✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gobara ta lakume shugana a Kasuwar Gamzaki a Adamawa

Gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Shaguna da dama sun kone a wata gobara da ta tashi a Babbar Kasuwar Gamzaki da ke yankin Jimeta a Yola, babban birnin Jihar Adamawa.

Alamu sun nuna cewa gobarar ta afku ne da sanyin safiyar ranar Alhamis lamarin da ya sanya daruruwan ’yan kasuwa garzaya don ganin halin da dukiyarsu ke ciki.

Majiyoyi sun ce wutar ta shi ne sakamakon rashin wutar lantarki a wasu shagunan kasuwar.

Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Bashir wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin a ziyarar da suka kai wa wadanda lamarin ya shafa, ya ce gwamnati za ta taimaka musu wajen sake kafa sana’o’insu.

“Mun gode wa Allah da Ya sanya wutar ta tashi ne da rana kuma mutane sun fara fitowa, da an tafka asara mai yawa,” in ji shi.

Ya ja hankalin wadanda abun ya shafa da su dauki kaddara, ya kuma ce gwamnatin jihar za ta taimaka musu.

Ya yaba da tsarin da ’yan kasuwar suka kafa na amfani da wutar lantarki ta hanyar kunna wuta da misalin karfe 9 na safe zuwa 6 na yamma.

Ya kara da cewa, “Gobarar ta tashi ne a shagunan sayar da kayan da wuta na iya tashi da wuri kuma an yi nasarar dakile ta saboda hadin kan da aka bayar wajen kashe ta kafin isowar jami’an kashe gobara.”

Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar Gamzaki, Alhaji Ali Kachalla, ya zagaya da jami’an gwamnatin don gane wa idonsu irin barnar da gobarar ta yi a kasuwar.