✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lissafin da ya sa Tinubu ya samu galaba a zeban dan takarar APC

Sa'a 71 da suka gabaci zaben fid-da gwamnin, sun kasance cike da shakku da rudani game da abin da ke iya faruwa a zaben.

Sa’o’i kadan kafin zaben fid-da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, cuku-cuku da kinibibin siyasa sun sauya akalar tafiyar zuwa goyon bayan tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a yunkurinsa na zama dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

Cikin kimanin sa’a 71 kafin zaben fid-da gwamnin, fagen siyasar Najeriya ya shiga cikin wani yanayi na shakku da rudani game da abin da ke iya faruwa a zaben.

Kusan ko’ina, daga kafafen yada labarai zuwa kafofin sadar da zumunta, labari da muhawarar da ke tashe shi ne taron jam’iyyar APC mai mulki.

Manyan masu fada-a-ji a jam’iyyar da masu rike da madafun iko a kasar sun yi ta kokarin ganin an rage yawan masu neman takarar da kuma samun goyon baya ga Tinubu, tsohon gwamnan Legas.

Janyewar da wadansu ’yan takara suka yi ya baiwa Tinubu fifiko a kan sauran ’yan takara da ke kafafa-da-kafada da shi, duk da cewa fafatawar ba ta kare ba har zuwa lokacin da muke hada wannan rahoton.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jam’iyyar su 22 ne ke kan gaba wajen cukumurdar da aka kwashe makonni ana yi.

A nashi bangaren, Buhari bai bayyana dan takarar da yake goyon baya ba, lamarin da ya sa kowane dan takara ke ganin zai kai bantensa, a yayin da suke neman goyon bayan Fadar Shugaban Kasa.

Ahmad Lawan a matsayin dan takarar APC

Bayan wasu tarurruka da suka yi a Fadar Shugaban Kasa da kuma Sakatariyar Jam’iyyar APC ta Kasa da sauran wurare, a ranar Litinin din da ta gabata ne shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya girgiza fagen siyasar Najeriya, inda ya bayyana Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar da jam’iyyar ta zaba.

Sai dai sanarwar da ya yi ta fuskanci tirjiya daga gwamnonin Arewa da suka dage a kan matsayarsu na farko cewa dole ne mulki ya koma yankin Kudancin kasar.

Ko da yake Shugaba Buhari ya nesanta kansa da sanarwar ta Abdullahi Adamu, majiyoyi sun ce wasu mukarraban shugaban kasar ne kanwa uwar gami a cikin wannan lamarin.

Kamar dai yadda aka yi zato, maganar zabar Ahmad Lawan a jam’iyyar bai je ko ‘ina ba ya ruguje.

Zabin gwamnoni

Gwamnonin sun kekashe kasa, suka kuma zage damtse don ganin an rage adadin masu neman tsayawa takara kamar yadda shugaba Buhari ya umarta.

Shugaban ya yi wata ganawa da Majalisar ba da Shawara ta Jasa ta Jam’iyyar APC, ciki har da wasu gwamnonin, inda ya bukaci a rage masu yawan neman tsayawa takara 23 gabanin babban taron jam’iyyar.

Bayan ganawar da dare da Kwamitin Ayyuka na Jam’iyyar, da zuwa wayewar garin Talata gwamnonin suka mika wa Fadar Shugaban Kasa sunayen mutum biyar.

Majiyoyinmu masu kwari sun tababtar mana cewa mutum biyar da aka mika sunayen nasu ga Shugaba Buhari duk ’yan kudanci ne, domin a tantance su a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Mutum biyar da aka gabatar wa Buhari sanayen nasu su ne Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da kuma Gwamna Dave Umahi  na Jihar Ebonyi.

Majiar ta gaya mana cewa, “Sun zabo daya daga Kudu maso Gabas daya daga Kudu maso Kudu da uku daga shiyyar Kudu-maso-Gabasa bisa matsayinsu na cewa mulki ya koma Kudu.”

Ba za ta sabu ba —Sauran ’yan takara

Nan take, ’yan takara biyar suka yi watsi da jerin sunayen da gwamnonin suka gabatar, suna masu cewa ba a tuntube su ba kafin gwamnonin su kai ga yanke shawara.

‘Yan takarar su ne Gwamnan Jihar Kuros Riba Ben Ayade; tsohon Minista a Ma’aikatar ilimi, Emeka Nwajiuba; tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu; tsohon Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha; da dan kasuwa Tein Jack-Rich.

Sun bayyana hakan ne a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar ranar Talata, inda suka nesanta kansu daga cikin jerin sunayen.

Ya kamata Buhari ya sa baki

Hakazalika, ’yan takara shida daga shiyyar Kudu maso Gabas sun rubuta wa shugaban kasa wasika, inda suka bukace shi da ya sa baki yayin taron don “jagorancin da ya dace”.

A nasa bangaren, Fasto Tunde Bakare ya yi watsi da jerin sunayen gwamnonin, yana mai cewa har yanzu yana cikin takara.

Bayan da hayaniyar da ta biyo bayan jerin sunayen da gwamnonin suka gabatar, Shugaba Buhari ya ki amincewa da shi.

Rashin nasarar matakai daban-daban, ciki har da na shugabannin yankin Kudu maso Yamma da dattawan Kudu maso Gabas da gwamnoni ne ya share fagen gudanar da zabe a tsakanin masu son tsayawa takara.