✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Gwamnoni suka gurgunta dimokuradiyya a Najeriya — Ghali Na’Abba

Gwamnoni ne suka haddasa duk wata matsala da kasar ta tsinci kanta a ciki.

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Alhaji Ghali Umar Na’Abba, ya yi zargin cewa gwamnoni ne musabbabin matsalar da Najeriya take fuskanta ta yadda sun kassara dimokuradiyyar kasar.

Yayin zantawarsa da manema labarai na BBC Hausa a ranar Talata, ya ce gwamnoni ne suka haddasa duk wata matsala da kasar ta tsinci kanta a ciki.

A cewarsa, “duk da ana ganin dimokuradiyya a Najeriya wuyanta ya isa yanka, amma akwai sauran aiki idan aka yi la’akari da matsalolin da suka dabaibaye ta.

“Akwai rashin adalci a jam’iyyun siyasar kasar nan domin kuwa ana siyasar uban gida ta bangaranci, wanda hakan yana faruwa ne a jam’iyyar APC da ta PDP.

“Duk manyan jam’iyyu biyu na kasar na PDP da APC babu wacce take kwatanta adali da bin tsari na gaskiya.

“Ya kamata a koda wane lokaci ta bayar da damar mu’amala a tsakanin mutane sannan ta bude kofar da mutane za su zabi duk wanda suke ra’ayi, amma yanzu babu wannan tsari saboda gwamnoni sun kassara tsarin da dimokuradiyya ta kawo.

“Haka kuma, gwamnonin sun dakile duk wata kafa da za ta bai wa matasa damar damawa da su a fagen siyasa, wanda kuma hakan babbar barazana ce ga makomar kasar nan.”

Alhaji Na’Abba wanda ya shafe shekaru da dama a jam’iyyar PDP gabanin komawarsa APC, ya ce, “a yanzu bana tare da kowace jam’iyyar saboda ba dimokuradiyya ake yi ba kuma ba wani zabe da ake yi.

“A yanzu ko kadan ba a kwatanta gaskiya sannan babu wani adalci da ake yi a lokacin zabe,” inji shi.

Da yake bayyana ra’ayinsa dangane da gazawar wannan gwamnati, tsohon Kakakin Majalisar ya ce, “mun sha bayar da shawarwari amma ta yi domin kuwa bata jin kira.”