✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gwamnoni ke cinye kudaden kananan hukumomi

Daga an biya albashi, sai ya zuba abin da ya rage a aljihu, babu ruwansu da sauran ayyukan ci gaba

Shugaba Buhari ya nuna takaicinsa bisa yadda gwamnoni ke cinye kudaden kananan hukumomin jihohinsu da kuma koya musu satar dukiyar al’umma.

Buhari ya ce akwai daure kai yadda wasu gwamnoni da zarar an ba kananan hukumomin jihohinsu kasonsu na kudade daga Gwamnatin Tarayya sai su wawushe, su bar musu dan kadan, su kuma shugabannin kananan hukumomin su handame abin da ya rage.

“Wannan abin da na gani ne…. idan aka aiko wa jihar milyan N100 a misali, sai gwamna ya kwashe miliyan N50, ya aika wa shugaban karamar hukuma N50m da takarda da zai sa hannu cewa miliyan N100, ya karba.

“Idan shugaban karamar hukumar ya biya albashi, sai shi ma ya zuba abin da ya rage a aljihu, babu ruwansu da sauran ayyukan ci gaba.”

Ya bayyana hakan ne a jawabinsa a  Abuja ga manyan jami’an gwamnati da ke halartar kwas na 44 na Cibiyar Koya Dabarun Mulki (NIPPS) da ke Kuru, Jihar Filato.

Shugaban ya ce, wannan babban abin takaici ne, da ke nuna irin yadda cin hancin da rashawa suka yi nisa a Najeriya.

Ya yi tir da dabi’ar da ya ce gwamnonin suka rika, da yadda suka koya wa shugabannin kananan hukumomi satar dukiyar al’umma wanda kuma ke hana ci gaba daga tushe.

Don haka shugaban ya yi kira gare su da su ji tsoron Allah su daina haka.