✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ‘Cousin’ ke kawo tarnaki ga masoya

Wasu na ganin kozin na tafka aika-aika idan ba a yi masa shinge tsakaninsa da 'yar uwarsa ba.

Ka taba jin labarin wadanda daga wasan yaya da kanwa (wato Cousins a turancin Ingilishi) suka rikide zuwa masoya, suka aure miji ko budurwa ko saurayin wata?

Zara Muhammad, ta ba mu labarin yadda daga kanwa da yaya, sahibinta ya narke cikin kogin son ’yar innarsa, ya bar ta da ciwon zuciya.

A cewar Zara, da farko ba ta yi zaton wata soyayya, ballantana ma mai karfi na iya shiga tsakanin masoyin nata da cousin dinsa ba.

Amma gararin da Cousin din sahibinta da ta yi mata kutse ta kwace shi, ta jefa ta, da irin kwakwar da ta ci kafin ta samu ya dawo gareta, ya sa take kaffa-kaffa da duk wata Cousin dinsa, domin kada a koma gidan jiya.

Cousin kalma ce ta Ingilishi da ke nufin dan kawu, dan inna, dan goggo ko dan baffan mutum — wadanda ake kira abokan wasa a al’adar Bahaushe.

Yaya kuke ji a ranku idan kuka ga ana dasawa tsakin rabin ranku da Cousin dinsu da ba jinsinsu daya ba?

Sanannen abu ne cewa zamantakewar soyayya da aure aba ce da ta da ke mamaye zuciya, har ta sanya begen juna, musamman idan ta kasance cike da nuna wa juna kulawa da kauna da tausayi da sauransu.

Shi ya sa rabuwa da masoyi ko idan ya juya wa masoyinsa baya, yake shiga damuwa, wani lokaci har da rashin lafiya.

Daga yayana, kanwata

A wani lokaci wadanda ke zama kanwa uwar gami su jefa masoyi a cikin irin wannan hali su ne Cousin.

Daga yaya da kanwa ko tsokanar juna, sai Cousin su makale wa juna, su zame wa masoyan Cousin dinsu alakakai, kamar yadda aka yi wa Zara, ko da yake ta kwato abinta da kyar.

Matsalatar ta fi tsanani idan a gida daya aka taso ko dangantakar na da kusanci sosai tsakanin Cousin da masoyin mutum.

Shi ya sa yawancin masoya maza da mata ke ganin yayu ko kannen masoyansu na dangi a matsayin babbar barazana.

A al’adar Malam Bahaushe, ’ya’yan ’yan uwa abokan wasan juna ne, amma duk da haka, akwai iyaka tsakanin maza da ’yan uwansu mata, walau na kusa ko na nesa.

Sai dai yanzu zamani ya kawo yawaitar cudanya, saboda wasu dalilai, ciki har da kwaikwayon al’adun wasu kabilu, har ta kai ga wuce gona da iri a tsakanin Cousin da Cousin.

A wani lokaci hakan kan kai ga aikata abin kunya ko bacin rai, ko zama silar fasa aure ko mutuwarsa ko raba  masoya ko yin fitsara ko aikata babban fasadi.

Aminiya ta tattaunawa da wasu don jin irin rawar da Cousin ke takawa a soyayya ko zamantakewar aure.

Ya fi kowa illa —Budurwa

Wata budurwa, Aisha Danlami, na ganin cewa “Gaskiya shi Cousin ya fi kowa illa, saboda idan a gidanku ya taso kun zama daya, kun shaku kuma akwai abubuwan da za ku rika yi wanda idan saurayi ya gani ba zai dauka ba saboda zai dauka akwai wani abu a kasa.

“Shi kuma Cousin ba lallai akwai wani abu a tsakaninku ba ko da kuwa bai fito ya nuna ba.”

Aisha ta kara da cewa yana da matukar tasiri a rayuwar mace idan suka shaku.

“Shi Cousin ta wata fuskar shi ma ‘besty’ ne saboda kun shaku ga ’yan uwantaka watakila ma gida daya kuka tashi, komai tare ake yi.

“Saurayi mai kishi ba zai dauka ba, saboda yana ganin kulawar da Cousin ke bayarwa, kuma da za ka masa bayani ba lallai ya dauka ba, dole zai ga cewa kare shi ake yi.

“Kuma shi Cousin da ya ce auren mutum zai yi za a ba shi, saboda iyaye sun san cewa ku ’yan uwa ne shi ke nan haka za a yi ko da mace ba ta so an fi karfinta.”

Ya danganta

Ita kuwa wata matar aure, Nafisa Usman, cewa ta yi, “Ya danganta da mu’amalarsa da ke tsakaninsu, wani Cousin din za ka ga sun shaku sosai da sosai da ’yar uwarsa har ta kai ga matakin da za ka ga yana kishinta kuma kila shi bai isa aure ba ko kuma bai hada abin da yake iya yin aure ba.

“Wasu lokutan har da samarinta yana kishi, idan kuma ya ga abun ya fi karfinsa sai ya bari ta yi auren.

“Irin wannan shakuwar da suka riga suka yi da ita ko bayan an yi auren za a ga yana bibiyarta, idan ba ta nuna masa cewa ita matar aure ba ce ta shiga hankalinta.

“To, daga haka idan tana da miji mai kishi ya ga wannan Cousin ba muharraminta ba ne, wanda idan ta kai ta kawo akwai aure tsakaninsu, to sai ya ga ba dalilin da zai rika masa zarya a gida.

““Idan miji na da kishi bai kai zuciya nesa ba ko matar ba ta da fahimta, daga haka ne sai ka ga aure ya mutu,” in ji ta.

Cousin ya kusa kashe min aure

Wata matar aure daga Jihar Kano da ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana yadda wani dan uwanta ya kusa yin sanadin mutuwar aurenta.

“Wato ni sai da mahaifina ya shiga tsakaninmu sannan aka samu zaman lafiya ni da mijina.

“Shi Cousin din nawa mahaifinsa da mahaifina ’yan uwan juna ne, kuma wani lokacin a gidanmu yake kwana, akwai lokacin da muka yi soyayya irin ta yarinta haka, amma daga baya muka rabu.

“Tun lokacin da nake gida yadda muke wasa da shi Cousin din nawa, ashe abun ba ya yi wa mijin dana aura dadi, amma bai taba nuna min ba har sai bayan da muka yi aure.

“Ya sha zuwa gidana mu wuni ana hira, wasu lokuta ma shi yake taya ni wanke-wanke da shara haka, idan mijina ya dawo sai ya tafi.

“Ashe mijina ba ya son zuwansa haka, wata rana ya fito ya bayyana min, ni kuma na kasa fada masa saboda kar a dangi a min wani irin kallo.

“Ranar da mijina ya sake dawowa daga aiki ya same shi ranar haka muka kwana ana tashin hankali, daga karshe sai mahaifina ne ya raba fadan sannan ya cewa Cousin dina ya daina zuwa gidan tun da mijina ba ya so.”

Na kasa saurayin cousin dina na aure ta

Shi kuwa Ibrahim Murtala Ibrahim, ya bayyaa mana yadda a matsayinsa na Cousin ya kasa samarin matarsa kafin su yi aure.

“Da farko ba soyayya muke yi ba, amma lokacin dana fuskanci yadda wani saurayinta yake kafa mata dokoki a kaina, ya sa ni kuma na ce wallahi sai na yi soyayya da ita don na bakanta masa rai.

“Haka muka dinga dauki ba dadi, har ya hakura ya ce mu je mu karata ni da ita, daga baya kuma sai na zauna na yi tunanin cewa yanzu idan ba ta samu wani ba ban kyauta ba.

“Da yake matar mutum kabarinsa, haka na je kamar wasa muka fara soyayya, kuma da yake ’yar uwata ce ba wata matsala da muka fuskanta, ga shi yanzu wata shida da aurenmu.”

Mahangar addini

Malama Batulu Nabulusi Bako, ta yi tsokaci kan wannan maudu’i a mahangar addinin Musulunci.

“Idan muka koma doron addinin Musulunci, farkon magana ta Annabi (SAW), mu fara ta kanta saboda duk abin da aka sauka daga doron koyarwar Annabi Muhammad (SAW) za ka ga an sauka a kan layi ne.

“Manzon Allah ya yi magana a kan dangi, saboda dangi su ne mutuwa.

“Cousin na miji ne ko na mata a su ne ake samun fitina saboda zai shiga gidan mutum a duk lokacin da ya ga dama ko mai gidan na nan ko ba ya nan.

“Wani lokacin idan fitina ta gilma a kan haifi da, sai a ga yana kama da wani wanda ba za a taba dauka bakon haure ba ne a cikin gidan mutum ba.

“A zamanance kuwa, za ka ga Cousin suna wasan banza da zantukan banza da mace, sannan iyaye sun zuba ido ba sa hana su komai.

“Wani lokaci mace akwai shigar da iya mijinta za ta yi wa, amma ganin wannan dan uwanta ne sai ka ga ta zauna ba ta damu ba a cikin gida.

“Daga nan abubuwa da dama idan suka bullo za ka gani ai ba komai ba ne, dan uwanta ne yana mata wasanni ko ta yi kwalliya ya zo yana yaba kwalliyarta.

“Gaba daya wannan ba daidai ba ne saboda ba ya daga cikin koyarwar Manzon Allah (SAW).

“Sannan idan aka duba a tsari na tarbiyya ma wannan ba daidai ba ne.

“Ita kanta ’ya mace idan tana da tarbiyya za ta ga cewa ba daidai ba ne ta dinga cudanya da wani wanda ba dan uwanta na jini ba,” cewar Malama Batulu.

Mutane da daman na ganin ‘besty’ ne kadai ke kawo matsala a zamantakewar soyayya ko aure, amma wasu na ganin tasiri da illar da Cousin ke yi ta fi yawa.