Daily Trust Aminiya - Yadda Hausawa ke sarrafa harshe (3)
Subscribe

Yadda Hausawa ke sarrafa harshe (3)

Wannan mako Aminiya ta kawo muku ci gaban nazarin da ta faru kan yadda Hausawa suke sarrafa Harshe, inda ta kalato makalolin masana adabi domin amfanin masu karatu da kuma daliban ilimi:

Gatse

Gatse, salon magana ne da ke cike da tarin fasaha wajen iya zance. Magana ce wacce duk abin da aka faɗa ba shi ake nufi ba. Wato salon magana ne da eh ke zuwa a matsayin a’a. Yi, ke zuwa a matsayin kada a yi. Wato duk abin da aka faɗa ba shi ake nufi ba, akasinsa ake nufi.

Babu wani takamaiman lokaci ko wuri ko wadansu mutane da suka keɓanta da yin gatse. Amma an fi yinsa ko dai a lokacin da mutum yake fushi ko yake kusa da yin fushin. Misali, idan aka ce da mutum ya aikata wani aiki mummuna, wanda shi kuma yana ganin kamarsa a ce ya aikata wannan aikin, ya wuce nan. To, idan aka ce wane kai ka aikata kaza? Sai shi kuma ya ce eh, ni ɗin ne. A wannan gaɓar za a gane cewa gatse yake yi idan aka lura da yanayin fuskarsa da kuma sigar da ya faɗi maganar. Saboda duk lokacin da za a yi gatse, da wahala a ga fuskar mai yin gatsen ba a ɗaure ba. Sannan sigar fitar maganar ita ma za a ga da alamar zafi a ciki.

Sannan a wasu lokutan da yara kan tambayi izinin aikata wani aikin da bai kamata ba, akan yi musu gatse. To ko a nan ɗin ma jin haushin tambayar ke saka a yi gatsen. Misali, kamar a ce an kawo wani abin amfani a gida da ya kamata a ce kowa a gidan ya samu wani adadi, to wani daga cikin yara bayan ya ɗauki nasa sai kuma ya ce na ƙara wani? Sai a ce da shi eh, ƙara mu gani.

Haka nan a wasu lokuta akan bibiyi gatse da ƙwafa, gyaɗa kai, cizon fatar baki, harara da sauransu. Duk waɗannan idan suka biyo bayan magana suna tabbatar da cewa wannan magana gatse ce.

Baƙar Magana

Baƙar Magana, magana ce wacce idan aka gaya wa mutum za ta harzuƙa shi ta ɓata masa rai. Zarruƙ, Kafin Hausa da Alhassan (1987), suka ce: “Baƙar magana ita ce duk wata magana da aka yi domin ta sosa zuciyar wani mutum.”

Sigogin Baƙar Magana

Akwai sigogi da dama da ake bi wajen yin baƙar magana, daga ciki akwai:

Baƙar Magana Kai-Tsaye: Ita ce duk wata magana da ake fitowa fili a gaya wa mutum domin ransa ya yi baci. Misali, na cinye idan an isa a ƙwata da ƙarfi. Wannan magana ce da ake gaya wa wanda ake ganin an fi ƙarfinsa. Dole wannan magana ta ɓata wa wanda aka gayawa rai, saboda yana kallo ga haƙƙinsa a hannun wani, amma kuma an ce idan ya isa ya ƙwata da ƙarfi idan kuma ba haka ba, to an ciye masa.

Baƙar Magana ta hanyar Gatse: Baƙar magana ce da ake yinta a fakaice. A irin salo na wannan baƙar magana akan yi amfani da gatse ne; wato halin da ake faɗin kishiyar abin da ake nufi. Misali, mutum ne ya je kasuwa zai sayi wani kaya, sai mai kaya ya tsuga wa kayan kuɗi, to a nan mai saye zai iya gaya wa mai sayarwa baƙar magana a fakaice. Kamar a ce ya kamata a sayar da kayan Naira dubu, sai shi mai kayan ya ce a saya Naira dubu uku, to a nan mai saye zai iya gaya wa mai sayar da kayan baƙar magana ta cikin gatse kamar ya ce, a’a, naira dubu goma.

Baƙar Magana cikin raha: Baƙar Magana ce da akan yi ta domin nishaɗi ba domin neman faɗa ba. Yawanci mahauta su suka fi yin wannan. Misali, idan aka samu mahauci yana gasa nama, ana iya tambayarsa a ce da shi, naman ya gasu kuwa? Shi kuma zai iya amsawa da cewa, yanzu nake fiɗa. Wato ke nan ba a gama feɗe dabbar ba ma tukuna bare a yi maganar gyara naman a saka shi jikin tsinke. Ko kuma ta wata hanyar mutum mai yawan shekaru ya rage shekarunsa, ana iya gaya masa magana ta cikin raha a ce da shi, a’a, gobe za a raɗa maka suna. Wato ke nan shi jariri ne.

Kirari

Kirari maganganu ne na kambawa da ake yi wa mutum ko kuma shi ya yi wa kansa. Kirari kan ƙara kwarzanta wanda aka yi wa. Ana amfani da ƙwarewar zance wajen yin kirari.

Akwai dangataka tsakanin kirari da take. Maroƙa su ke kiraranta mutum, su kwarzanta shi, su kambama shi, su zuga shi da sauransu, bayan makaɗa sun kaɗa masa takensa, wannan gaɓa ita ta ƙulla alaƙa tsakanin kirari da kuma take. Sannan bambancin da ke tsakaninsu kuma shi ne cewa shi kirari maganganu ne, take kuma kiɗa ne. Koda an ji maganganu a lokacin da ake kaɗa kirari, za a tarar cewa ana bayyana abin da kiɗa ko busa ke faɗa ne domin masu ƙaramin azanci su fahimta.

Akwai ƙwarewar magana da salo-salon sarrafa harshe a cikin kirari. Akan siffanta mutum da wani abu domin a fito da martabar wannan mutum. Dubi wurin da maroƙin Shata yake siffanta shi da mai maƙogwaron ɗanyen zinare, domin ya nuna tsananin kyawun muryar Shata wajen waƙa. Idan aka saurari wannan kirari, za a ji yadda wannan maroƙi yake ta zuga Shata, yake nuna masa shi wani na daban ne. Haka nan shi kansa Shatan akwai wurin da yake kuranta kansa a cikin Bakandamiyarsa inda yake cewa:

“Allah Ya yarda,

Har yau ni ke yi,

Ba ku samo canjina ba,

Balle in zauna,

Wai har in ce zan huta, in dai ɗan samu in sarara.

A’a, wane hutu Shata,

Ka riƙa dai.

Gwauron giwa mai ban tsoro na Habu Ɗan Ibrahim,

Kyarkeci mai wawar sura ɗan yaro,

Zaki mai zarin ƙarfi ɗan iro.”

Haka nan idan muka saurari waƙar Ɗan’anache ta Lawan, za mu ji wurin da yake cewa, “…To ya buge ukku, ya kashe ukku, ga wasu ukku sun gaza motsi…,” sannan kuma a cikin kirarin da yake yi wa wani ɗan dambe mai suna Duna yana cewa, “Duna bugunka ya ɗara bindiga zafi…,” da sauransu.

Babu wani takamaiman rukunin mutane da suka keɓanta da a yi musu kirari, ko suka keɓanta da yin sa. A kasar Hausa ba wai kawai mutane ake yi wa kirari ba, a’a, har ma da sauran halittu da abubuwa marasa rai.

Ana amfani da salon siffanta abin da ake yi wa kirari da irin kirarin da ake son yi masa. Misali, idan ana son fito da jarumtakar mutum ko wani abu, akan kwatanta shi da zaki, giwa, damisa, doki da sauransu, wannan kuma saboda ƙarfin da suke da shi. Idan kuma ana son bayyana irin yawan kyauta da mutum yake yi, sai a kwatanta shi da damina  da sauransu. Mai haƙuri kuma akan kwatanta shi da damo da sauransu. Haka-haka, abubuwan ke tafiya. Wato idan ana son siffanta mutum da wani abu sai a nemi wata dabbar ko wani abin da ya yi fice da wannan siffar a danganta shi da ita.

Cikin kirari akwai ƙwarewar magana, sarrafa harshe, taskace al’adu, nishaɗantarwa, ilimantarwa, har ma da gargaɗi da sauran ɗimbin darussa da za a iya koya.

Ba’a

Ba’a, na ɗaya daga cikin rassan Adabin Bakan Hausa wacce ke cikin rukunin azancin zance. Ba’a, salo ne na iya magana da Hausawa kan yi amfani da shi a wurare da dama don bayar da dariya. Tana ɗaya daga cikin salon da wadansu daga cikin makaɗan ban-dariya ke amfani da shi wajen bayar da dariya.

Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yar’aduwa (1987), sun ba ta ma’ana da cewa, “Magana ce wadda ake yi wa abokin zance ko taɗi da niyyar raha don a ji daɗin zance ko da niyyar shammata don a yi dariya. Wani lokaci ba’a kan ɓata ran wanda aka yi wa ita.”

Shi kuwa Farfesa Ɗangambo (1984), ya ba su aji ɗaya ne tare da baƙar magana, inda ya ce, “Ba’a da baƙar magana, maganganu ne da kan ɓata rai ga wanda aka yi wa.”

Ke nan bisa la’akari da waɗannan ma’anoni guda biyu, ba’a, tana ayyuka biyu; faranta rai ga mai sauraro da kuma ɓata rai ga wanda aka yi wa. Amma kuma a al’adance, aikin faranta ran ya fi yawa. Misali a yanayin da uba ya yi wa ɗansa ba’a, za a tarar cewa da uban da ɗan duk sun samu nishaɗi, haka ma tsakanin miji da mata, haka tsakanin saurayi da budurwa, haka nan ma tsakanin abokai da sauransu. Sai dai wani abin lura shi ne cewa salo da kuma irin launin ba’a shi ke maishe ta ta ɓata rai ko ta saka raha. Misali, faɗin mai gambara ‘Wuya siriri kamar damtsen tsohuwar da ta shekara ba lafiya’ wannan zai iya harzuƙa mutum.

Haka kuma bayan aikin raha da ɓata rai da ba’a ke yi, tana taimakawa wajen yi wa mutum nuni da barin aikata abin da bai kamata ba. Misali, idan ana cikin zance sai aka ji wani ya fiye magana da yawa, to na gaba da shi zai iya ce masa, ka fiye surutu kamar kabari. Jin wannan shi kuma za ta saka ya ɗan tsagaita.

Dukkan rukunan mutane, manya da yara, maza da mata sukan yi ba’a don a yi raha. Amma Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce mahauta (masu sana’ar fawa) sun fi iya ba’a. Har ma ya kawo wannan ɗan gajeren labarin don tabbatar da haka:

“Wata rana, wani mutum ya je wurin wani mahauci zai sayi tsire, ya dubi tsiren, ya ce, “Kai, malam, wannan naman ya gasu kuwa?” Sai mahaucin ya dube shi, ya ce, “A’a, ai yawo take yi.” Wato yana nufin dabbar ma ba a riga an yanka ta ba tukuna, ƙarewar ɗanye ke nan ko rashin gasuwa.

Ana yin ba’a ce a duk lokacin da ta kama, babu wani keɓantaccen wuri ko lokaci ko biki da ake yin ba’a. Makaɗan ban-dariya kan yi ba’a a lokacin da suke gudanar da sana’arsu ta kiɗa, haka ma mahauta sukan yi ba’a a lokuta da kuma wuraren da suke gudanar da sana’o’insu, mahaifi kan yi wa ’ya’yansa ba’a a duk lokacin da ta kama, miji kan yi wa matarsa ba’a, samari kan yi wa junansu ba’a a lokutan hira da sauransu.

Mun ciro wani sashi daga littafin Junaidu I. da ’Yar’aduwa T.M. (2003). Harshe da Adabin Hausa a Dunƙule. Gudunmawar Farfesa Dangambo kuma daga Rumbun Ilimi na shafin Intanet.

munkammala

More Stories