✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda hatsarin mota ya jefa Abuja cikin duhu

Tifa makare da duwatsu ta ruguza turken tura wutar lantarki mai karfin KV 132 a Abja

Hatsarin motar daukar duwatsu ya jefa wasu manyan unguwannin Abuja cikin duhu sakamakon karyewar wani babban turken wutar lantarki na Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN).

Hukumar TCN ta ce tifar da ke makare da duwatsu ta kwace wa direbanta ne sannan ta auka wa wani turken lantarki mai karfin KV 132, ta ruguza shi a ranar Talata.

“Sakamakon haka, an samu daukewar wuta a unguwannin Maitama, Wuse, Central Area, da wasu yankuna na Garki,” a cewar Janar-Manajan Hulda da Jama’a a TCN, Misis Ndidi Mbah.

Ta bayyana cewa turken tura wutar lantarkin da ya karye shi ne ke ba da wuta daga yankin Katampe zuwa Tashar Samar da Iskar Gas (GIS) da ke Kwaryar Birnin Abuja.

Amma dai jami’ar ta ba da tabbacin cewa TCN na aiki kai da fata don samar da wata hanya da za ta maye gurbin Tashar Katampe zuwa GIS domin ganin unguwannin sun samu wuta.

Ta ce, “Injiniyoyinmu na kokarin kawar da kayan wuta da suka fadi a sakamakon hatsarin daga kan hanya domin kawar da cunkoson ababen hawa.

“Hakazalika suna ci gaba da aikin tantance barnar da aka yi da kuma  aikin gyaran wucin gadi don samar da wuta a unguwannin, kafin a yi cikakken gyaran da za a mayar da komai yadda yake.”

Ta kara da cewa ba a samu asarar rai a hatsarin da ya haifar da matsalar ba, kuma TCN na sa rana nan ba da jimawa ba za a samar da wuta a unguwannin da abin ya shafa.