✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda jami’an tsaro suka ragargaji ’yan bindiga a hanyar Abuja-Kaduna

Jami'an tsaron sun hallaka dan bindiga sun kwace makamai bayan musayar wuta

’Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannun jami’an tsaro a kan Babbar Hanyar Kaduna zuwa Abuja, a lokacin da bata-garin suka yi yunkurin yin garkuwa da mutane.

Jami’an tsaron hadin gwiwar sun ragargaji ’yan bindigar tare da kashe daya daga cikinsu ne a musayar wuta da suka yi a lokacin da jami’an tsaron suka kai dauki bayan ’yan bindigar sun kai wani hari a ranar Lahadi.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya ce, “Jami’an tsaron sun yi nasarar kwato bindiga kirar AK47 da harsasai da kuma babur din ’yan bindigar.”

Ya ce ganin irin ragargazar da jami’an tsaron suka yi musu, sai ’yan bindigar suka ranta a na kare zuwa cikin daji.

“Sojoji da jami’an tsaron rundunar hadin gwiwar kuma na ci gaba kokarin tabbatar da kariya da aminci ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar,” in ji shi.

Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Yekini Ayoku, ya yaba wa jami’an tsaron bisa wannan namijin kokari, tare da ba su tabbacin cewa ba za a taba mantawa da abin da suka yi ba.