✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda El-Rufa’i ya cire dansa daga makarantar gwamnati a cikin sirri

A lokacin mutane sun dauka sanya shi a makarantar zai inganta harkar ilimi a Jihar.

Gwamna Nasir El-rufai ya cire dansa, Abubakar Sadik daga Makarantar Gwamnati ta Kaduna Capital School cikin sirri bayan abin da mutane da yawa suka bayyana a matsayin yunkurinsa na nuna wa duniya cewa kamar kowa yake.

Yayin da saka shi a makarantar lokacin ya sami yabo daga sassa daban-daban, amma cirewar an yi ta ne ba tare da kowa ya sani ba, lamarin da wasu suke kallo a matsayin yaudara.

Sai dai babu tabbas kan ko Gwamnan ya canza shawararsa ne, a daidai lokacin da wasu masharhanta ke cewa matakin ba zai rasa nasaba da yawan sace dalibai daga makarantun gwamnati ba, musamman a jihar ta Kaduna da kuma makwabtanta, ko matsin lamba daga ’yan uwa ko kuma rashin tabbas a kan ingancin makarantun gwamnatin.

Mazauna yankin da makarantar take sun nuna takaicinsu kan yadda gwamnan ya cire dan nasa, watanni kadan bayan ya fara cudanya da sauran ’ya’yan talakawa a inuwa daya.

Mutane da dama dai a lokacin sun dauka sanya Sadik a makarantar gwamnati zai inganta harkar ilimi a Jihar.

“Abin takaici ne matuka, saboda gaba daya lamarin ya fi kama da wasan kwaikwayo ko yaudara,” inji Ibrahim Yaro, wani mazaunin Kaduna.

“Ya kamata shugabanni su zama masu magana daya su rika cika alkawuran da suka dauka.

“Bayan ya cire dan nasa daga makarantar, yanzu kuma ya dage sai kara kudi yake yi yana korar malamai.

“Gaskiya mu fa ba mu fuskanci inda ya dosa ba, ya kamata wani ya yi masa magana,” inji shi.

Sai dai har yanzu Gwamnatin Kaduna ta ki ta ce uffan kan lamarin.

Ranar da aka kai shi makarantar

Gwamna Nasir El-Rufa’i lokacin da ya kai dansa makarantar gwamnati
Gwamna Nasir El-Rufai a lokacin da ya kai dansa makarantar gwamnati.

A lokacin da El-Rufai tare da rakiyar matarsa Ummi suka kai dan nasu Sadik mai kimanin shekara shida Makarantar Kaduna Capital a 2019 a matsayin wani mataki na cika alkawarin yakin neman zabensa, mutane da dama sun rika jinjina masa a matsayin gwarzo da ya daura damarar inganta harkar ilimi a Jihar Kaduna.

Makarantar dai na daya daga cikin makarantu mafiya suna da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya.

Watanni bakwai bayan saka shi a makarantar, Aminiya ta ziyarce, ta inda ta iske Sadik El-Rufai wanda a lokacin yake ajin Firamare na 2B, har ya yi sabbin abokai, ya kuma fara sabawa da yanayin da ma malamanta, yayin da aka samar da cikakken tsaro don gadin makarantar.

A lokacin dai kasancewarsu a makarantar ta karfafa gwiwar iyaye da dama suka cire ’ya’yansu daga makarantun kudi, tare da tunanin cewa ba za su yi nadamar kai ’ya’yansu makarantun gwamnati ba, kuma makomar ’ya’yan nasu za ta yi kyau.

To sai dai Aminiya ta gano cewa tuni Gwamnan ya shammaci jama’a, inda ya cire dan nasa a sirrance ya kuma saka shi a wata makarantar ta daban wacce ba a bayyana ba, ya bar mazauna yankin cikin mamaki.

Wakilinmu ya gano cewa an cire Sadik daga makarantar ne jim kadan da janye kullen COVID-19 wanda ya tilasta rufe makarantu. Sai dai ko bayan sake bude makarantun ba a sake ganin keyar Sadik ba.

Mutane da dama sun bayyana takaicinsu a kan abin da gwamnan ya yi, wanda suke ta’allakawa da matsalar rashin tsaro, karancin kayan aiki, suna masu cewa matakin ba kawai saba alkawari da yaudara ba ne, a’a har ma da wasa da hankulan mutane.