Daily Trust Aminiya - Yadda Hausawa ke sarrafa harshe
Subscribe

Wani zane daga cikin littafin Magana Jari Ce

Yadda Hausawa ke sarrafa harshe

A wannan mako Aminiya ta yi wani nazari ne kan yadda Hausawa suke sarrafa Harshe, inda ta kalato makalolin masana adabi daban-daban domin amfanin masu karatu da kuma daliban ilimi.

Sarrafa harshe ɗaya ne daga cikin rassan adabin baka. Masana Harshen Hausa sun bambanta wajen ambaton wannan reshe na Adabin Baka. Farfesa Ɗangambo (1984), ya ambace shi da Hikima da Sarrafa Harshe, wanda daga nan muka ciro wannan suna. Sai kuma Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (1992), suka kira shi da “Azancin Magana.” Zarruƙ, Kafin Hausa da Alhassan (1987), sun ambace shi da “Salon Magana.” Amma dukkansu sun yarda  da zamowar: Karin magana da Ƙarangiya da Kacici-kacici da Zaurance da Take da Habaici da Zambo da Gatse da Baƙar Magana da Kirari da kuma Ba’a a matsayin rassan sarrafa harshe.

Sarrafa harshe salo ne da Bahaushe yake amfani da shi wajen sarrafa magana ta sigogi mabambanta da ke ƙayatar da zance ko isar da wani babban saƙo ta cikin hikima kuma a wasu ’yan kalmomi dunƙulallu. Da su ake yi wa zance (na baka ko a rubuce) ado; adon harshe.

Karin Magana

Karin magana salo ne na yin magana taƙaitacciya kuma dunƙulalliya wacce ke ɗauke da ma’ana mai faɗi don isar da saƙo cikin hikima. Akan yi amfani da wannan salo wajen yin nuni, gargaɗi, yabo, ƙarfafa gwiwa, da sauransu duk a hikimance, ta yadda kusan in ba cikakken Bahaushe ba, fahimar wannan zance yana da wahala.

Ma’anar Karin Magana:

Masana Harshen Hausa sun fassara Karin Magana gwargwadon fahimtarsu. Daga ciki akwai:

Farfesa Ɗangambo (1984) da ya ce, “Karin Magana dabara ce ta dunƙule magana mai yawa a cikin zance ko ’yan kalmomi kaɗan, cikin hikima.”

Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yar’aduwa (1992), sun ce: “Karin Magana, tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaƙa tare da bayar da ma’ana gamsasshiya, mai faɗi, mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki.”

Ke nan idan aka lura sosai, za a ga cewa Karin Magana, magana ce dunƙulalliya wacce ba kowa ne zai iya gane ta ba tare da an yi masa cikakken bayani ba. Amma yau da gobe da yawan amfani da ita, musamman a zamunan da suka shuɗe da ake yawan tsarma su a cikin zance, sai ya zama Bahaushe yana iya gane abinsa. Misali, ana iya yi wa mutumin da ba ya da tattali nuni cikin ’yan kalmomi marasa yawa, kamar a ce da shi, wannan abin da kake yi zai hana ka farcen susa. Ko kuma idan ana son yin magana game da wani abu mai amfani da marar amfani. Kamar a ce idan an aikata abin, wani abu marar daɗi zai faru da wanda ya aikata, to ana iya yi masa nuni ta hanyar cewa da shi, wannan abin ba zai haifar maka da ɗa, mai ido ba; da sauransu.

Kowane ɗaya aka ɗauka daga cikin wannan Karin Magana guda biyu, za a tarar cewa maganganu ne dunƙulallu, waɗanda idan aka tashi farfasa su, za su ci wuri mai yawa. Amma idan aka faɗe su da baki ko aka rubuta su, za a ji su ko a gan su gajeru. Sannan shi wanda ake magana da shi zai iya fahimtar abin da ake nufi.

Amfanin Karin Magana

1. Taƙaita doguwar magana.

2. Nuni, gargaɗi da faɗakarwa cikin nishaɗi, sannan a taƙaice.

3. Bayyanar da ƙwarewa da fasahar Bahaushe wajen iya magana.

4. Adon harshe. Abin da ake nufi da adon harshe a nan, shi ne cewa karin magana yana ƙara wa zance kyau da kuma daɗi.

Karangiya

Ƙarangiya salon magana ce ta hikima wacce ake yi don nuna gwanintar harshe ko koyar da yara yadda za su iya magana. Akan kuma kira wannan salon magana da Kakkarya Harshe ko Gagara- Gwari.

Ma’anar Karangiya

Masana fannin Hausa sun ba ta fassara gwargwadon hali. Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce, “Hikima ce ta sarrafa harshe, domin koya wa yara iya magana.” Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yar’aduwa (1992), suka ce, “Salon sarrafa saututtuka ta cuɗanya muryoyin kalmomi su riƙa maimaita junansu cikin taƙidi don nuna gwaninta.”

Amfanin Ƙarangiya

Haƙiƙa akwai abubuwan amfani a cikin wannan salo na magana:

1. Tana karantar da yara ƙwarancewa wajen sarrafa harshe.

2. Tana ƙara wa yara kaifin tunani da natsuwa, saboda su kalmomin da ake furtawa suna da kamanceceniya, sannan da sauri da sauri ake son faɗinsu. Saboda haka idan ba a yi a hankali ba sai ya zama a wasu lokuta mutum ya tsinci kansa wajen furta kamlomin da ba su da ce ba.

3. Nishaɗantarwa, akan samu nishaɗi cikin ƙarangiya musamman idan aka samu wanda ya kasa faɗi sai sautin ya koma wani iri wanda wannan kan saka shi mai yin da masu sauroro su yi dariya.

Rabe-Raben Ƙarangiya

An rarraba su bisa la’akari da yadda ake yin su:

Gagara-Gwari: Shi ne matakin farko na salon maganar ƙarangiya wacce ake koya wa yara a makaranta. Saboda haka yara ma na iya yin wannan. Amma wani wanda ba Hausa ne harshensa ba, sannan ba a cikin Hausawa aka haife shi ba, to, faɗinsu daidai zai zama da kamar wuya, gurguwa da auren nesa. Misali:

Kai jan mutumin nan,

Ka ɗauki jar sandar can,

Ka kori jar akuyar can,

Mai cin jar dawar can,

Ta gaba da gonar Jatau.

Ingiza-bami: Salon magana ne da ka iya ingiza wanda ba ya da lura ya wayi gari yana faɗin maganar batsa ko ma zagi a wasu lokutan. Saboda haka samari da ’yan mata su suka fi amfani da irin waɗannan. Misali:

Na bugi bakin dokin baba da bayan hannu.

A nan da zarar kalmar dokin ta zame, sai a wayi gari ana faɗin “Na bugi bakin baba da bayan hannu”. Ke nan, an ingiza bami ya faɗi magana marar daɗi game da mahaifinsa.

Mai Nuna Gwaninta: Tirƙashi! Wani kaya sai amale. Shi wannan nau’in salon ƙaraginya sai gwanaye a Harshen Hausa suke iya yinsa. Mawaƙa su suka fi yin wannan don nuna gwanancewarsu a harshe.

Kacici-kacici

Shi kacici-kacici ana yinsa ne a lokaci ɗaya da tatsuniya wanda wadansu kan buɗe hirar da shi, sannan tatsuniyoyi su biyo baya, a wasu lokutan kuma yakan zo a ƙarshe, wanda idan aka ɗauki kacici-kacici mai kama da waƙa ne, ana zuwa ƙarshensa kowa sai ya watse.

Kacici-kacici a mahangar masana

Kacici-kacici, reshe ne na sarrafa harshe wanda yara kan yi ta hanyar tambaya da amsa. Amma Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yar’aduwa (1992), sun fassara shi a matsayin “Shiryayyun tambayoyi ne da kan zo a gajarce na hikima masu ɗaukar fasali ayyananne da ke buƙatar bayar da amsoshi”. Shi kuwa Farfesa Ɗangambo (1984), ya bayyana shi a matsayin nau’in tatsuniya mai tambaya da amsa.

Wannan nau’i na sarrafa harshe, yana da matuƙar muhimmaci ga yara. Saboda yana taimaka wa yara wajen kaifafa tunaninsu. Sannan yana koya wa yara iya magana ta fuskar bayar da amsar da ta dace ga kowace tambaya. Haka yana koya wa yara yin tunani kafin yanke hukunci, saboda a wasu lokutan sai an yi nazari kafin a iya bayar da amsar tambayar, inda kuma ba amsa sai a ce an ba da gari. Wato an sallama ba za a iya ba, a nan kuma sai shi mai tambayar ya faɗi amsa, wanda wannan yana koyar da yara sanin duk abin da ya gagari mutum, to za a iya samun mai yi.

Ana yin kacici-kacici ne ta hanyar tambaya da amsa. Mutane biyu, ko fiye da haka ne ke yinsa. Ɗaya na tambaya saura kuma suna amsawa. A duk lokacin da za yi kacici-kacici akan fara tambayar da cewa, Ƙulun ƙulu fito. Wannan kamar ita ce taken kacici-kacici, duk wanda ya ji wannan amo, sai ya nufi wurin, idan kuma ba mai sha’awar wannan wasa ba ne, sai ya kama gabansa.

Nau’o’in Kacici-Kacici

Kacici-kacici iri-iri ne, daga ciki akwai:

Nau’i na farko:

Tambaya: Ƙulun ƙulu fito.

Amsa:   Gauta

Tambaya:  Taƙanda ba ƙashi ba.

Amsa:  Kanwa.

Tambaya:  ’Yan matan gidanmu sun raba mana goro

Amsa:  Kashin awaki.

Tambaya:   Baba na ɗaka gemu na waje.

Amsa: Hayaƙi.

Tambaya: Daga nesa na jiyo muryar ƙawata.

Amsa:  Ganga

A wannan salo na kacici-kacici, yara sukan taru ne a wani waje, sai kuma a samu mai tambaya ya tsaya daga gefe guda, a bayan mai tambayar sai a samu wata bishiya ko wani abu a ce ita ce wurin sha; kamar tudun mun tsira kenan. To idan ana cikin wannan tambaya ana bayar da amsa, duk wanda ya faɗi wani abu wanda ba amsar tambayar ba ce, sai a rufe shi da duka shi kuma ya ruga da gudu har sai ya je ya taɓa wannan bishiya sannan a ƙyale shi. Wato ya sha ke nan.

Nau’i na biyu:

A wannan nau’in kuma za a riƙa ambato sunayen wasu abubuwa ne waɗanda suke da wata siffa, hali, ko ɗabi’a iri ɗaya, sai masu bada amsa sun sakankance sai a sako bare kuma a ciki. Duk sai a yi shiru, to wanda bai san dawar garin ba yana bayar da wannan amsa, sai a haushi da duka, har sai ya je ya sha tukuna. Misali:

Tambaya:  Bibita da jini

Amsa:  Tanjam

Tambaya:  Akuya da jini

Amsa:  Tanjama

Tambaya:  Jaki da jini

Amsa: Tanjama

Tambaya:   Mutum da jini

Amsa:  Tanjama

Tambaya:  Doki da jini

Amsa:  Tanjama

Tambaya:  Kaza da jini

Amsa:  Tanjama

Tambaya:  Bishiya da jini

Amsa:  Babu

To a wannan amsa ta ƙarshe duk wanda ya ce tanjam, ya kauce hanya sai duka.

Mun ciro wani sashi ne daga littafin Junaidu I. da ’Yar’aduwa T.M. (2003). mai suna Harshe da Adabin Hausa a Dunƙule. Gudunmawar Farfesa Dangambo kuma daga Rumbun Ilimi na shafin Intanet.

Za mu ci gaba a makon gobe

More Stories