✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ganawar Buhari da Gwamnonin APC ta kasance

Gwamnonin sun amince shugaba Buhari ya zabi wanda za a ba kujerar shugabancin jam’iyyar.

A Yammacin ranar Laraba ce Kungiyar Gwamnonin APC karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ta gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Bayan ganawarsu ta sirrance, Gwamnonin sun ce sun tattauna da Buhari kan batutuwa da dama musamman game da babban taron jam’iyyar da zai gudana ranar Asabar inda za a zabi shugabannin jam’iyyar.

Ganawar na zuwa a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke ci gaba da fuskantar baraka da rashin jituwa tsakanin jiga-jiganta kan babban taro na kasa da kuma zaben shugabanninta.

Wadanda suka halarci zaman sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da gwamnoni 16 daga jihohin Kebbi, Filato, Kogi, Yobe, Ogun, Kaduna, Ekiti, Ebonyi, Imo, Neja, Jigawa, Kwara, Zamfara, Nasarawa da Borno.

Bayanai dai sun ce tuni jam’iyyar ta kebe wa yankunan kasar mukamai daban-daban, ciki har da kebe wa yankin Arewa ta Tsakiya kujerar shugaban jam’iyya na kasa.

Shugaba Buhari na kokarin ganin an kauce wa kada kuri’a wajen zaben shugabanni, a maimakon haka yake neman a sasanta tsakanin ‘yan takara.

Da wannan ne gwamnonin jihohi suka amince da tayin shugaban kasar inda suka ce za su goyi bayan duk wanda shugaba Buhari ya ce a ba kujerar shugabancin jam’iyyar.

Sai dai wasu kusoshin jam’iyyar sun bayyana cewa ba su yarda da wannan tsari ba, kamar tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, wanda ya ce zai ci gaba da fafutikar neman kujerar shugaban jam’iyyar duk da cewa ba yankinsu ne aka kebe wa kujerar ba.

Haka kuma Yarin ya bayyana cewa a ganinsa bai wa wani yanki ko wani mutum mukamin ba tare da zabe ba, rashin adalci ne.