✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gasar karatun Al-Kur’ani ta kasa ke gudana a Kano

Mahaddata masu fafatawa a musabakar fun fito ne daga jihohi 36

Mahaddata 300 na fafatawa a Gasar Karatun Al-Kurani ta Kasa karo na 35 da da ke gudana a Kano.

Shugaban Kwamitin Shirya Gasar, Farfesa Abubakar Yelwa Muhammad, ya ce mahaddatan na fafatawa ne a rukuni shida, ciki har da rukunin Izu 60 da Tafsiri.

Farfesa Yelwa ya ce an zabo mahaddata masu fafatawa a musabakar ce daga jihohi 36 ciki har da birnin tarayya.

“Manufar ita ce hada kan matasan Najeriya su dabbaka koyarwar Musulunci da inganta kyakkyawar alakar da za ta haifar da zaman lafiya a cikin al’umma,” inji Shugaban Musabakar.

Ya bayyana cewa Kwamitin Alkalan Gasar na da alkalai shida da aka zabo bisa cancanta, wadanda kuma tsoffin masu fafatawa ne Gasar Karatun Al-Kur’ani ta Kasa.

“Shida na aiki daya kuma yana jiran ko-ta-kwana, kuma an kebe su ne bisa kwarewa da gogewarsu a fannonin da suke aikin,” inji shi.

Farfesa Yalwa daga Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Usmanu Dan Fodio da ke Sakkwato, ya kuma bukaci mahalarta taron gasar da su kiyaye dokokin da aka shimfida na na takaita yaduwar cutar COVID-19.

A nasu bangaren, mahalarta sun nuna gamsuwa da yadda ake gudanar da gasar.

Gasar karatun Alkur’anin karo na 35 ya samu dimbin mahalarta da suka hada da malaman addinin Islama, dalibai, yan jarida da sauran jama’a.