✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda daukewar ruwan sama zai shafi jihohi 7 a Arewa —Nimet

Za ta shafi Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Kastina, Neja, Yobe da Borno

Ana sa rai yanayin rashin ruwan sama zai shafi jihohin Sakkwato da Zamfara da Yobe da Kebbi da Kastina da Neja da ma wasu sassan Jihar Borno, kamar yadda hukumar nazarin yanayi ta Najeriya (NiMet), ta sanar.

Babban Daraktan Nimet, Farfesa Mansur Bako Matazu ya snaar a ranar Talata cewa jihohi kamar Oyo da Kwara da Ekiti Filato da Abuja su ma za su fuskanci yanayin zafin amma ba mai tsanani ba.

Ya bayyana hakan ne a Abuja a wajen taron rattaba hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna kan horarwa a kan nazarin yanayi tsakanin hukumar da Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Umudike, a Jihar Abiya.

Ya ce jihohin Kudu maso Gabas da na Kudu maso Kudu za su samu ruwan sama matsakaici in ban da Jihar Kuros Riba da za ta samu kasa da hakan.

A watan Yuli da Agusta, hukumar NiMet din ta ce yanayin karancin ruwan zai dan sassauta kuma jihohin da abin ya shafa za su dan samu ruwan sama fiye da yadda aka saba.

Game da tasirin hasashen, Farfesa Matazu ya ce ya kamata manoma su shuka iraruwan da suka dace da abin da hasashen ya gano saboda kauce wa tafka hasara mai girma.

Ya ce lallai ne manoma su shuka amfanin gonar da zai jure wahalhalun rashin isasshen ruwan saman.

“Abin da ake nufi da bushewar yanayi a nan ba wai rashin ruwan saman gaba daya ba ne, a’a yanayi ne na daukewar ruwan saman na kwana 10 zuwa mako biyu tsakanin lokatun da aka samu ruwan yadda ya kamata.

“Dole manoma su yi amfani da dabarun da suka dace ta hanyar shuka iraruwa masu jure fari a daidai lokacin da za a samu daukewar ruwan saman.

“Yana da kyau manoman su zama masu aiki da shawarwari da matakan kandagarki wadanda NiMet ke bayarwa lokaci zuwa lokaci domin rage radadin illar da daukewar ruwan za ta haifar na karamin lokaci,’’ kamar yadda ya ba da shawara.