✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dubban mutane suka yi dafifin bankwana da gawar Pelé

Pelé ya rasu yana da shekara 82 a duniya sakamakon ciwon daji da ya sha fama da shi.

Dubban masoya ne suka taru don yin bankwana da gwarzon Dan Kwallon Kafar Duniya Pelé.

Tsohon dan wasan tsakiyar Brazil, Ze Roberto da dan Pelé, Edinho ne suka taimaka wajen daukar akwatin gawarsa yayin da Neymar da Vinicius Junior na Real Madrid suka aike da furanni don nuna alhininsu.

Ana sa ran shugabannin duniya da dama za su halarci jana’izar dan wasan ciki har da sabon zababben shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva.

Za a ajiye gawar Pelé a filin wasa na Santos na tsawon awa 24 don bai wa jama’a damar yin bankwana da shi.

Tuni Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya isa Brazil don halartar jana’izar Pele.

Dubban mutane sun kafe riguna masu dauke da hotunan tsohon dan wasan da ya buga wa kungiyar Santos wasa 659, ya kuma zura mata kwallaye 643.

Dubban mutane daga sassan duniya ake sa ran za su yi wa birnin Santos dafifi don nuna alhininsu game da rashin gwarzon dan kwallo da duniya ta yi.

Pelé dai ya rasu yana da shekara 82 bayan ya sha fama da ciwon daji na tsawon lokaci a asibitin Albert Einstein da ke birnin Sao Paulo.

Shi ne dan wasa daya tilo a tarihin duniya da ya taba lashe Gasar Kofin Duniya har sau uku.

Kuma shi ne dan wasa mafi karancin shekaru da ya taba lashe gasar da shekara 17 a duniya.