✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda da ya yi wa matar mahaifinsa ciki a Nasarawa

Matar ta bayyana yadda rashin haihuwa bayan shekara 19 da aure ya jefa rayuwarta cikin rudani

Wata matar aure a Jihar Nasarawa ta bayyana cewa dan mijinta ne ya dirka mata ciki.

Matar ta dora laifin kan mijin nata da ta ce ya gabatar mata da dan nasa ne a matsayin dan uwansa ba dan cikinsa ba.

“Auren saurayi da budurwa muka yi ni da mijina, wanda yanzu ya rasu.

“Mun fara samun matsala ne bayan na shafe shekara biyar ba tare da na yi ko batar wata ba.

“Hakan ne ya sa surukata ta dinga tsangwama ta har shi ma ya goyi bayanta saboda rashin samun ciki da na yi,” a cewarta.

Ta kara da cewa, “Wannan halin da nake ciki ne ya sanya ni jan hankalin dan mijina ba tare da na san cewa dansa ba ne.

“Sai bayan na samu ciki, lokacin yaron ya samu gurbin karatu a Kwalejin Ilimi ta Akwanga ne na san cewa dan cikinsa ne.

“Bayan yaron ya rasu a hadarin mota a kan hanyarsa ta zuwa Kwalejin Akwanga ne ’yan uwan mijina suke sanar da ni cewa dan cikinsa ne.

“A lokacin ne fa na gano cewa ai cikin da nake dauke da shi na dan mijina ne,” kamar yadda ta bayyana wa jaridar The Nations.

Ta ce ta shafe shekara 19 da ta yi da aure ba tare da haihuwa ba ne ya jefa ta a halin da ta tsinci kanta.

The Nation ta ruwaito matar tana bayyana yadda mijinta ya kawo wani matashi mai shekara 17 a matsayin dan uwansa, alhali kuwa dan cikinsa ne.