✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dambarwa ke cinye shugabannin EFCC

Gwamnati kan yi taka-tsantsan tare da bincike sosai kafin ta zabo mutanen da take nadawa su jagoranci Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arziki…

Gwamnati kan yi taka-tsantsan tare da bincike sosai kafin ta zabo mutanen da take nadawa su jagoranci Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC).

Abin mamaki shi ne yadda shugabancin jagororin hukumar da aka yi zuwa yanzu ke karewa da zargin sun aikata ba daidai ba ko kuma wata dambarwa.

Ko da yake wasu na ganin shugabannin hukumar na tabo wasu shafaffu da mai ne shi ya sa ake komawa a zarge su da aikata wani abun da za a bincika, har daga karshe a tube su ba tare da kotu ta tabbatar da zargin ba.

Daga lokacin da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya kirkiri EFCC zuwa yanzu ta samu shuhabanni hudu: Nuhu Ribado da Farida Waziri da Ibrahim Lamorde sai kuma Ibrahim Magu.

Nuhu Ribadu

Shi ne ya fara jagorantar hukumar bayan Obasanjo ya zabo shi daga rundunar ‘yan sanda a shekarar 2003 zuwa 2007, lokacin da shugaban kasa Umaru Musa Yar’aduwa ya cire shi.

Nuhu Ribadu ya yi ayyuka da dama na yakar cin hanci da rashawa wanda har ya gabatar da shaidar kudi naira biliyan N15 a gaban kotu da wani gwamna da ya yi kokarin sayensa domin dakatar da binciken sa da yake yi.

Ya kuma bankado wasu manyan laifuka, amma daga karshe aka sauke shi kuma aka nemi a kama shi, har sai da ya tsere daga kasar.

Ko da yake aikin, an yi ta zargin sa da kasancewa karen farautar da gwamnatin Obasanjo ke amfani da shi wajen gallaza wa wadanda suke takun saka da gwamnatin.

Da farko babban sufetan ‘yan sanda na kasa, Mike Okiro ya umcrci Ribadu da ya ajiye aikin EFCC domin zuwa ya halarci wani kwas na wucin gadi na shekara daya a Kuru, Jihar Filato.

Mutane da kungiyoyi sun yi allawadai da matakin amma daga karshe, hukumar kula da ma’aikatan ‘yan sanda ta kore shi daga aiki, aka kuma cire shi daga mukaminsa.

Farida Mzamber Waziri

Bayan Nuhu Ribado, Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya nada Farida Mzamber Waziri wadda ta shugabanci hukumar daga watan Mayu 2008 har zuwa Nuwamba, 2011.

Nasarorin Farida a yaki da cin hanci da rashawa sun hada da kama mataimakin shugaban jam’iyya PDP mai mulki, bisa laifin rashin biyayya ga kasa da kuma badakalar kwangilar Naira biliyan 84, har kotu ta daure shi na wata 30 a kurkuku.

Ta kuma kwato naira biliyan N17 daga tsohon Sufeta Janar na ‘yan sanda, Mustapha Adebayo Balogun.

Sannan ta binciki tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu da na Ribas, Peter Odili da Joshua Dariye na Filato da Saminu Turaki na Jigawa da kuma Jolly Nyame na Taraba.

A yayin da take EFCC, Farida Waziri ta ce watar da wasu jami’an gwamnati ke yi na kamanceceniya da tabin hankali, ta kuma bayyana takaicin cewar kotu ba ta yanke musu hukumci ba.

Daga karshe, Shugaba Goodluck Jonathan ya sallame ta bisa zargin nuna son kai da zabar mutanen ta ke bincika.

Ta kuma yi ta samun sabani da Ministan Shari’a na wancan lokacin Muhammad Bello Adoke, wanda ya zarge ta da zama a kan binciken gwamnan Bayelsa, Timipreye Sylva.

Ibrahim Lamorde

Ya ja ragamar EFCC daga watan Nuwamba, 2011 har ya kammala shekarunsa hudu, amma Shugaban Muhammadu Buhari bai ba shi damar zarcewa ba.

Ibrahim Magu

wadda ake yi masa lakabi da mai rikon amana kuma marar tsoro wajen yaki da cin hanci da rashawa ya shugabanci Hukumar a matsayin riko tun daga 9 ga watan Nuwamba 2015 har zuwa lokacin da aka dakatar da shi ranar 7 ga watan Yuli, 2020.

Magu wanda daya ne daga jami’an bincike na farko da Nuhu Ribado ya yi amfani da su wajen yakar cin hanci da rashawa.

An kuma yi masa lakabi da sarkin yakin yaki da cin hanci da rashawa ga gwamnatin Buhari.

Daga cikin binciken da Magu ya jagoranta karkashi Ribado akwai na Gwamna Bukola Saraki, wadda hakan ya jaza durkushewa bankinshi na Societe Generale Bank of Nigeria, da kuma binciken tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori.

A shugabancinsa, EFCC ta kwace kadarori da kudaden badakala na biliyoyin Naira da miliyoyin Daloli da Famafami daga hannun tsoffin jami’an da masu ci da attajirai da ‘yan siyasa.

Kazalika EFCC ta yi nasarar ganin kotu ta yanke hukuncin dauri ga wasu manyan mutane da kama da laifin satar dukiyar kasa da wasu shari’o’in suka shafe shekaru ana yi.

Amma shi ma Magun ana zargin sa da mayar da EFCC ‘yan amshin gwamnati wajen takura wa ‘yan adawa da kuma kawar da kai daga wasu fitattun zarge-zarge.

Bayan haka an sha zargin hukumar da gazawa wajen bincike da gabatar da gamsassun hujjoji domin yanke wa masu laifi hukunci, lamarin da ya sa hukumar ke yawan shan kaye a kotu.

Kalubalen da Magu ya fuskanta

Kawo yanzu, Magu ya fuskanci kalubale iri-iri da suka hada da matsalar sa da Farida Waziri a lokacin da ta gaji mai gidansa Nuhu Ribado.

Farida ta zarge Magu da boye takardun binciken wasu manyan mutane inda ta sa aka bincike gidansa amma ba a kama shi wani laifi ba.

Daga nan aka mayar da shi hedikwatar ‘yan sanda kafin daga baya aka daktar da shi daga aiki ba tare albashi ba.

Bayan Ibrahim Lamorde ya karbi Farida Waziri, ya nemi a dawo da Magu EFCC su yi aiki tare. Amma da ya tura wa babban sufeton ‘yan sanda jerin sunaye da sunan Magu a ciki, sai aka cire sunan Magu, sai da shugaban kasa ya sa baki sannan aka maido shi.

Haka nan kuma Magu bai taba samun amincewar Majalisar Tarayya ba domin a nada shi a matsayin cikakken shugaban hukumar, sakamkon zargin sa da rashawa da hukumar DSS ta yi a rahotonta ga majalisar.

An kuma zarge shi da mallakar kadarori a ciki da wajen Najeriya da suka zarce matsyin albashinsa.

Haka kuma an yi ta samun takun saka tsakaninsa da Ministan Shari’a da zargin yin kafar ungulu a yaki da gwamnatin shugaba Buhari ke yi da rashawa.

Daga karshe rahoton Ministan Shari’a Abubakar Malami ya sa an dakatar da shi bisa zargi 22 da ya gabatar wa shugaban Kasa.

Kwamitin ya ce a takatar da Magu ne domin samun damar gudanar da cikakken bincike kan zargin karkatar da kudaden gwamnati da aka kwato daga wadanda suka wawure.

Yaki da cin hanci da rashawar da Magu ya yi a tsawon lokacin da ya kwashe a matsayin Shugaba ya taba manyan mutane da dama.

Ya kwato kudade da daure wasunsu, hakan wasu ke ganin cewar anya ba bi baya?