✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda iyaye suka yi wa ’ya’yan cikinsu 48 fyade a shekara 2

Wasu daga cikin yaran sun rasu, wasu sun dauki juna biyu; wasu iyayen kuma sun lalata ’ya’yan cikinsu fiye da daya

A cikin shekaru biyun da suka gabata, sama da yara 48 ne iyayensu 34 suka yi wa fyade, kamar yadda alkaluman da Aminiya ta tattaro suna nuna a ranar Asabar.

Lamarin ya faru ne a jihohi 13, inda Legas ke kan gaba da yara 11 da iyayensu suka yi wa fyade, Ondo 5, Ekiti 4, Kwara 3, Ogun 3; sai mutum kowanne a jihohin Abia, Anambra, Kano, Delta, Osun, Edo, Kebbi da Kuros Riba.

Bisa kididdigar yaran da aka yi fyaden,  yaro daya ne namiji, wanda mahaifinsa ya lalata; akwai hudu manya, sauran kuma kananan yara ne, ciki har da yaro dan watanni 15.

Ta rasu bayan mahaifinta ya yi mata fyade

Na baya-bayan nan a ciki shi ne a watan Agustan 2022, inda wani mai gadi mai shekaru 55, Arowolo Ayodeji, ya furta cewa ya yi lalata da a ’yarsa mai shekara 19 sau biyu a Ipoti Ekiti, jihar Ekiti.

Magidancin ya ce abin da ya aika sharrin shaidan ne, yana mai cewa, “Ba da gangan na yi ba.”

Kakakin Hukumar Rsaron Farin Kaya ta Najeriya (NSCDC), Olasunkanmi Ayeni, ya bayyana cewa mutumin ya fara lalata da yarinyar ne tun tana shekara bakwai.

“Yana nufin cewa ya shafe laifin ya shafe shekaru biyu yana yin wannan aika-aikan,” in ji Mista Ayeni.

A ranar 19 ga Fabrairu, 2022, wani matashi mai shekara 28, Audu Dare, wanda ya yi wa ’yarsa mai shekara shida fyade, wanda ya yi sanadin mutuwarta, an tsare shi a gidan yari da ke Ado Ekiti.

Tsohuwar matar Dare ta rabu da shi, Eniola Aina, ta shaida wa ’yan sanda cewa ta yi aure da shi shekaru da suka wuce kuma sun haihu tare, amma ta bar gidansa shekaru hudu da suka wuce saboda halin rashin sanin ya kamatansa.

“Wata rana ya zo gidana da ke Ilawe Ekiti ya nemi fita da ’yata, ni kuma na amince, suka fita tare, daga baya ya dawo da ita misalin karfe 12 na dare ya yi tafiyarsa.

“Ba a jima ba, ta fara kukan ciwon kai da radadi a al’aurarta.

“An kai ta asibiti da ka kusa da mu, inda ta shaida min cewa, ‘Baba ne ya yi min fyade’, daga bisani ta rasu washegari.”

Ya yi wa ’ya’yan cikinsa hudu fyade

A wani labarin kuma, ’yan sandan sun kama wani uba mai ’ya’ya shida Sunday Julius kan lalata da ’ya’yansa mata hudu masu shekaru bakwai, 10, 11 da 15 a jihar Legas.

Rahotanni sun ce matar Julius, wanda ke zaune da iyalansa a wani daki da ke unguwar Alimosho a jihar, ​​ta sha kama shi da yaran.

“Mun yi aure a 2007 kuma mun haifi ’ya’ya shida tare, ’yarmu ta farko, wadda yanzu ta kai shekara 15, ta ba ni labari shekaru bakwai da suka wuce cewa a duk lokacin da muke barci da dare, yakan lallaba zuwa inda take kwana, ya kwanta da ita, ya rika shafa mata al’aura.

“Haka kuma, ’ya’yana na biyu da na uku da na hudu (dukkansu mata) su ma sun koka cewa mahaifinsu kan yi lalata da su idan na tafi yin talla.

“Yakan yi ne da tsakar dare bayan na yi barci mai nauyi. Sun ce yakan yi barazanar cutar da su idan sun tona asirin. Sai kwanan nan ni da kaina na kama shi da dare.

“Mu biyu muka kwanta a gado daya amma ya mike ya kashe fitila ya lallaba ya nufi inda ’yarmu mai shekara 10 take.

“Washegari, na gaya masa cewa na gan shi yana rungumar yarinyar, amma ya musanta hakan.

“Sai da na yi kwana hudu ba na ba shi abinci, daga nan sai ya fara duka na,” inji matar mai shekara 36, ​​wadda ke sayar da kayan lambu.

Yadda babana ya lalata ni bayan dawota daga Islamiyya

Babbar ’yar mutumin, mai shekara 15, wacce ke aji daya na babbar sakandare, ta bayyana cewa mahaifinta ya fara lalata da ita ne wata rana da yamma bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya.

Ta ce, “Zan cire kayana ne sai (daddy) ya shigo, ya sa na kwanta a kan gadon sannan ya yi lalata da ni.”

“Da goggona ta ta shigo, sai ya yi sauri ya sake ni; daga baya ta tambayi me ya faru, shi ne na bayyana mata cewa daddy ya dade yana lalata da ni.

“Shi ne ta fada ma mahaifiyata, ita kuma (mum) ta zarge ni da rashin sanar da ita a kan lokaci.

“Na ji tsoron gaya wa kowa saboda (daddy) ya yi barazanar kashe ni. Ban san cewa yana kwana da ’yan uwana ba.”

’Yan’uwanta biyu, masu shekaru bakwai da 11 sun ce mahaifinsu ya yi lalata da su sau biyu da dare kuma ya gargade su da kada su gaya wa kowa.

Mai shekaru 10 a cikinsu ta ce mahaifinta ya yi lalata da ita “sau da yawa a cikin dare.”

Da aka tambaye su dalilin da ya sa ba sa kururuwar neman agaji, sai suka ce yakan cew musu su yi shiru ko kuma ya rufe bakinsu.

Dan sanda ya dirka wa ’yar cikinsa ciki

A garin Ile-Oluji na Jihar Ondo kuma, an kama wani dan sanda, Sunday Udoh mai shekaru 38 yana kokarin tilasta wa ’yarsa zubar da cikin da ya yi mata.

Kakakin ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, ta ce sun kama shi ne a wata cibiyar lafiya da ke Ile-Oluji, inda ake zargin ya je ya zubar wa yarinyar ciki.

“A binciken da ake yi, an gano cewa wanda ake zargin yana yunkurin biya a zubar da cikin ’yarsa mai kimanin shekara 15, wacce yake kwana da ita.

“A halin yanzu ofishin kula da jinsi na sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Akure ne ke gudanar da shari’ar,” in ji shi.

Ya yi wa ’yarsa mai shekara 10 fyade

A makon jiya ne ’yan sanda suka cafke wani uba mai shekara 27, Adeniyi Adeleke, bisa zargin yi wa diyarsa ’yar shekara 10 fyade.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce bincike ya nuna Mista Adeleke ya aikata wannan aika-aika ne domin tsafi.

Haka kuma, an kama wani mutum mai shekaru 46 mai suna Jimoh Rafiu bisa zargin lalata da ’yarsa mai shekaru 6, bisa uzurin da matarsa ​​ta ki ta ba shi kanta.

Da take fallasa lamarin, karamar yarinyar ta sanar da kungiyar masu fafutukar kare hakkin yara da masu rauni cewa mahaifinta ya yi mata fyade akai-akai.

Mahaifiyarta ta ce a duk lokacin da ta dawo daga aiki, mijinta yakan cire kayan ’yarsa ne bisa hujjar cewa tana bukatar iska mai dadi.

Sai dai bayan yarinta ta ce tuna tana jin alamun radadi da mararta da tsakanin kafafunta a lokacin da take mata wanka, mahaifiyarta ta tambaye ta, sannan daga bisani ta tunkare shi bisa abin da ’yar ta shaida mata.

Mahaifin ya amsa aikata laifin kuma ya yi alkawarin dainawa.

Sai dai bayan kwanaki kadan yarinyar ta kasa jure radadin da ke addabar cikinta, lamarin da ya sanya mahaifiyar ta kai kara ofishin ’yan sanda na Idimu, lamarin da ya kai ga kama shi.

Jimoh ya amsa aikatawa amma ya dora laifin a kan matarsa da ke kin kwanciyar aure da shi, da kuma shaye-shaye.

Mutane da yawa da suka yi stokaci game da wadannan abubuwan sun yi mamakin dalilin da maza za su yi irin wannan munanan abu, wanda ya saba wa dokoki da al’adun kasar.

Sun yi kira ga jihohi da su kafa dokoki masu tsauri a kan wannan mummunan laifi, da suka hada da hada da daurin rai da rai, hukuncin kisa da kuma dandaka.

An yanke wa mai yi wa ’ya’yansa fyade daurin rai-da-rai

Da take yanke hukunci kan daya daga cikin shari’o’in a kwanan nan, kotun hukunta masu aikata laifuka a cikin gida da ke Ikeja a Jihar Legas, ta yanke wa Michake Ogbar hukuncin daurin rai-da-rai har sau uku, bisa laifin yi wa ’ya’yansa mata uku fyade, masu shekaru 10, 20 da 24 a jihar Legas.

Da yake karanta hukuncin, Mai Shari’a Abiola Soladoye ya ce, “Shaidun da ke gaban kotu sun nuna cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da fyade lifin fyaden da ake zargi a gaban kotun.

“Wanda ake tuhumar, wanda shi ne mahaifin ’yan matan su uku, an same shi da laifin da ake tuhumar sa, saboda haka an yi abin da ya kamata. Wannan lamari ne mai ban takaici, abin kunya ne ga iyaye.

“Wanda ake tuhumar ya lalata zuri’arsa ta hanyar lalata da ‘ya’yansa mata. Wannan abin kunya da me ya yi kama!

“An samu wanda ake tuhuma da laifi kuma an yanke masa hukuncin daurin rai da rai a kan laifi na daya.

“A kan shari’a na biyu, an yanke masa hukuncin daurin rai da rai, kuma a kan mutum uku kuma an yanke masa hukuncin daurin rai da rai.”

Miyagun kwayoyi, rashin aure da tsafi ne sababi —Masani

Wani kwararre a fannin ilimin halayyar dan Adam, Mahmuda Sarki ya ce abubuwan da suka shafi zamantakewa, muhalli, tunani da zamantakewar al’umma sune manyan abubuwan da ke haifar da irin wannan lamari.

“Abubuwa da yawa na iya haifar da hakan, amma rashin tarbiyyar iyayensu, shan muggan kwayoyi, tarbiyyar yara ga mara aure, suturar da ba ta dace ba, rashin kamun kai na iya jawo fyade cikin sauki.

“A mafi yawan lokuta, mazan masu shan miyagun kwayoyi suna aikata wannan abu, amma ba a cikin  hayyacinsu ba, musamman idan aka rabu da iyayen yaran.

“Wasu ubanni na yi wa ’ya’yansu fyade don yin tsafi, yayin da wasu kuma ke fama da tabin kwakwalwa. Wadannan kadan ne daga cikin dalilan,” inji shi.

Ina mafita?

Dangane da yadda za a magance matsalolin, ya ce ya kamata kungiyoyi masu zaman kansu su sa baki don ganin ana hukunta masu laifi.

Ya yi kira ga iyaye da su hana sanya tufafin da ke nuna tsiraici, su kuma wayar da kan ’ya’yansu yadda za su bijirewa masu fyade da kuma kai kara a kai.

Ya kuma shawarci malaman addinin Islama da na Kirista su rika yin wa’azin yaki da fyade, sannan masu ilimin halayyar dan Adam da su tashi tsaye wajen wayar da kan jama’a.

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Hamisu Kabir Matazu & Haruna Ibrahim