✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda hukumomi ‘suka dirar wa Musulmai masu zanga-zanga’ a Indiya

An bayar da rahoton harbe Musulmi, ko kama su, ko rushe gidajensu

Wani bidiyo ya karade kafofin sadarwa na zamani ranar Lahadi wanda masu yada shi suka ce yana nuna yadda hukumomi suke rushe gidan wata baiwar Allah ne a Indiya.

Laifin mai fafutukar, Afreen Fatima, inji masu yada bidiyon, shi ne yin kira ga hukumomi su hukunta wasu manyan jami’an jam’iyyar BJP mai mulki.

“A yanzu haka ana rusa gidanta”, inji Sara Ather, daya daga cikin wadanda suka yi tsokaci a kan lamarin a Twitter.

“[Wannan shi ne] sakamakon fada wa hukumomi gaskiya; sakamakon kasancewa Musulma mai fitowa ta yi magana a Indiya”.

Hoton bidiyon dai ya nuna yadda wata katafila take zunkudar ginshikin da ke rike da kyauren harabar wani gida har ya fadi.

An dai bayar da rahoton rusa gidajen Musulmai a wasu sassa na kasar.

Zanga-zanga

Rahotanni sun kuma ce akalla mutum biyu, wadanda samari ne, aka kashe yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da ’yan sanda suka bude wuta a kan masu zanga-zangar a wasu sassan.

Wata kafar yada labarai mai suna Boom ta ruwaito cewa an kashe samarin ne ranar Juma’a a Ranchi, babban birnin Jihar Jharkhand da ke gabashin kasar.

“Ranar 10 ga watan Yuni wasu samari biyu – Mohammad Mudasir dan shekara 14 da Mohammad Sahil mai shekara 19 – suka mutu yayin da wasu mutane fiye da 20 suka jikkata sakamakon wutar da ake zargin ’yan sanda sun bude a kan masu zanga-zanga a Ranchi”, inji kafar.

Sai dai kuma kafar ta ambato babban jami’in ’yan sanda na garin, Anshuman Kumar, wanda ya tabbatar da mutuwar samarin, yana musanta hannun jami’ansa a lamarin.

Gidan talabijin na Aljazeera ya ruwaito cewa a Jihar Uttar Pradesh kuma ’yan sanda sun kama mutum akalla 230 da ake zargi da tayar da zaune tsaye bayan da hatsaniya ta wasu a garuruwan kasar bayan Sallar Juma’a.

Wasu daga cikin Musulmin kasar ta Indiya dai sun fita tituna a ’yan kwanakin da suka gabata suna zanga-zanga ne don nuna adawa da kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da ake zargin manyan jami’an BJP sun furta.

Tuni dai aka dakatar da mai magana da yawun BJP din, Nupur Sharma, sannan aka kori daya jami’in, Naveen Kumar Jindal, bayan da wasu kasashen Musulmi suka nuna rashin jin dadinsu game da sakin bakin da suka yi.

Hanyoyin diflomasiyya

Aljazeera ya ruwaito cewa kasashen Qatar da Saudi Arabia da Hadaddiyar Daular Larabawa da Oman da kuma Iran – wadanda muhimman abokan cinikayyar Indiya ne – su suka nuna rashin amincewarsu ta wasu hanyoyin diflomasiyya suka kuma yi amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen yin kira ga gwamnatin Indiya ta nemi afuwa.

Da dama daga cikin wadanda suka yi wallafe-wallafe a kafofin sadarwa na zamani sun koka da cewa wannan ci gaba ne na yadda hukumomi suke gallaza wa Musulmi a Indiya.

Daruruwan Muslmi ne dai suka yi zanga-zanga a jihohin kasar ta Indiya, ciki har da Uttar Pradesh da Bengal ta Yamma da Maharashtra da Jammu da Kashmir da kuma babban birnin kasar New Delhi.