✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda jarumar Bollywood Kangana ta sa zare da ’yan sanda

’Yan sanda a brinin Mumbai na Indiya sun bai wa jarumar fina-finan Bollywood Kangana Ranaut shawara ta kaurace wa birnin. Hakan ya biyo bayan wani…

’Yan sanda a brinin Mumbai na Indiya sun bai wa jarumar fina-finan Bollywood Kangana Ranaut shawara ta kaurace wa birnin.

Hakan ya biyo bayan wani sako ne da Kangana ta wallafa ranar Litinin a shafinta na Twitter tana cewa ’yan sanda sun mamaye mata ofis.

“Sun kwace min ofis da karfin tsiya, suna auna komai, sannan suna musguna wa makwabtana.

“An ma fada min cewa gobe za su rushe min gini”, inji ta.

Ta kuma wallafa wani hoton bidiyo wanda ta ce na ’yan sandan ne yayin da suka mamaye ofishin nata.

– Asalin takaddamar –

Tun da farko dai Kangana ta yi godiya ga Ministan Harkokin Cikin Gida na Indiya, Amit Shah, saboda tsaron da ya sama mata bayan ta yi ikirarin cewa ana yi wa rayuwarta barazana bayan ta yi zargin ta’ammali da miyagun kwayoyi a Bollywood.

Tsaron da aka bai wa Kangana, mai lakabin Y+, shi ne samar da zaratan sojoji dauke da makamai don su yi gadin ta.

Takaddamar da ta barke tsakanin jarumar da ’yan sanda dai ta samo asali ne daga sukar da Kangana ta yi a kan binciken da jami’an ke yi game da mutuwar jarumi Sushant Singh Rajput.

Jarumar ta ce ne ta fi tsoron ’yan sanda a kan ’yan mafiyar Bollywood.

– Barazana – 

Kafofin yada labarai na Indiya sun ambato jarumar tana cewa jam’iyar ’yan kishin kasa ta Jihar Maharashtra, Shiv Sena, na yi mata barazana.

Da yake mayar da martini ga kalaman Kangana, dan Majalisar Wakilai na Indiya, Lok Sabha, Vinayak Raut, yana shawartar jarumar da kada ta je Mumbai.

“Muna rokon ta da kada ta zo Mumbai; wannan ba komai ba ne illa cin fuska ga ’yan sanda”, inji Raut, wanda shi ne jagoran Shiv Sena.

A wani sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Juma’a, Kangana ta ce, “Na ga mutane da dama suna yi min barazana kada na zo Mumbai, don haka yanzu na yanke shawarar zuwa a wannan makon ranar 9 ga watan Satumba, kuma zan bayyana lokacin idan na dira a filin jirgi”.