✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda IPOB ta kone direban kamfanin Dangote a Imo

An harbe direban da yaran motarsa sannan aka cinna musu wuta.

Wasu tsageru da ake zargin ’yan a-waren Biyafara (IPOB) ne sun kashe wani direban kamfanin Dangote da yaransa biyu suka kona gawarsu a Karamar Hukumar Orsu ta Jihar Imo.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a lokacin da direban mai suna Saidu Alhassan, da yaran nasa, Halliru Mallam da Danjuma Isari, suke hanyarsu ta komawa Obajana a Jihar Kogi bayan dakon siminti da suka yi.

Wasu majiyoyi a jihar sun ce da farko bata-garin sun umarci direban da yaran motar su sauko daga motar, sannan suka harbe su suka kuma banka wa gawarwakin wuta.

Daga bisani ne aka tsinci gawarwakin a yashe a kusa da tirelar, inda aka dauke su zuwa Obajana.

Tun bayan da IPOB ta fara tilasta wa mutane zaman gida a yankin Kudu maso Gabas, jami’an tsaro, ’yan Arewa da sauran mutanen jihar ke fuskantar barazana daga ’yan a-waren na Biyafara.