✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Jam’iyyar APC ta samu kanta a tsaka-mai-wuya a Adamawa

Allah ne kadai Mai ba da mulki kuma Shi Yake bai wa wadda Ya so.

Ga dukkan alamu wankin hula na neman Jam’iyyar APC ga dare a Jihar Adamawa inda take fuskantar gaza tsayawa takara a zaben Gwamnan Jihar, bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Yola ta haramta mata tsayawa takara a zaben na badi.

Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Malam Nuhu Ribadu ne ya shigar da kara a kotun a ranar 27 ga Mayu, 2022 inda ya zargi abokiyar takararsa, Sanata A’ishatu Binani da sayen kuri’u, kuma ya ce kuri’un da aka jefa sun fi adadin masu zaben ’yan takara na jam’iyyar.

Ya shigar da karar ce bayan bayyana Sanata A’ishatu Dahiru Binani a matsayin ’yar takarar jam’iyyar jim kadan da kammala zaben fid-da-gwani na jam’iyyar.

A zaben fid-da-gwanin A’ishatu Dahiru Binani ta samu kuri’a 430 sai Nuhu Ribadu ya zo na biyu da kuri’a 288.

Ganin haka ya sa ya shigar da karar inda ya yi zargin cewa abokiyar takararsa Binani ta sayi kuri’un wakilai, don haka ya bukaci kotun ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fid-da-gwanin da jam’iyyarsu ta gudanar a birnin Yola.

A karar Malam Nuhu Ribadu ya bukaci kotun ta dakatar da Binani daga bayyana kanta a matsayin ’yar takarar jam’iyyar sannan ta bayyana shi a matsayin wanda ya ci zaben fidda-gwanin sannan ta umarci jam’iyyarsu ta bayyana shi a matsayin dan takarar APC a zaben 2023.

Tsohon Shugaban Hukumar (EFCC) din ya kuma nemi kotun ta hana Jam’iyyar APC mika sunan A’ishatu Dahiru Binani ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), bisa dalilinsa na cewa ta bi haramtacciyar hanya ce domin cin zaben.

A martanin da ya mayar ga APC da Binani na rashin amincewar farko, lauyan Ribadu, Mathew Burka (SAN), ya bukaci kotun ta yi watsi da sanarwar farko ta jam’iyyar.

Ya kara da cewa an fara shigar da karar Mai lamba FHC/YL/ CS/12/2022 bisa ka’idojin kotu.

Amma a jawabansu dabandaban kan bukatar da Ribadu ya gabatar, APC da Binani ta hannun lauyoyinsu, Sule J. Abdul da Sam Ologunorisa sun kin amincewa da bukatun nasa.

Yayin da Jam’iyyar APC ke kalubalantar hurumin kotun, don bin kadin lamarin, Binani a cikin martaninta na farko ta ce ba a tsara karar Ribadu da kyau ba.

Ta bayyana karar a matsayin wadda ba ta dace ba, mai dauke da ringingimu da rashin gaskiya kuma take kunshe da zargezargen aikata zamba, laifi, kuma ba za a iya saurara ko tantance su, ta hanyar asalin sammacin ba.

A zama na farkon kotun ta dage zamanta zuwa 14 ga Oktoba, 2022.

Sai dai a wannan ranar ta 14 ga Oktoba, Babban Kotun Tarayyar ta yanke hukuncin rushe zaben fid-da-gwanin na Jam’iyyar APC da kuma hana jam’iyyar shiga zaben 2023.

A hukuncin kotun karkashin Mai shari’a Abdul’azeez M. Anka ta bukaci Binani ta daina bayyana kanta a matsayin ’yar takarar Gwamna ta Jam’iyyar APC.

Mai shari’ar ya ce ya yanke wannan hukunci ne bisa hujjar cewa zaben fid-da-gwanin bai halatta ba, saboda an kada kuri’a ba bisa ka’ida ba, sannan an hana wakilai daga Karamar Hukumar Lamorde, inda aka ce sam ba a ma gudanar da taron ba.

Zan daukaka kara kan hukuncin – Sanata Binani

Bayan yanke hukuncin da Babbar Kotun ta yi ne Sanata A’ishatu Dahiru Binani ta ce za ta daukaka kara kan soke nasararta da kuma hana Jam’iyyar APC shiga zabe a shekarar 2023.

A zantawar da ta yi da kafar labarai ta Muryar Arewa, a karon farko tun bayan, yanke hukuncin, ta ce Malam Nuhu Ribadu yana nan a matsayin babban wa gare ta kuma yana da damar shigar da kara a kotu. Ta ce ta dauki wannan shari’a a matsayin jarrabawa ce, ta kara da cewa Allah ne kadai Mai ba da mulki kuma Shi Yake bai wa wadda Ya so.

Ta ce “Hukuncin da aka yanke na soke zaben bai yi ba, kamata ya yi a ba jam’iyyar damar gudanar da sabon zaben fid-da-gwani.

“Don haka abin da zan yi shi ne in nemi hukuncin da zai tabbatar da tikitin takarar Gwamna a gaban Kotun Daukaka Kara.

“Na bukaci magoya bayana su kwantar da hankalinsu su jira sakamakon hukuncin Kotun Daukaka Kara. A matsayina na ko’odinetan yankin neman zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, burina shi ne in tabbatar da nasarar ’yan takarar APC a zaben 2023,” in ji ta.

“Dukkanmu ’ya’yan Jam’iyyar APC ne. Kasancewar Malam Nuhu Ribadu babban yayana ne kuma aminin dan takarar Shugaban Kasa ne babu abin da zai rage min kwarin gwiwa daga aikin da nake yi na tabbatar da nasarar Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa,” inji Binani.

Ba Binani ba zabe – Mata

Wannan hukuncin da kotun ta yanke ya sa Jam’iyyar APC ta fada cikin wani hali inda mata da dama suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka gudanar da zanga-zangar lumana dauke da hotuna suna cewa “Ba Binani, babu zabe.”

Da suke mayar da martani kan hukuncin kotun, wasu mata daga kananan hukumomin Jihar Adamawa 21 sun taru suka cika titunan suna cewa hukuncin makirci ne kawai ga mata ba wani abu ba.

Matan dauke da alluna sun rika rera taken “Babu Binani, babu zabe” da “Kulla makirci a kan mata ya yi yawa” da “Binani ce muke so.”

Shugabar matan da suka shirya zanga-zangar, Misis Comfort Ezra ta bukaci mata su tashi tsaye wajen ganin Binani ta yi nasara domin ita kadai ce mace mai fatar zama Gwamna a Najeriya baki daya.

“Muna kiran ku a yau da kakkausar murya kan yadda ake mayar da mata saniyar ware a fagen siyasa, musamman jam’iyyun siyasa da gangan suka sa tarnaki a kan yunkurin mata a lokacin zaben ’yan takararsu,” in ji ta.

Ta ce, “Hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na bayabayan nan, da ya ki amincewa da zaben ’yar takarar Gwamna mace daya tilo a Najeriya a zaben 2023, Sanata A’ishatu Dahiru Binani ta Jam’iyyar APC wata mugunta ce ga mata don dakile tagomashin da ’yar takarar ke da shi a tsakanin al’umma.”

Sai ta yi kira ga matan kasar nan su farka, kuma suna fadakar da dukkan matan Najeriya, ba wai iya na Jihar Adamawa kadai ba.

“Muna kira ga dukkan mata a fadin kasar nan su tabbatar ba a yi wa mata zagon-kasa ba ta hanyar danne musu hakkokinsu,” inji ta.

Misis Ezra ta ce A’isha Dahiru Binani ta samu kuri’a 430 inda ta doke ’yan takara 5 ta kuma samu tikitin Jam’iyyar APC, hakan ya girgiza jama’a a sauran wurare, ganin wannan babbar nasara da mata suka samu ne, ake ta yi mata bita-da-kulli don ganin an kassara wannan takarar ta mata gaba daya ba wai A’isha Binani kadai ba.

“Hanyoyin neman hana ta tikitin da kotu ta bi, wata hanya ce ta kokarin da maza ke yi wajen danne mata da cin zarafinsu.

“Sauran mata da kuma wasu ’ya’yan Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa sun bayyana wannan hukuncin da kotun ta yanke da cewa yin kafar ungulu ne ga ci gaban mata a tsarin dimokuradiyyar kasar nan, kuma kamata ya yi a sake zaben tunda an yi korafin cewa an gudanar da wasu abubuwa da ba su dace ba a wajen zaben fid-da-gwani, sai alkalin a ba jam’iyyar umarnin sake gudanar da sabon zabe.

“Amma dai tunda ’yar takararmu ta daukaka kara muna jiran hukuncin da kotun za ta yanke.

“Fatarmu dai a yi mana adalci mu mata, domin ya kasance mun kafa tarihi a tsarin dimokuradiyya na mun samar da mace Gwamna ta farko a tarihin kasar nan,” in ji ta.

Duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin Malam Nuhu Ribadu kan wannan hukunci ya ci tura, ganin cewa bai samu abin da ya nema na a tabbatar masa da takarar ba, maimakon haka ma an hana jam’iyyarsa tsayawa ne a takarar.