✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dauke wutar lantarki ya girgiza tattalin arzikin China

Matsalar dai ta shafi kusan kaso 44 cikin 100 na tattalin arzikin kasar.

Matsalar daukewar wutar lantarki a wasu biranen Arewa maso Gabashin kasar China ta jefa miliyoyin gidaje da masana’antu cikin duhu tare da fuskantar barzanar katse ruwan sha a wasu yankunan.

Jaridar Global Times da ke kasar a ranar Talata ta rawaito cewa dauke wutar wacce ta zo da ba-zata dai ta shafi biranen Jilin da Liaoning da kuma Heilongjiang, sakamakon takaita yawan wutar da gwamnati ta yi.

An dai fara takaita yawan wutar ne a ranar Alhamis sakamakon karancin gawayi, ba tare da sanar da mutane gabanin daukar matakin ba.

Hakan dai inji jaridar, ya fusata mutane da dama sannan ya tilasta kashe fitilun kan tituna da ma sabis din kamfanonin sadarwa a wasu yankunan.

Wata masana’anta a birnin Jilin ta yi gargadin cewa dauke wutar zai iya sa a katse samar da ruwan sha, yayin da kafar yada labaran kasar ta CCTV ta rawaito cewa sai da wata masana’anta a birnin Liaoning ta garzaya da ma’aikatanta 23 asibiti sakamakon gurbacewar iska lokaci da wasu injina suka daina aiki sakamakon iftila’in.

“Sau takwas ana dauke mana wuta a yau kawai…ni kam ma bani da ta cewa,” inji wani fusataccen mazaunin birnin Liaoning, kamar yadda ya wallafa a shafin sada zumuntar kasar na Weibo.

Kazalika, shi ma wani mutum ya yi korafin cewa matsalar ta tilasta wa manyan kantina rufewa ba kamar yadda suka saba ba, wasu kuma suka koma amfani da kyandura a cikinsu.

Matsalar dai ta kuma shafi masana’antu da dama a kasar wacce ke zama ta biyu a girman tattalin arziki a duniya, ciki har da kamfanonin Apple da na Tesla.

A wani labarin kuma, cibiyar Goldman Sachs ta yi harsashen cewa matsalar ta shafi kusan kaso 44 cikin 100 na tattalin arzikin kasar, lamarin da ya kai ga tafka asarar kaso daya cikin 100 na ma’aunin tattalin arzikin kasar (wato GDP) a watannin hudun karshen 2021.