Daily Trust Aminiya - Yadda cutar Kurona ta sa wa duniya takunkumi
Subscribe

Ana gwada Shugabar Ma’aikata ta Tarayya, Dokta Folasade Yemi-Esan da na’urar gwajin zafin jiki lokacin da za ta shiga xakin taro na Majalisar Zartarwa ta Qasa don gano cutar Kurona Hoto: Fadar Shugaban Qasa

Yadda cutar Kurona ta sa wa duniya takunkumi

A ranar Laraba 18 ga watan Maris ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirye-shiryenta na zaftare kasafin bana, inda take tunanin rage kusan Naira tiriliyan 1.5, sakamakon yadda cutar Kurona take barazana ga duniya, wadda zuwa yanzu harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen duniya suka samu tasgaro. Zuwa shekaranjiya Laraba an samu karuwar mutum uku masu dauke da cutar a Najeriya, inda yanzu suka zama mutum 8.

Za a rufe makarantu a wasu jihohin Najeriya

A shekaranjiya Laraba, gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma da wasu jihohin Arewa ta Tsakiya sun ce za a rufe dukkan makarantu a jihohinsu na tsawon kwana 30 saboda cutar ta Kurona.

Gwamnonin sun ce sun dauki wannan mataki ne domin kiyaye yaduwar cutar a wani taro da suka gudanar a Kaduna. A wata takarda da suka fitar bayan taron, wanda shugabannin gwamnonin yankunan, Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina da Gwamna Sani Bello na Jihar Neja, sun ce ya kamata a kulle makarantun ne daga ranar 23 ga Maris din nan.

Jihohin da suke shiyyoyin biyu dai sun hada da Kaduna da Kano da Katsina da Jigawa da Zamfara da Sakkwato da Kebbi daga Arewa maso Yamma. Sai Kwara da Neja da Filato da Benuwai da Nasarawa da Kogi daga Arewa ta Tsakiya.

Waxansu masu yi wa qasa hidima suna ficewa daga sansaninsu a Abuja bayan da aka sallame su saboda cutar Kurona

“Gwamnonin sun amince su  hada kai wajen nemo hanyoyin da za su kare mutanensu daga cutar ta Cobid-19. Kowace jiha za ta ci gaba da wayar da kan mutane da sauransu kan bukatar kula da lafiyar jiki da muhalli da wanke hannu da sauransu,” inji sanarwar.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina da Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da Abubakar Badaru da Jihar Jigawa da Nasir El-Rufa’i na Jihar Kaduna da Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato da Bello Matawalle na Jihar Zamfara da Abubakar Sani Bello na Jihar Neja. Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Gawuna ne ya wakilci jiharsa, sai kuma Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak da ya kasance tare da taron ta wayar salula.

Gwamnatin Jihar Legas ma ta sanar da cewa za a rufe dukkan makarantun gwamnati da na kudi daga ranar Litinin 23 ga Maris, 2020. A wata sanarwa da ya fitar a shekaranjiya Laraba, Kwamishinan Ilimi na Jihar Folashade Adefisayo ya ce an yi haka ne a kokarin dakatar da yaduwar cutar Kurona.

Jihar Legas ce inda aka fara samun bullar cutar a Najeriya mako biyu da suka gabata, kuma zuwa yanzu kusan jihohi 10 ne suka rufe makarantu a sassan Najeriya. Har hada wannan rahoto babu tabbas ko sauran jihohin kasar nan za su bi sahun wadannan jihohi wajen rufe makarantunsu. Jihar Enugu da Babban Birnin Tarayya ma su bi sahu inda suka ce za su rufe makarantu a ranar Litinin mai zuwa.

’Yar Buhari ta killace kanta

Daya daga cikin ’ya’yan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Buhari ta killace kanta daga jama’a bayan ta dawo daga kasar Ingila.

Ita da kanta ce ta killace kanta kuma mahaifiyarta A’isha Buhari ta bayar da sanarwar haka a shafinta na tweeter.

Majalisar Wakilai ta bukaci a yi addu’a

A nata bangare, Majalisar Wakilai ta bukaci a hana gudanar manyan tarurruka a fadin kasar  nan har sai an samu saukin cutar.

Dan majlisa Zakari Charles, dan Jam’iyyar PDP daga Kaduna ne ya kawo batun a karkashin muhimman abubuwan da suka shafi kasa. kuma majalisar ta bukaci hukomomin filayen jiragen sama su tabbatar sun yi duk mai yiwuwa wajen hana taruwar mutane da dama a wuri daya.

Bayan taruwa wajen ibada masallatai da coci-coci, a Najeriya ana taruwa domin daura aure da suna da sauransu. Bayan bukatar a hana tarurrukan, majalisar ta bukaci duk makarantun kasar a nema musu kayan gwaji, sannan ta bukaci a samar da rana daya da za a yi wa kasa addu’a.

Majalisar ta bukaci dukkan wakilanta su yi gwaji domin sanin matakin lafiyarsu, sannan ta hana baki zuwa majalisar.

A jiya Alhamis kuma Majalisar Dattawa, ta dakatar da sauraren ra’ayin jama’a tare da haramta wa baki kai ziyara harabar majalisar.

An samu karin mutum 5 dauke da cutar a Najeriya

Ma’aikatar Lafiya ta ce an samu karin mutum biyar da suke dauke da cutar da hakan ya sa yanzu akwai masu cutar 8 ke a kasar nan.

Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire ya ce an samu karin mutum biyar da suke dauke da cutar kuma uku daga cikinsu sun fito ne daga Amurka, biyu kuma daga Dubai. Ya ce, “Har yanzu muna kokarin tattara bayanan mutanen. Biyu daga cikin ukun da suka zo daga Amurka ’yan Najeriya ne, uwa da danta dan mako 6. Wannan yaron shi ne mafi karancin mai dauke da cutar a Najeriya. Na uku kuma dan Amurka ne da ya shigo iyakar kasa, kuma shi ne mutum na farko da ke dauke da cutar da ba ta jirgi ya shigo ba.”

Ministan ya ce sun karbi bayanan kowane daga cikinsu, kuma suna kokarin nemo dukkan wadanda suka hadu da masu cutar.

Ya bukaci ’yan Najeriya su kwantar da hankalinsu, inda ya ce an bude wajen aikin gaggawa da Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya za ta jagoranta tare da hadin gwiwar masu ruwa-da-tsaki a bangaren.

Aminiya ta gano cewa hudu daga cikin masu cutar suna Legas ne, daya kuma a Ekiti.

Ana bibiyar wadanda suka yi hulda da Ba’amurken da ya mutu a Ekiti

Gwamnatin Jihar Ekiti ta yi karin haske kan wani dan asalin jihar da ya kamu da cutar bayan ya tuka wani dan Amurka. Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Dokta Mojisola Yaya-Kolade, ta ce ana zargin dan Amurkar daga Jihar Birginia tare da rakiyar wata ’yar asalin Jihar Ekiti ne ya harbi mutumin dan shekara 38 da cutar COBID-19 bayan saukarsa a Najeriya.

Sanarwar ta ce dan Amurkar da ’yar rakiyarsa sun zo Najeriya ne ranar 3 ga Maris inda suka sauka a filin saman Murtala Mohammed da ke Legas. Ta ce binciken farko-farko ya nuna cewa dan Najeriyar da ya kamu da cutar shi ne ya dauki dan Amurkar da ’yar rakiyarsa a mota zuwa Ibadan, wurin da suka shafe tsawon kwanaki kafin su isa Ado Ekiti ranar 13 ga Maris. “Kwana guda kuma bayan isarsu ne sai dan Amurkar ya kamu da rashin lafiya, kuma aka dauke shi zuwa wani asibitin kudi, kafin a mayar da shi Asibitin Koyarwa, inda a can ne ya mutu,” inji sanarwar.

Ta ce hukumomin asibitin sun ankarar da kwamitin kada-ta-kwana mai yaki da cutar Kurona a Jihar Ekiti inda aka dauki samfurin jinin Ba’amurken da abokan tafiyarsa biyu.

Ta ce, “Gwajin da aka yi wa direban da ya kai su, ya nuna cewa cutar Cobid-19 ta harbe shi, yayin da gwaji ya nuna ita ’yar rakiyar ba ta dauke da cutar, shi kuma gwajin da aka yi wa mamacin a wannan lokaci bai kammala ba,” kamar yadda BBC Ya ruwaito.

Asalin cutar da yadda take

Annobar cutar Kurona ta kashe dubban mutane a sassan duniya, bayan bullarta a watan Disamban da ya gabata a kasar China. Bakuwar cutar wadda aka fi sani da Coronabirus ta yadu zuwa kasashe fiye da 150, abin da ya sa hukumomi daukar matakan hana yaduwarta da suka hada da killace garuruwan da aka samu bullarta, da makarantu da cibiyoyin kasuwanci da wuraren haduwar jama’a da kuma hana shigar baki daga wuraren da aka samu bullar cutar.

Wani kwararre a fannin lafiya kuma tsohon Ma’aikacin Hukumar Lafiya ta Duniya Nasir Sani Gwarzo, ya yi wa BBC bayani kan asalin cutar da yanayinta da yadda take yaduwa da kuma matakan kariya.

Asalin cutar Kurona

A bayaninsa kan asalin cutar, da dalilin da ya sa ake kiranta coronabirus, wanda ya ce ba shi ba ne asalin sunanta ba ya ce:

“Coronabirus ba shi ne asalin sunan kwayar cutar ba, suna ne na danginta, ya ce birus na da dangi biyu: masu sanda daya da masu sanda biyu.

“Masu sanda daya (RNA) kuma sun kasu kusan 17, to a cikin danginsu akwai dangin corona (coroabaride), shi ya sa ake kiran ita sabuwar kwayar cutar corona (Nobel Coronabirus),” inji shi.

Masanin ya ce dalilin da ya sa ba a ayyana wa bakuwar cutar suna ba shi ne saboda ba a taba samun irinta ba a tarihi, sai wannan karo.

Yanayin cutar

Ya ce, alamun cutar na kamanceceniya da na mura mai tsanani a cewarsa, “Tana sa tari da ciwon kai da zubar majina da ciwon makogoro da sauransu.”

Sai dai ya ce bambancinta da mura shi ne: “Ta fi mura tsanani tunda tana haddasa zazzabi mai tsananin gaske kuma tana iya yin kisa.”

Ya ce a cikin kowane mutum 200 da suka kamu da ita, za ta iya kashe mutum daya ko kasa da haka. “Wannan shi ya sa ake damuwa a kanta, inji shi.

Yadda cutar ke yaduwa

Dokta Sani Gwarzo ya ci gaba da cewa, cuta ce mai saurin yaduwa fiye da yadda ake zato. “Ana ganin idan mutum daya ya kamu, a cikin yini guda zai iya shafa wa mutum uku zuwa tara. Sannan a cikin kwana shida adadin zai iya ninkawa wajen hawa tara a cikin kankanin lokaci,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Misali idan mutum yana cikin taro, sai ya yi atishawa ko ya yi kaki ya tofar ko kuma ya face majina da hannunsa to, zai iya shafa wa mutane a hannayensu.”

Matakan kariya

Game da matakan kariya daga cutar, masanin lafiyar ya ce kula da tsabta za ta taimaka kwarai, duk da yake cutar bakuwa ce ba a gano kanta ba ko samo rigakafinta.

Ya shawarci wadanda suke mura su daina shiga cikin taron jama’a ko a ba su hutu har su samu sauki. Sannan a bar tagogi a bude yadda iska za ta rika wucewa, musamman idan mai murar ba shi kadai ba ne a dakin.

Abin da ya biyo bayan bullar cutar

Gidan rediyon BBC ya rairayo manyan abubuwan da suka faru bayan bullar cutar ta Kurona kamar haka:

 • Fiye da mutum dubu 200 ne suka kamu da cutar a fadin duniya, kuma sama da 8,000 suka mutu.
 • Najeriya ta haramta wa ’yan kasashe 13 shiga kasarta, wadanda cutar ta fi yi wa kamari, yayin da aka samu wadansu mutum biyar sun kamu da cutar, cikinsu har da wata mata da jaririyarta mai mako shida a duniya.
 • A Burkina Faso ta sanar da mutuwar wata mace mai shekara 62 kuma mai ciwon suga.
 • Karin mutum biyu sun mutu a Masar dan kasar mai shekara 70 da ’yar Italiya mai shekara 78 a wani asibitin da aka kebe su.
 • Coronabirus ta shiga dukkan jihohin Amurka 50 bayan Jihar West Birginia ta bayyana rahoton bullar cutar a ranar Talata.
 • Sama da mutum 1,700 ne suka makale a kan wani babban jirgin ruwa a tekun Cape Town da ke Afirka ta Kudu sakamkaon fargabar wadansu daga cikinsu na dauke da cutar.
 • A Birtaniya an samu fiye da mutum 700 a cikin awa 24, jimilla sama da mutum 2,600 ke nan na wadanda suka kamu. Yankunan Scotland da Wales sun sanar da rufe makarantu.
 • Kasar Spain ta rufe dukkan otel-otel a yakin da take yi da cutar musamman a birnin Madrid.
 • Kungiyar Tarayyar Turai ta fara aiwatar da haramcin shiga kasashen kungiyar daga wasu kasashe. Shugabannin kungiyar sun amince cewa shingen da wasu kasashe suka saka a cikin gida za a cire su.
 • Rufe iyakar kan tudu tsakanin Amurka da Kanada- iyaka tsakanin kasashen biyu da ta fi kowace girma a duniya- za a rufe ta. Babu karin bayani game da rufewar amma shugabannin kasashen biyu sun tabbatar da faruwar haka.
 • Tsohon Kyaftin din Super Eagles ta Najeriya John Mikel Obi ya bar kungiyar Trabzonspor bisa amincewar bangarorin biyu ’yan sa’o’i bayan ya ce ya kamata a dakatar da wasannin gasar Turkiyya na Super Lig a kasar Turkiiyya saboda Coronabirus.

Babu cutar a Kano

Gwamantin Jihar Kano ta musanta jita-jitar da aka yi ta yayatawa cewa an samu bullar cutar a jihar, a cewarta dukkan mutum ukun da ake zargi da cutar da aka gwada su sakamakon ya nuna cewa babu cutar a tare da su.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce babu wani abu mai kama da cutar  a tare da mutanen da aka gudanar da gwaji a kansu, don haka babu cutar a jihar gaba daya.

Kwamishinan ya bayyana cewa a yanzu haka gwamnatin jihar ta shirya tsaf wajen daukar duk matakan da suka kamata don yakar cutar

Hanyoyin kariya daga cutar

Dokta Aminu Mohammed, likita ne a Asibitin Kwararu na Murtala Mohammed da ke Kano, ya yi wa Aminiya karin haske game da cutar, inda ya ce cutar tana da alaka da numfashi domin da farko tana kama mutum ne kamar yadda mura take yi.

Ya ce matakan da za a bi don kariya su ne “Mutum ya rika yawan wanke hannu  da sabulu. A kuma guji yawan taba fuska da hannu musamman baki ko hanci kasancewar ita cutar tana da alaka da abin da ya shafi hanci.”

Haka kuma ya ce a rika amfani da abin kunshe hanci a duk lokacin da mutum zai shiga cikin taron jama’a. Kuma idan mutum yana atishawa ko tari ya rika rufe bakinsa da hancinsa.

Likitan ya shawarci mutane da zarar sun kamu da mura su garzaya asibiti don neman magani saboda idan aka tari abin da wuri ana samun nasara.

Haka likitan ya shawarci jama’a  su rika yin sarace da ruwan zafi da zarar sun ji wani alamu na mura ko toshewar numfashi saboda yin sarace yana kashe duk wasu kwayoyin cuta da ke nasaba da numfashi.

Gwamnatin Legas ta haramta taron sama da mutum 50 a masallatai da coci-coci

A wani mataki na kare yaduwar cutar Kurona Gwamnatin Jihar Legas ta haramta taruwar jama’a a wuraren ibada a daukacin fadin jihar. Kwamishinan Al’amuran Cikin Gida na Jihar Anofiu Elegushi ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba bayan wani taron da ya yi da masu ruwa-da- tsaki kan al’amuran addinai a jihar. Taron ya samu halartar Babban Limamin Jihar Sheikh Suleiman Abou Nolla da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen jihar, Aledander Bamgbola.

Babban Limamin Jihar, Sheikh Abou Nolla ya ce abin da gwamnatin ta yi abin a yaba ne, sannan ya bukaci Musulmin jihar su bi umarnin gwamnati.

Gwamnatin Tarayya ta rage kasafin kudi da Naira tiriliyan 1.5

A wani mataki na daban, Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na rage kasafin kudin bana da Naira tiriliyan 1.5. Ministar Kudi da Tsare-tsare, Hajiya Zainab Ahmed ce ta sanar da haka lokacin da take zantawa da manema labarai a shekaranjiya Laraba.

Idan ba a manta ba, Majalisa ta amince da kasafin kudin a kan farashin mai Dala 57 kan ganga, amma yanzu farashin ya fadi zuwa tsakanin Dala 28 zuwa 30.

Da aka tambaye ta ko nawa za a yanke, sai ta ce, “Mun aike wa kowace ma’aikata tsarin da za ta bi wajen rage kasafinta. Amma dai za mu rage kusan Naira tiriliyan 1.5.”

Ministar ta ce gwamnati za ta ci gaba da biyan albashi kuma ba za rage ma’aikata ba, amma za a dakatar da daukar sababbin ma’aikata ko maye gurbin wadansu.

Ansaruddeen ta dakatar da Sallar Juma’a a masallatanta

Kungiyar Ansaruddeen ta Najeriya ta dakatar da Sallar Juma’a da manyan tarurruka a masallatanta a fadin kasar nan sakamakon cutar ta Coronabirus.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Alhamis ta ce ta dauki wannan mataki marar dadi ne lura halin da ake ciki na dakatar da Sallar Jum’a da duk wani taro da ya wuce na mutum 50. Ta ce dakatarwar za ta fara aiki ba tare da bata lokaci ba har sai abin da hali ya yi.

“Matakin ya zama wajibi ne don hana yaduwar cutar Coronabirus kamar yadda Kungiyar Malaman Musulunci ta Duniya ta riga ta bayar da fatawa a kai,” inji sanarwar wadda ta ce kungiyar za ta bi umarni da shawarwarin da gwamnati ta bayar amma za a sanar da jama’a duk wani ci gaba da ake samu dangane da matakin.

“Mun san jama’a da dama ba lallai su ji dadin wannan labari ba, amma ya kamata su san cewa saboda ceto al’umma aka yi haka.Don haka muna shawartar mutane su ci gaba da yin sallolinsu a gidajensu su rika bin matakan tsabta da sauran ayyukan ibadah’’ kamar yadda BBC ya ruwaito daga sanarwar.

Saudiyya ta rufe masallatai

Hukumomin Saudiyya sun rufe masallatan kasar in ban da masallatai biyu masu alfarma na Ka’aba da na Annabi (SAW), tare dakatar da yin Sallah a cikin jama’a a cewar Kamfanin Dillacin Labaran Kasar. A baya mahukuntan Saudiyya sun hana masu zuwa aikin Umarah shiga kasar saboda dakile yaduwar cutar.

An dauki matakin ne makonni kadan kafin azumin watan Ramadan da Musulmi kan yi tururuwa zuwa kasar domin  yin Umarah. An tabbatar da mutum 133 sun kamu da cutar a Saudiyya zuwa ranar Litinin da yamma.

Sai dai tuni aka samu mutum shida da suka warke daga cikin wadanda suka kamu a baya, yayin da sauran masu dauke da cutar ke killace a cibiyoyin lafiya daban-daban a fadin kasar. Kafofin labarai sun ambato Minsitan Lafiya na kasar, Tawfik Al-Rabiah, yana hasashen cewa za a samu karuwar masu dauke da cutar Kurona nan gaba a kasar.

Mutanen Iran na kutsawa wajen ibadar mabiya Shi’a duk da hani kan haka

Wadansu mutanen Iran sun kutsa da karfi sun shiga wajen ibada na Fatima da ke birnin Kum, bayan an rufe na wucin-gadi saboda annobar cutar Kurona.

Wani dan majalisa, Ali Motahhori ya yi kira a gurfanar da su gaban shari’a, yana mai cewa baya ga barazanar lafiya da hakan ke jawowa, suna kuma bata Musulunci.

Sai dai babban mai kula da wajen ibadar Ayatollah Mohammed Saeedi, tun a lokacin rufewar ya ce ya kamata a bar wajen a bude saboda “waje ne na samun waraka’’ kuma “ya kamata a karfafa wa mutane gwiwar zuwa wajen.’’

A Iran mutum 1,135, suka rasu daga cikin mutum 17, 361 da suka kamu da cutar, inda ta zamo ta uku bayan China da Italiya.

Ana ci gaba da binciken maganin Coronabirus

Ana ci gaba da binciken kan maganin warkar da cutar Coronabirus.

Wasu kamfanonin samar da magunguna na Sanofi da Regeneron na gudanar da gwaji kan kwayar maganin Kebzara ga sama da mutum 400 da ke fama da cutar inda aka fara gwajin a New York.

Masu bincike a Spain kuma na amfani da wani magani na daban, wanda aka taba amfani da shi wajen warkar da cutar kanjamau kan mutum 200 da nufin rage lokacin da suke dauke da cutar.

Akwai kuma maganin zazzabin Maleriya na Chlorokuine da ake amfani da shi ga wadansu mutum 3,000 da ke fama da Coronabirus, inda ake fata zai hana wa cutar hayayyafa.

Nahiya daya da ba a samu bullar cutar ba a duniya

Wannan nahiya ita ce Antarctica. Baya ga dimbin tsuntsayen penguins da ke wajen, akwai ayarorin bincike daban-daban a nahiyar. Amma har yanzu babu mai dauke da cutar ko alamunta a can.

Masu bincike ’yan Birtaniya sai da suka shafe kwana 14 a killace kafin su tafi yankin da ke Kudancin duniya, kuma an dauki matakai da dama koda wani abu zai taso da zai shafi aike musu da kayayyaki.

Akan samu masu bincike har kusan 1,000 duk shekara daga kasashe daban-daban da ke zuwa Antarctica.

Asibiti mafi kusa da yake yankin yana da nisan dubban mila-milai daga kasar Chile.

A daina firgita mutane kan cutar Kurona – Dokta Rijiyar Lemo

A hudubar da ya gabatar a ranar Juma’ar mako jiya a Masallacin Juma’a na Dorayi Karama da ke Birnin Kano, Sheikh Muhammad Sani Rijiyar Lemo, ya ce faruwar annoba ba bakon abu ba ne ga dan Adam, sai dai a wannan lokaci an kururuta batun tare da jefa tsoro ga mutane, inda ya bukaci al’ummar Musulmi su dauki cutar Kurona a matsayin wata jarrabawa da Allah Ya kaddara kuma yin imani da kaddara daya ne daga cikin rukunan imani da bai kamata Musulmi su daga hankalinsu a kai ba.

Dokta Muhammad Sani Rijiyar Lemo ya ce, Allah Ya riga Ya kaddara komai da zai faru da kowane mutum, don haka wajibi ne kowane Musulmi ya kasance yana da cikakken imanin cewa amfani da cutarwa ba su samun mutum face da yarda da kuma izinin Allah, don haka idan Allah Ya jarrabi mutane da cuta babu mai kwaranye ta daga gare su, sai Allah. Kuma idan Ya shafe su da alheri babu mai iya kawar da shi daga gare su.

“Don haka Musulmi su hakikance a zukatansu cewa Allah ne Yake shafar mutane da rashin lafiya ko cuta kuma Shi ne zai kwaranye su, inda ya kawo misalai da dama kan rayuwar annabawa da salihan bayi daga al’ummar Annabi Muhammad (SAW).

Ya ce, wani lokaci kuma Allah Yakan saukar da annoba ko masifa ga jama’a ne saboda miyagun ayyukan da suke aikatawa inda a irin wannan hali wajibi ne Musulmi su tuba su koma ga Allah.

Kuma ya bukaci Musulmi su kasance masu tawakkali ga Allah kan duk abin da ya zo gare su tare da kiyaye sabubba da shari’a ta sani kan kiwon lafiya da sauransu.

Dokta Rijiyar Lemo ya ce irin wannan annoba da take faruwa a duniya take daga hankali, azaba ce ga kafirai da munafukai da masu sabo da sauran masu aikata laifuffuka, amma rahama ce ga masu imani inda ya kawo misalai daga Hadisin da A’isha (RA) ta tambayi Annabi (SAW) game da annoba, inda ya ce: “Lallai ita azaba ce da Allah Yake aikata ga wanda Ya so kuma Ya sanya shi rahama ga mumini. Kuma babu wani bawa da annoba za ta same shi a wani gari, amma ya zauna ya yi hakuri bai gudu daga cikinsa ba face ya samu ladan shahidi.”

Don haka Allah Yana azabtar da bayinSa da irin wannan annoba, kuma idan mumini ya mutu a irin wannan annoba to insha Allah ya mutu yana  ai shahada, ko yana da ladan shahidi.

More Stories