✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gobarar gas ta kashe ’yan gida daya

Mutum uku sun rasu, ciki har da karamin yaro a gobarar iskar gas.

Mutum uku ’yan gida daya sun rasu, ciki har da karamin yaro a gobarar iskar gas.

Mutanen sun rasu ne a yammacin ranar Laraba a yayin da wani mai gyara ke tsaka da kara gas a wani firij da gas dinsa ya yi kasa.

“Abin da ya faru shi ne suna girki da ice a waje. Ana cikin haka kuma suna kokarin kara gas, shi ne abin ya yi bindiga.

“Mutum uku sun rasu, ciki har da karamini yaro. ’Yan gidan ne abin ya ritsa da su. Ginin gidan na gargajiya ne,” inji Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Ogun, Fatai Adefala.

Wani ganau ya bayyana wa Aminiya cewa gas din ya yi bindiga ne da misalin karfe uku na ranar Laraba a unguwar Oke-Egunya da ke garin Abeokuta na Jihar.

“Ana kara wa firij din iskar, a lokacin akwai wani da ke girki da ice, daga nan ne wutar ta tashi, gas din ya yi bindiga,” inji shi.