bayanan da Aminiya ta samo ya nuna cewa, shirin ya karbu a jihar lura da yadda shirin ya kara sa makarantun suna cika da dalibai fiye da baya.

Aminiya ta ziyarci Makarantar Firamare da ke Unguwar Nainawa a garin Damaturu, inda Shugaban Makarantar Malam Suleiman Abdullahi ya tabbatar da cewa shirin ya taimaka sosai wajen karuwar yawan dalibai.

Malam Suleiman ya kara da cewa, a yanzu haka akwai dalibai sama da dubu uku da suke amfana da wannan shiri.

Da Aminiya ta tuntubi Manajan Shirin a Jihar Yobe, Hajiya Fatsuma Accama, ta ce shirin ciyar da daliban firamare da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shi wanda aka fara a jihar a ranar 30 ga Satumban 2019, ya yi matukar tasiri a jihar musamman ganin jihar ba ta dade da farfadowa daga rikicin Boko Haram ba.

Hajiya Fatima ta ce a yanzu haka akwai dalibai dubu 106 da 797 da suke amfana da wannan shiri a kananan hukumomin jihar 17 kuma a yanzu haka akwai cibiyoyi 772 tare da masu dafa abinci kimanin 992 a fadin jihar.

Ta ce wannan shiri yana taimakawa matuka dangane da kara inganta ilimi a tsakanin al’umma.