✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gwamnoni ke facaka da biliyoyin Naira a zaben kananan hukumomi

Kano ta kashe N2.3bn, Kaduna N1bn, Filato N1bn Jigawa da Gombe sun yi gum

Gwamnoni kan kashe biliyoyin Naira wurin gudanar da zaben kanan hukumomin jihohinsu da jami’iyyu masu mulki ke lashe gaba daya kujerun da aka takara ba jami’iyyun adawa sun samu ko da kujera daya ba.

Bugu da kari, gwamnonin ba sa bayanin yawan kudaden da suke kashewa wurin gudanar da wadannan zabuka da masu fafutikar siyasa ke gani a matsayin izgili ga tsarin dimokuradiyya.

Wannan ya sa ake zargin gwamnonin na fakewa ne da sunan gudanar da zaben kanana hukumomi suna wawure kudaden gwamanti.

Hakan ya sa wasu kwararru ke kira da a rushe hukumomin zaben jihohi (SIECs), a yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 gyaran fuska ta yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta rika gudanar da zaben kananan hukumomi.

A fahimtarsu, hakan zai sa dukkannin jam’iyyun siyasa cikakkiyar damar samun ciyamomi da kansiloli ta hanyar fafatawa wurin kafa shugabannin a matakan al’umma.

A wakon jiya wasu jihohi sun kasa samu ko sisin kwabo daga Naira biliyan 123.348 da Gwamnatin Tarayya ta raba wa jihohi.

Kudaden sun yi wa jihohin ta leko, ta koma ne saboda ba su cika sharudan da Gwamnatin Tarayya ta gindaya ba na rabon gudanar da kudaden da suke samu a fili, gaskiya, tsantsaini, tara kudaden shiga da kuma biyan basuka.

Yadda jihohi ke gudanar da zaben kananan hukumomi

Rahottani daga jihoin sun nuna duk da biliyoyin da ake kashewa, zaben kananan hukumominsu na dabaibaye da rudani ta yadda jam’iyyu masu mulki ne ke lashe akasarin kujeru a zabukan shugabannin kananan hukumomi da na kansiloli.

Sannan in banda Jihohin Kano, Ribas, Borno, Kaduna da Filato, ragowar jihohin da suka gudanar da zaben kananan hukumomi da wakilanmu suka tuntuba, sun ki bayyana yawan kudaden da suka kashe a kan zabukan.

Kano ta kashe biliyan N2.3

Zaben kananan da aka gudanar a baya-bayan nan shi ne na Jihar Kano, ranar Asabar, 16 ga Janairu, 2021.

Zaben wanda babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kaurace wa, aka kuma samu karancin fitowar jama’a ya lakume Naira biliyan 2.3.

A tattaunawarsa da mu, Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce ana kashe kudi sosai wurin gudanar da zabe a tsarin dimokuradiyyar da Najeriya ke bi.

Ya ce an ware wa zaben N2.3bn ne saboda yawan masu zabe a Jihar.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Farfesa ya ce APC ta lashe kujerun Shugabannin Kananan Hukumomi 44  da kansiloli 484 na Jihar.

Jigawa: Babu bayanin nawa aka kashe

A Jihar Jigawa kuma, Hukumar Zabenta, (JISIEC) ta gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar 29 ga Yuni, 2019, inda jam’iyyar APC mai mulki ta lashe daukacin kujerun shugaban karamar hukuma 27 da kansiloi 287.

Wakilanmu ba su samu Shugaban JISIEC, Alhaji Sani Ahmed Babandi a lokacin da suka ziyarcu ofishin hukumar ba, sannan bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da aka aika masa ba.

Daraktan Kudi da Gudanarwar na Hukumar, Muhammad T. Yunusa, ya ki bayar da bayanan kudaden da aka kashe wurin gudanar da zaben, bisa hujjjar cewa Shugaban Hukumar ne kadai zai iya bayanin.

“Zan dai tabbatar cewa an gudanar da zaben cikin nasara a ranar 29 ga Yuni, 2019. Muna kuma da wani da ke zuwa ranar 29 ga Yunin 2021 da yardar Allah. Iya abin da zai iya cewa ke nan,” inji shi.

Tun 2014 har yanzu ba ranar zabe a Katsina

Rabon da a yi zaben kananan hukumomi a Jihar Katsina tun shekarar 2014 zamanin Gwamna Ibrahim Shema na jami’iyyar PDP.

Da Gwamna Aminu Bello Masari ya hau mulki, sai ya sauke su ya nada kantomomi a kananan hukumomin.

Mun tuntubi Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Bako, amma ya ce ba a sa ranar zaben kananan hukumomi ba a jihar.

Ci-birbiri a zaben Kaduna

Rabon da a yi zaben kananan kumomi a Jihar Kaduna tun ranar 12 ga Mayu, 2018, inda jam’iyyar APC mai mulki ta lashe kananan hukumomi 15, babbar jam’iyyar adawa ta PDP kuma ta tsira da hudu.

Rashin tsaro ya hana gudanar da zaben a kananan hukumomin Jaba, Kaura da Kajuru; na Chikun kuma bai kammalu ba.

A Jaba, Kajuru da Kaura da ba a yi zabe ba an nada kantomomi.

Kasafin 2018 na Jihar Kaduna ya nuna an ware wa zaben N1.013b.

Legas sai nan gaba

Wakilinmu ya gano cewa a cikin wannan shekarar za a yi zaben kananan hukumomin Jihar Lega idan wa’adin shugabanni masu ci ya kare.

A zaben da ya gabata, jam’iyyar APC ma mulki ce ta lashe daukacin kujerun shugabannin kananan hukumomin.

Yadda abin yake a Ekiti

A ranar 7 ga Disamba, 2020 ne Jihar Ekiti ta yi zaben shugabannin kanana hukumomi da wa’adinsu zai kare a watan Disamban 2021.

A zaben, jam’iyyar APC mai mulki ce ta lashe duk kujeru 16 na ciyamomin kananan hukumomi da kansiloli 177.

Sai dai an kasa gano nawa aka kashe wurin gudanar da zaben shugabannin da wa’adinsu shekara daya ne rak.

Ondo da Filato ma haka abin yake

A Jihar Ondo ma inda Jam’iyyar APC ke mulki a yi zaben a ranar 22 ga Agusta, 2020 inda jamiyyar ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomin 18.

A bangaren kansiloli kuma ta lashe 194 daga kujeru 198 da ake da su a jihar.

Jam’iyya mai mulkin Jihar Filato ta APC ta cinye kujeru 12 daga cikin kananan hukumomi 13 da ak yi zaben, inda babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta tsira da 1.

Ragowar kananan hukumomi hudu kuma ba a gudanar da zabe ba; daga baya gwamnan jihar ya nada ’yan jam’iyyarsa a matsayin shugabannin riko.

Jihar dai ta kashe N1.040bn a kan zaben da aka gudanar a 2018.

Duk kanwar ja ce

Naira biliyan biyu ne zaben kanan hukumomin Jihar Ribas ya lakume, kamar yadda Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Paulinius Nsirim, ya shaida mana.

A Jihar Akwa Ibom kuma jam’iyyar PDP mai mulki ce ta cinye dukkannin shugabannin kananan hukumomi da kansilolin a zaben ranar 31 ga Oktoban 2020, wanda babbar jam’iyyar adawa ta APC ta kauracewa.

A watan gobe za a gudanar da zaben kananan hukumomin Jihar Edo, inda a lokacin da aka yi na baya, jam’iyyar APC mai mulki ce ta yi nasara da dukkannin kujerun da aka yi takara.

A halin yanzu dai ciyamomi biyu da wasu ’yan tsirarun kansiloli ne ba su sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP da Gwamna Godwin Obaseki ya koma ba a bara.

Masu sharhi na ganin babu abin da zai sauya a zaben kananan hukumomin da ke tafe.

Jihar Kuros Riba inda jam’iyyar PDP mai mulki ta lashe dukkannin kujeru a zaben kananan hukumominta 18 na watan Mayun 2020, babu bayani game nawa aka kashe wurin gudanar da shi.

Mun tuntubi Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Kwamared Asu Okang, amma ya ce , “Wata nawa da gudanar da zaben kananan hukumomin jihar, amma ba ku nemi wadannan bayanai ba sai yanzu?”

Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Borno ce ta lashe zaben na watan Nuwamban 2020, wanda Shugaban Hukumar Zaben Jihar (BOSIEC), Alhaji Abdu Usman, ya ce an kashe milyan N600 wurin gudanarwa.

Ana sa ran gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Fabrairu a Jihar Yobe amma babu bayani game kudaden da za a kashe.

A zabukan baya dai jam’iyyar APC mai mulki ce ta tashi da daukacin kujerun ba tare da jam’iyyun adawa sun samu ko daya ba.

A zaben Jihar Gombe na watan Disamban 2020 jam’iyyar APC mai mulki ta lashe duk kujen kananan hukumomi 11 da kansiloli 114 na jihar.

Kwamishinan Yada Labaran Hukumar Zaben Jihar Jihar (GOSIEC) Mista Bulus Kudi, da muka tambaya karin bayani game da kudaden da aka kashe, ya tura mu zuwa ga Shugaban Hukumar wanda shi kuma bai amsa kiran wayarmu ko rubutaccen sakon da muka tura masa ba.

Jam’iyyar PDP mai mulki ce ta cinye dukkanin kujerun shugabannin kananan hukumomi a zaben da aka yi a watan Fabrairun 2020 a Jihar Enugu.

Shugaban Hukumar Zaben Jihar (ENSIEC), Mike Ajogwu, ya ce zaben kamar wanda aka yi kafinsa, jam’yyar PDP mai mulki ce ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomin.

Sai dai ya kasa bayyana yawan kudaden da aka kashe wurin gudanar da zabubakan.

A Jihar Abiya jam’iyyar PDP mai mulki ta lashe daukacin kujeru 17 na shugabannin kananan hukumomi, jami’iyyar Labour Party kuma ta samu kujerun kansiloli 10 a Karamar Hukumar Ikwuano.

SIECs ba za su iya adalci ba —NILDS  

Tsohon Minista a Ma’aiaktar Tsare-tsaren Kasa kuma Darakta-Janar na Cibiyar Nazarin Ayyukan Majalisa (NILDS), Farfesa Abubakar Sulaiman, ya yi kira da a rusa SIECs domin inganta zaben kananan hukumomi.

Ya ce “Mun fi mayar da hankali a kan gwamantin kasa ba mu damuwa da abin da ke faruwa a kanan hukumomi, duk wata hukumar zabe ta jiha a soke ta.”

Ya ce tunda hukumomi daya-daya ne ke kula da kuma gudanar da tsari karatun jami’a, jarabawar kammala sakandare, da jarabawar shiga jami’a, to haka ya kamata INEC ta zama ita ce mai kula da zabuka a dukkannin matakai, amma babu wata hukumar zaben jihar da za ta iya zama ‘yar ba-ruwanmu.

Zaben kananan hukumomi ko zamba?

Darakatan Bunkasa Cigaban Dimokuradiyya (CDD), Idayat Hassan, ta ce tun da Najeriya ta koma tsarin mulkin dimokuradiyya a 1999, ake samun koma-baya a kanana hukumomi saboda rashawa, rashin sa ido da raunin shugabanci.

Ta ce gwamnoni na kin gudanar da zaben kananan hukumomi ta yadda suke nada yaransu ko manyan ‘yan jam’yyarsu a matsayin kantomomi.

“Gwamnoni ke nada shugabannin SIEC babu ruwansu da kwarewa ko abin da ake bukata. Abin takaici shi ne jam’iyyun adawa sun fara kaurace wa zabukan.

“Kafin kananan hukumomi su yi aiki yadda ya kamata sai an samo mafita game da zabukansu da wanda zai gudanar da su da kuma ‘yancinsu na gudanar da kudadensu,” inji ta.

Sai an gyara tsarin mulki —Lauyoyi

Lauyoyin da muka gana da su sun yi kira da a yi wa kundin tsarin mulki gyara domin kawo karshen matsalolin da ke hana kananan hukumomi ikon cin gashin kansu.

Solomon Umoh (SAN) ya ce batu ne da ya shafi dokar kasa, saboda haka sai an gyara kundin tsarin mulki kafin a samu mafita.

“Ba za mu ce ca ba za a yi zabe ba saboda dokar kasa ta wajabta yin zabe,” inji shi.

Shi kuma Abdulhamid Mohammed Esq ya yi kira da INEC ta rika gudanar da zaben kananan hukumomi domin tabbatar da gaskiya da adalci.