✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ganawar Buhari da Oshiomhole ta kasance

Ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomhole a fadarsa ta Aso Villa da ke Abuja.…

Ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomhole a fadarsa ta Aso Villa da ke Abuja.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, shi ne ya jagoranci Oshiomhole wanda yake sanye da wando da taguwa mai kama da ta jami’an tsaro da ya saba sanyawa har Ofishin Shugaban Buhari.

Wannan shi ne karo na farko da Oshiomhole ya ziyarci shugaban kasar tun bayan da Kwamitin Gudanarwa na APC da aka kaddamar da kwamitin riko na jam’iyyar bayan rikicin jagoranci da ya mamaye ta.

Aminiya ta tabbatar da cewa ganawar shugaban kasar da Oshiomhole ta tabo batun zaben gwamnan Jihar Edo, wanda za a gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.

Zabe na gaskiya

Oshimhole ya bai wa manema labarai tabbaci bayan ganawarsa da Shugaba Buhari cewa jam’iyyar APC ce za ta yi nasara a zaben, ya kuma ce ya nemi shugaban kasar ya samar da tsaro mai inganci a yayin zaben.

Ya kuma ce ya bukaci Shugaba Buhari ya tabbatar an gudanar da tsaftataccen zabe mai nagarta da kuma cikin lumana ta tsari na gaskiya da adalci.

Ya kuma nemi a hukunta duk wanda aka kama yana take doka, ko tayar da zaune tsaye ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake goyon baya ba.