✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun matar da ke kokarin tsallakewa da jariran sata zuwa Amurka ta cika

Asirinta ya tonu ne lokacin da ta je ofishin jakadancin Amurka dake Abuja da nufin samun takardun tsallakewa da su.

Dubun wata mata ta cika a jihar Abiya bayan ta yi yunkurin tsallakewa da jariran sata zuwa kasar Amurka a matsayin ’ya’yan cikinta.

Tun da farko dai Hukumar Yaki da Fataucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce ta kulle wani gidan kyankyasar jarirai da aka gano a garin na Aba da ake zargi da hannu dumu-dumu a badakalar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, NAPTIP ta ce binciken kan gidan kyankyasar jariran ya biyo bayan cafke ’yar Najeriyar dake Amurkan da aka yi da jarirai biyu da ta yi ikirarin ita ta haife su amma bincike ya nuna sabanin haka.

 A cewar Hukumar, tuni ta cafke mutane uku, ciki har da matar ’yar asalin Najeriya mazauniyar Amurka, yayin da ta kaddamar da bincike don kamo mamallakin gida, Mista Nwamaka Ijeoma Agozie, wanda tuni ya cika wandonsa da iska.

Gidan dai wanda ake wa lakabi da Nwamaka Herbal Centre, na yankin Ikpokwu ne a Karamar Humumar Ukwa ta jihar Abiya kuma an rufe shi ne bayan mai shi ya yi kememe wajen amsa gayyatar da NAPTIP ta yi masa.

NAPTIP ta ce, “Wacce ake zargin ta ke ikirarin kasancewa Fasto a Amurka ta ce bata san wanda ya yi mata cikin ba a can saboda ta kwanta da maza da dama a shekarar 2018.

“Ta ce lokacin da take da juna-biyun ta je wani asibiti a birnin Atlanta amma likitoci suka ce su ba su ga kowanne irin ciki ba.

“Hakan ne ya sat a yanke shawarar zuwa Najeriya wurin asibitin Mista Nwamaka wanda ya bata wani irin magani, cikin ’yan sa’o’i kuma ta haife ’yan tagwaye. Ta kuma ce sai da ta biya Naira miliyan biyu kudin karbar haihuwa.

“Sai dai asirinta ya tonu ne lokacin da ta je ofishin jakadancin Amurka dake Abuja da nufin samun muhimman takardun da za su bata damar tsallake Najeriya da yaran a matsayin ’ya’yan cikinta.

“Ofishin dai ya nuna kokwanto a kan ikirarin nata, inda daga bisani ya yi mata Gwajin Kwayar Halitta (DNA) wanda sakamakonsa ya nuna ba ma kawai ba ita ta haife su ba, amma yaran ma ba su da alaka ta jinni da juna,” inji Babban Daraktan NAPTIP, Imaan Sulaiman Ibrahim a cikin sanarwar.

Hukumar ta ce guduwar mamallakin gidan ne ma ya kara jefa mata shakku kan sahihancin ikirarin matar.