✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dan majalisa ya jagoranci kubutar da mutum 10 daga hannun masu garkuwa

A makon da ya gabata, wani dan majalisa daga jihar Kwara ya yi ta maza inda ya jagoranci ceto mutum 10 ‘yan mazabarsa daga hannun…

A makon da ya gabata, wani dan majalisa daga jihar Kwara ya yi ta maza inda ya jagoranci ceto mutum 10 ‘yan mazabarsa daga hannun masu garkuwa da mutane.

Dan majalisar wanda ke wakiltar mazabar Banagbe ta daya da ta biyu da ke yankin Bani a karamar hukumar Kaiama a jihar Honurabul Sa’id Baba Ahmad ne ya jagoranci ba-ta-kashin da ta kai ga kashe masu garkuwar su biyar.

Kazalikaa, sun sami nasarar kwato makamansu da suka hada da bindiga kirar AK-47 guda biyar.

A zantawarsa da Aminiya, dan majalisar ya ce a ranar Lahadin da ta gabata ne wasu masu garkuwar suka sace mutum 13 ‘yan mazabarsa a yankin gandun daji na jihar Oyo da ke  kan iyakar jihar da jihar Kwara da misalin karfe na yamma akan hanyarsu ta dawowa daga cin kasuwa.

Yace bayan da labarin ya riske shi ne ya ga cewa bai ga ta zama ba inda ya ankarar da rundunar ‘yan sanda, sannan ya kira al’ummar Fulanin yankin da shugaban kungiyar Miyetti-Allah reshen jihar Oyo.

Ya ce nan take su ka shirya zama a kashegarin ranar da aka yi garkuwar, jama’a ‘yan sa kai suka haxu daga cikin ‘yan sintiri na kungiyar Fulanin da ta ‘yan kato da gora da ma sauran jami’an soji da na ‘yan sanda su ka shiga dajin.

Ya ce, “Mun shiga dajin a ranar Talata kwana biyu da kame mutanen sai dai bayan kwana guda wato ranar Laraba ‘yan sanda da sojin sun fita daga dajin suka barmu a can domin a lokacin sun kasa jure wa a cigaba da aikin tare da su.

“Amma a namu bangaren da suka hadar da ‘yan sakai na kungiyar Miyetti-Allah da sauran ‘yan sintiri mun cigaba da zama a dajin har Allah yasa muka gano su muka kuma yi nasara akansu bayan mun Kwana hudu muna nemansu.

“Mun kirga kanmu a lokacin aikin, muna da mutum 600 da doriya mun kuma raba kanmu ne sashe sashe.

“Bangaren da muka cimma masu garkuwar mun haura mutum 100, bayan da muka gano su sai mu kayi musayar wuta inda cikin ikon Allah nan take muka hallaka mutum hudu daga cikinsu wadanda muka tabbatar da gawarwakinsu, yayin da wasu suka gudu da raunin harsashi a jikinsu.

“Mun kuma kashe karin mutum guda da shima ya bude wuta a wani sashi daban na dajin.

“Munyi nasarar kubutar da mutum 10 cikin 13 da aka yi garkuwar da su, ragowar 3 kuma ‘yan uwansu sun riga sun biya kudin fansa a boye inda masu garkuwar suka sallamo su kwana daya kafin mu cin musu,” inji dan majalisar.

Daga nan sai ya shawarci gwamnati da ta  yi amfani da ‘yan sa kai wajen magance matsalar ‘yan bindiga domin su suke da juriyar shiga dazuzzuka.